Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci

0
19

Akan so duk lokacin da mutum zai yi aure, mace ce ko namiji, ya dubi don me zai yi auren, shin kyawu ne? Kuɗi ne? Nasaba ce? Ko kuma addini ne?

Da yawa daga cikinmu mun fi damuwa da aure dan kyau, ko kuma na auri ɗiyar wane, ko kuma na yi auren jari, ko kuma na aure ta domin ina sha’awarta, shi yasa auren bai cika tasiri ba. Hakan yake a gurin matan, in namiji ya zo ba kya duba addininsa, sai dai zan huta in na aure shi? Ko kuma ɗan wane gida ne? Waye babansa?

Ko kuma yana cikin jerin abinda nake so, daga cikin irin mazan da iyaye mata suka fi so su auri ‘ya’yansu su ne kamar haka:

  1. Accounting
  2. Banker
  3. Chairman
  4. Director
  5. Engineer
  6. Finance minister ko kuma wani mai riƙe da muƙamin siyasa.

Idan ka zo cikin wannan lissafin ba mu damu da addininka ba bare amanarka, ko kuma ba mu damu mu yi bincike ba akan ka. Abinda za ku ji ana cewa kawai shi ne: “wance ta yi goshi ta yi sa’ar miji”. Don haka ƙoƙari za a yi a ɗaura auren ko ta halin ƙaƙa.

Shi yasa da kin zo sai ya ga kamar ya sayo ki ne, ba lallai ne ya ga darajarki ba ko kuma ta iyayenki, hasalima duk wani wanda ya shafeki ba lallai ne ya ga darajar shi ba. Sai ka ga nan da nan auren ya mutu, inda rabon an samu zuri’a, za su tashi ba su da uwa mace a gida.

Don haka ba lallai ne tarbiyyarsu ta yi kyau ba kamar na masu uwa a cikin gida, dan kuwa ba kowacce mace ce ke yin ƙoƙarin haɗa ‘ya’yan da ta haifa da wanda kishiya ta bar mata ta yi tarbiyyarsu tare ba. Ana samun masu wannan ƙoƙarin, amma ba su da yawa cikin mata.

Ba laifi ba ne in mun duba waɗannan abubuwan da na lissafa wajen neman aure. Kamar kyau, nasaba, kuɗi, amana, etc. Mafi dacewa shi ne mu kula da addini ya zama shi ne sahun gaba.

Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace da sahabbansa;

Na horeku da filawar kan juji, sahabai sukace; Ya rasulullah, mecece filawar kan juji? Annabi yace; kyakkyawar mace mara tarbiya, ba ƙaramin haɗari ba ce ga rayuwar al’umma haka ma namiji mara tarbiyya duk kuɗinsa da nasabarsa haɗari ne ga rayuwar al’umma.

Abubuwan da ka auri mace don shi ko kuma abubuwan da kika auri namiji don su, duk suna iya ƙarewa, misali kuɗi suna iya ƙarewa a kira  shi tsohon mai kuɗi, nasaba ma tana iya ƙarewa, haka mulki a kira mijinki tsohon chairman, ko kuma tsohon governor, haka kuma kyau ana tsufa sai ya tafi ko kuma da an yi hatsari an rasa wani sassa a jiki, shi kenan an nakasa. Amma addini in aka tsufa da shi ado yake ƙarawa mutum.

Sannan in kai aure domin addini, za ku ga kullum kuna ƙara son junanku. Da zarar tsofa ya kama ku zo kuna tausayin junanku, don haka aka fi so wajen aure mace ta duba mutum mai addini. Kamar yadda Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya faɗa; ana aure domin abubuwa huɗu:

  1. Kyau
  2. Nasaba
  3. Kuɗi
  4. Addini. Sai yace; “Na horeku da ku auri mai addini ta nan ne za ku more.

Randa aka yi sa’a kun kasance masu addini, ko ka yi aure da zarar ta zama matarka ya zama mijinki an kai ki ɗakinsa a matsayin matarsa, daren farko kamar yadda addinin musulunci ya koyar da mu (Muhammad Nasirideen Albani) ya koyar da mu a cikin littafinsa (Adabuzzubab) shafi na 96.

Ana so ango in zai shiga gida ‘yar tsaraba kaza ce ko nama ko dai wani abu na ci. Wannan sunna ce. Bayan an yi lashe-lashe za ku yi alwala za ki tsaya bayansa zai ja ki sallah raka’a biyu, bayan ya yi sallama zai karanta wannan addu’ar kamar haka:

“Allahumma barik li fi ahli, wa barik li ahli fi, allahummarzuqhum minni, warzuqni minhum, allahummajma’a bainana ma jama’tana fi khair, wa farriƙ bainana izha farraƙtu fi khair”.

Abinda ka faɗa; “Allah ka sanya albarka ga iyalina, Allah ka sanya ni mai albarka ga iyalina, Allah ka sanyata mai albarka a gareni, Allah ka azurta ta da ni, Allah ka azurtani da ita, Allah ka sanya haɗuwar mu ta  zama alkhari ni da ita, rabuwarmu in tazo Allah ka raba mu cikin alkhairi ni da ita”.

