Hakkin Zaman Gidan Miji

0
28

Tabbatar mace cikin gidan mijinta doka ce tabbatacciya daga Allah Maɗaukaki, ga abin da Allah yace: “(ku mata) ku tabbata cikin gidajenku, kada ku bayyanar da adonku irin bayyanar da adon maguzancin farko”. 

Bisa dogaro da wannan ayar, haramun ne mace ta fita daga gidan mijinta ba tare da izininsa ba, ko da kuwa ta leƙa waje ne. 

Wannan yasa wani ɗan uwa ya gargaɗi mata da cewa: 

Sai ta ukunsu gadangama ke nan, 

Ba ta nufin gyara sai cuta. 

Bata nufin khairi ga mijinta, 

Baga kishiyoyi ba ga mafiotaba. 

Ba ta nufin gyara sai ɓarna, 

Sai duka safe ta cuci mijinta. 

Ya tafi ofis ko kuma kanti, 

Ba ta ƙara zama ɗakinta. 

In mai noma ne ko zage, 

Ka tafi gona zaure za ta. 

Ta na neman ta ga masu wucewa, 

Wai ita dai su ga kyan fuskarta. 

In ta ga sun ƙi shiga harkar ta, 

Sai ka ji ta ce za ta maƙobta.

AYYUKAN CIKIN GIDA 

Imamul Bukhari da Muslim sun rawaici hadisi da aka karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas, Allah ya yarda da su, daga Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: “Dukkanku makiyaya ne, kuma dukkanku ababan tambaya ne game da abubuwan kiwonku,…. Mace ma makiyayiya ce a kan gidan mijinta da ‘ya’yansa, kuma ita ma abar tambayace game da abubuwan kiwonta”. 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

Sannan an karɓo hadisi daga Asma’u ‘yar Abubakar Siddik, Allah ya yarda da su tace: “Na kasance ina yi yi wa zubairu (mijina) hidindimun gida baki ɗaya, kuma ya kasance yana da wani doki da nake wahala da shi, ina yi masa ciyawa kuma ina kula da shi”. Iman Ahmad ne ya rawaito shi. 

A wata ruwayar kuma (Asma’u) ta ƙara da cewa, tana ɗinke guga, da kwaɓa gari. Ahmad ne ya rawaito shi. 

Sannan kuma dai an karɓo hadisi daga Aliyu, Allah ya yarda da shi, yace, haƙiƙa matarsa Faɗima da ta sami labarin an kawowa Annabi (Tsira da amincin Allah ya su tabbata a gare shi) bayi, sai ta je gida domin ta kokawa Annabi (tsiri da amincin Allah su tabbata a gare shi) game da kantar da hannunnta yake yi a sakamakon amfani da dutsen niƙa (ko ya agaje ta da baiwa). 

Da ba ta sami Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) a gida ba, sai ta gayawa Aisha (R.A), da Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) ya dawo, sai Aisha ta faɗa masa saƙon Faɗima, sai Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya tafi gidan ‘yarsa Faɗima; ko da ya isa sai ya tarar da ita da mijinta Aliyu (R.A)

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

Sun riga sun kwanta bacci, da suka yunƙura za su ta shi domin taro shi, sai yace da su ku yi zamanku a inda kuke, sannan sai ya zauna kuma yace da su: “Ashe bana sanar daku abin da ya fi wanda kuka tambaya ba, idan za ku kwanta bacci ku yi tasbihi talatin da uku, hamdala talatin da uku, takbir kuma sau talatin da huɗu”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito. 

Duba da waɗannan dalilai da wasunsu ne wasu daga cikin malamai suka yanke hukuncin cewa: ɗaukar ɗawainiyar aikace-aikacen da suka shafi cikin gida nauyi ne da ya rataya a wuyan matar aure.

Ko da yake ba laifi ba ne a shari’ance ga wanda yake da iko ya samo wa matarsa ‘yar aiki, sai dai fa ba ita ba samun ladan da ake ba wa waɗanda suka tsayu da kansu domin aiwatar da waɗannan ayyuka na cikin gida yaku ‘yan uwa mata! ku sani fa ba ƙasƙanci ba ne ku tsayu da: 

⮚ Ba wa dabbobin miji abinci da kuma share garkensu. 

⮚ Wanke banɗaki. 

⮚ Sharar tsakar gida. 

⮚ Dafa abinci. 

⮚ Gyara shimfiɗa. 

Da sauran su. 

Waɗannan abubuwa dukkansu share fagen shiga Aljanna ne, shi yasa Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) da sahabbansa ba su goyi bayan ‘ya’yansu da matansu su yi watsi ko sakaci da su ba. Wannan ke nan. 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceHaɗarin Ƙuntatawa Iyali Wajen Ciyarwa
Labarin na GabaMenene Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali?