Ma’anar Aure

0
30

Aure wani haɗi ne da ake yinsa tsakanin namiji da matar data halatta da aure agare shi, bayan amincewarsu da juna, domin tabbatar da halaccin gudanar cuɗanya a tsakaninsu da kuma biya wa junansu buƙatar sha’awa ba tare da ansami wani zargi ba.
Abubuwan Da Saida Su Aure Yake Zama Karɓaɓɓe:

A musulunce aure na tabbata ne da tabbatar waɗannan abubuwa masu zuwa kamar haka:
1. Samuwar amincewar waɗanda za a ɗaurawa aure.
2. Waliyyin matar da za a aura.
3. Shidu.
4. Sadaki.
5. Siga. (wato maganganun da aure yake ɗauruwa da su), kamar mai neman yace da waliyyin mace: ‘Ina neman auren wance’. Sai shi kuma waliyyin yace: ‘Na aura maka ita.

Domin karanta cikakken bayanin abubuwan da sai da su aure yake zama karɓaɓɓe danna koren rubutun nan.

Wannan bayani an ciro ne da littafin Nagartacciyar Rayuwar Aure wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi. domin karanta cikakken littafin danna wannan koren rubutun.