A lokacin da ka yi wannan addu’ar, Ubangiji zai ba ka kariya daga dukkan wani makirci ko tasiri da shaiɗan zai yi a cikin zaman aurenku. Miji zai yi kudibatul Haja, ko ya yi da larabci ko kuma da hausa idan bai iya larabci ba.

Daga nan sai ku tambaye junanku abubuwan da kuke so da wanda ba kwa so; inda za ka fara tambayarta kama daga abubuwan da tafi so na ci, na sha; da kuma irin suturar da ta fi sha’awar ta dinga gani a jikin mijinta. Kama daga abubuwan da ba ta so a yi mata, na tozarci wanda zai kawo ga ɓacin rai ko tashin hankali.

Bayan ta gama kai ma sai ka faɗa mata abubuwan da ba ka so domin ta sansu ta kuma kiyaye su; da kuma abubuwan da kake so su ma ta fahimce su; inda zai yi wu ka sanar da ita irin abincin da ka fi so, da kuma irin kayan da kafi sha’awa ka ga ta sa. Ba don kar na ari bakin mata ba, da sai nace akwai abubuwa guda uku wanda akasarin mata suka fi so a wajen mazajensu.

Idan mace ta rasa su, to duk abunda za ka ba ta ba zai burge ta ba, ko da kuwa kullum za ka yanka mata sa ta ci, to ba za ta ga muhimmancin shi ba. Ya kamata a cikin abubuwan da za ki faɗawa maigidan ya kasance akwai waɗannan ukun kamar haka;

1. Na farko shi ne kulawa

Ya baki lokacinsa. Dukkan mace ta kan so ta ga mijinta ya damu da ita, haka dukkan mace takan so ta ga ta isa da mijinta, wato baya ɓoye mata komai na rayuwarsa, kuma yana shawara da ita.

2. Na biyu shi ne tausayi

Mace takan so ta ga mijinta yana tausayinta a lokutan da take da lafiya da kuma lokutan da ba ta da lafiya, saboda ko shari’a ta nuna mana cewa mata masu rauni ne. Akwai lokutan da zai kasance ita za ta dunga jin haushinka, ko da kuwa kuna zaune lafiya.

Wannan shi ne lokacin da take da juna biyu, ba kai kaɗai ba, duk wani namiji za ta tsane shi a wannan lokacin, saboda haka ko da tana da mai aiki, ka dinga taimaka mata kana kuma lallaɓa ta har ma in da dama ka rinƙa jan ta da wasa don ka ɗebe mata kewa, ka mai da kanka yaro ka rinƙa tsokanarta, ka iya ƙulla zani a ciki kana cewa kai ma cikin ke da kai. Ko kuma ka kai kunnenka jikin cikin nata ka ce baby yace kaza za a yi.

3. Na uku shi ne ko wace mace tana so mijinta ya dinga yabon halittar ta

Ko da kuwa suran jikinta bai kai ƙololuwan da za a yaba ba. Idan ta yi kwalliya ka yaba ma kwalliyarta; haka idan ta yi girki ka yaba ma girkinta, haka kuma in kun yi mu’amalar kwanciya ka yaba mata.

Idan matarka baƙa ce ka zuga ta kace ai baƙaƙen mata sun fi kyau sun fi lafiya, farare yawan laulayi kullum kana asibiti haka in farace ka zuga ta kace farar mace albarkar mata, ku ake yayi kowa, tai fari ta wuce sa’a.

Haka duk irin halittarta ka yabeta. Idan doguwace ka zuga ta haka ma idan gajeruwace ka zugata.

 Kar ka sake ka yabi kyan wata a gaban ta, kar kuma kuna tafiya ka rinƙa kallon wasu matan kana nuna sun fi matarka duk abinda take da shi, ka yabi wannan abun duk muninsa tunda Allah ne ya bata ba ita ta ba wa kanta ba.

Mace tana son komai ta yi a yaba mata

In ta kawo labari kar a gwaleta, in ta yi kwalliya a yaba mata sosai ko da ta rasa abubuwa wanda zai gamsar da kai. Kar ka rinƙa tozarta ta kuma ka rinƙa gaya mata baƙaƙen maganganu.

Ire-iren waɗannan maganganun su ke sa mata su rinƙa fita hayyacinsu suna lalacewa suna ramewa duk irin daɗin da suke samu a gidan miji. Don haka, ya kamata mazaje su kula sosai.

Ina ga babu wasu abubuwan da mace take so irin waɗannan, domin kuwa idan ta same su a gidan aure kamar ta samu komai ne. Don haka ina baki shawara idan kika faɗawa mijinki waɗannan ki yi shiru da bakinki.

Da zan ari bakin ‘yan uwana maza, da zance; ka tambayi abubuwa guda uku; idan ta kiyaye su duk sauran nafila ne. Ta mutuntaka sannan ta mutunta duk wanda ya shafeka, ta kuma tsare sirrinka, sannan ta kiyaye bincika maka waya da bin diddigin wanda ka kira da kuma mai kiranka. Sannan ya kamata mace ta fahimci mijinta sosai fiye da komai.

Maza kala kala ne. Sun kasu kamar kala uku; akwai sarakan maza, akwai hanjin jimina akwai kuma limamai. Ya kamata ki tantance a wanne fage ne mijinki ya fita.

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceAbubuwan Da Ya Kamata Ka Sani Akan Android
Labarin na GabaTarihin Afirka Kashi Na Ɗaya