Shin Ahlus sunna ne suka kashe Husaini (R.A) ko Mu’awiyya ne ko Yazidu ne? Amsar wannan tambayar ba ta buƙatar dogon bayani, saboda shi da kansa Husaini (R.A) ya bada amsar wannan tambaya, haka nan ma Aliyu ɗan Husaini (R.A)
Wato Zainul Abidina da Ummukulsum ƴar Sayyidina Aliyu (R.A) wato ƙanwar Husaini waɗanda a gabansu komai ya faru sannan kuma akwai waɗansu manyan malaman Shi’a cikinsu har da masu muƙaman ayoyi duk sun ba da amsar wannan tambaya.
Dukkansu bakinsu ya zo ɗaya a kan cewa ƴan Shi’a ne suka kashe Husaini! Ga maganganunsu daga amintattun littatafansu babu ƙari babu ragi.
1- MAGANAR HUSAINI (R.A)
Imam Husainii (R.A) ya tabbatar da cewa, waɗannan ƴan Shi’ar da suka gayyato shi, sun yaudare shi, sun warware mubaya’ar da suka yi masa, sun koma bayan rundunar da suka zo domin yaƙarsa sai ya ce:
“Idan kuma kun ƙi (mara baya, kun saɓa alƙawari, kun warware mubaya’a da kuka yi min, na rantse ba wannan ne farau ba a cikin mugwayen ayyukanku. Irin haka kuka yi wa babana da ɗan uwana, da ɗan Baffa na Muslim, haƙiƙa duk wanda ya yarda da ku ya yaudari kansa”
Kuma tun da farko shi da kansa ya ɗan yi tababa dangane yawan wasiƙun da suka aiko masa, ya sha jinin jikinsa inda ya ce: “Haƙiƙa waɗannan suna tsorata ni, ga kuma wasiƙun mutanen Kufa, kuma ma jin kashe ni za su yi”.
Domin karanta bayani akan Falalar Kuka Ranar Ashura Danna nan
Kuma ya yi addu’a ya ce:
“Ya Allah ka shiga tsakaninmu da mutanen da suka gayyato mu domin su taimake mu, amma suka zo suka kashe mu”.
A ƙarshe dai Imam Husaini (R.A) ya yi musu baki, ya yi musu baƙar addu’a inda ya ce: “Ya Allah in ka raya su ka rarraba kawunan su , ka tarwatsa su ƙungiya-ƙungiya, kada ka sa shugabanni su yarda da su har abada, saboda sun gayyato mu domin su taimake mu, amma kuma sai suka afka mana da kisa”. Waɗannan kaɗan ne daga iƙrari da Imam Husaini ya yi kan bayanin waɗanda suka kashe shi.
2- MAGANAR ZAINUL ABIDIN (R.A)
Shi Aliyu ɗan Husaini (R.A) ne, yana daga cikin waɗanda suka kuɓuta daga cikin iyalan Husaini (R.A) a Karbala saboda shi ganau ne ba jiyau ba, ga abin da ya faɗa:
“Ya ku mutane (mutanen Kufa) ina haɗa ku da Allah shin ba ku ne kuka rubuta wa mahaifina wasiƙu ba, amma kuka yaudare shi, kuka yi alƙawarin yi masa mubaya’a da biyayya amma kuka yaƙe shi, kuka tozarta shi, Allah wadaranku, tur da tunaninku, shin da wane ido za ku yi tozali da Ma’aikin Allah ranar lahira idan ya ce da ku shi ne kuka kashe iyalansa, kuka keta alfarma tasa?”
Sai mata suka barke da kuka, su kuwa mazajen suka rinƙa zagin junansu suke cewa: “Kun halaka ba ku sani ba”.
Shi kuma (Zainul Abidin) sai ya ce: “Allah ya yi rahama ga duk wanda zai karɓi nasihata, ya yi aiki da wasiyyata a kan Allah da Manzonsa da iyalansa saboda mu masu koyi ne da Manzon Allah.
Gaba ɗayansu sai suka ce:
“Mun yi alƙawari za mu bi duk umarnin da ka ba mu, za mu tsare ka, za mu bi duk umarnin daka ba mu, faɗa taka aiki namu.
Za mu yaƙi wanda ka yaƙa, mu yi shiri da wanda ka yi shiri da shi. Sai mun kamo Yazidu, mun yi bara’a da waɗanda suka zalunce ka, suka zalunce mu”. Sai ya ce da su:
“Haba mayaudara, makirai, ai wannan ihu ne bayan hari, son zuciyarku ba zai bar ku ku iya aikata hakan ba. Wato so kuke ku yi min irin yadda kuka yi wa babana? Wallahi ba za ta yiwu ba jiya-jiya kuka kashe mahaifina a cikin iyalansa, alhali zuciyata ba ta rabu da baƙin cikin rabuwa da shi ba, da rabuwa da Manzon Allah (S.A.W) da ƴan uwana ba.
Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan
A lokacin da Zainul Abidin (R.A) yake wucewa sai ya ga ƴan Shi’ar Kufa suna ta kururuwa da koke-koke sai ya dube su cikin murya rarrauna ya daka musu tsawa ya ce: “Kuna wani koke-koke wai saboda mu, to su wane ne suka kashe mu in ba ku ba?”
3- MAGANAR UMMU KULSUM ƳAR ALI (R.A)
Ƙanwa ce ga Husaini (R.A) ita ma ganau ce ba jiyau ba, ga huɗubar da ta yi ga ƴan Shi’ar Kufa:
“Bayan haka, ya ku mutanen Kufa, ya ku maha’inta mayaudara,makirai, kada Allah ya tsayar da hawayenku, kada Allah ya kawar da kukanku. Ku dai kun yi kama da mahaukaciyar nan da take yini tana saka, sai kuma ta zo ta tsittsinka abin da ta saka gutsun-gutsun. Kuma rantsuwa don kawai biyan buƙatunku.
Babu abin da kuka iya sai girman kai da jiji-da-kai da gaba, da mugunta da ƙarya, ga kwaɗayi irin na kuyangi, da tsanin riƙo da gaba, aikinku ya munana Allah ya yi fushi da ku, kuma za ku dawwama a cikin wuta.
Kuna wani kuka saboda an kashe ɗan uwa na? Za ku yi kuka mai yawa, za ku yi dariya kaɗan, kun yi abin faɗar da ba zai rabi da ku ba, ba kuma za ku ga sauƙinsa ba har a bada, shi ne kashe dan cikamakon annabawa, wanda ya fito daga tsantsan tushen manzanci, shugaban samarin aljanna, wanda kuke fakewa da shi in ana yaƙi, wanda shi ne gatanku, tir da aikinku, zunubin ku ya munana ranar ƙiyama, kun shiga uku kun lalace kun yi asara kun gamu da fushin Allah, za ku gamu da ƙaskanci da wulaƙanci.
Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu
Ko kun san yadda kuka ɓata wa Manzon Allah rai?
Ko kun san girman alƙawarin da kuka ƙarya?
Ko kun san matsayin alfamar da kuka keta?
Ko kun san darajar jinin da kuka zubar?
Haƙiƙa kun yi taɓargazar da ta kusa sanya sammai su kece, ƙasa ta tsage, duwatsu su rumurmushe”
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan
4- MAGANAR ZAINAB ƳAR ALI (R.A)
Ita ma ƴa ce ga sayyaydi Ali (R.A) kuma tana cikin ƴan kaɗan da suka tsira daga kisa ranar karbala. A lokacin da su ke wucewa a kan raƙuma sai taji mata suna ta karuruwa sai ta leƙo daga darbuka (rumfar da ake yi akan raƙumi) tayi tsaki tace:
“ku mutanen kufa, mazajenku suna kashe mu, matanku suna yi mana kuka, sai ranar sakamako Allah zai yi hukunci tsakanin mu da ku”
Ya ɗan uwa mai karatu, ka ji maganganun waɗanda abin ya faru akan su, yanzu kuma ga maganganun manya-manyan malaman shi’a da kuma sunayen litattafan da suka yi bayani karara cewa ƴan shi’a su ne suka kashe Husaini.
Wani abin lura sh ine waɗannan malamai ƴan zamani ne waɗansu suna nan da ransu, Wadhrisu kuma ba wani daɗe wa suka yi da mutuwa ba.
KAZIM AL-IHSA’I ANNAJFI
Ya ce: “waɗanda suka yaƙi Husaini su dubu ɗari uku ne, dukkaninsu ƴan kufa ne, babu mutumin sham a cikinsu, babu mutumin Hijaz, babu mutumin Indiya ko Fakistan ko Sudan ko Misra ko Afrika, ƙabilu ne daban daban daga Kufa”
AYATULLAHIL UZMA MUHSINUL AMIN
Ya ce: “Sai kuma mutane dubu ashirin daga Iraƙi suka yi wa Husaini (R.A) mubaya’a, amma suka yaudare shi suka kashe shi”
HUSAINI KARANI
Ya ce: “Su mutanen kufa, ba wai tarwatsewa kawai suka yi daga bayan Husaini ba, a’a saboda tsabar munafurcinsu sai suka rinƙa gaggawar zuwa karbala suna ba da sunayensu domin a sa a cikin sojoji masu yaƙar Husaini don kawai su farantawa shaiɗan rai.
Misali akwai wani mai suna Amr binul Hajjaj wanda ya rinƙa nuna goyon bayansa ga Husaini da kare alfarmar ahlulbaiti har ma ya haɗa runduna domin ya kare Hani ɗan Urwah, amma sai ga shi ya canja yana kiran Husaini da sunan dan tawaye yana ma cewa da jama’arsa:
“Ku yaƙi wanda ya fice daga addini ya rabu da jama’a”! wani misali na irin wannan munafurci shi ne Abdullahi Ibn Hauzah Attamimi wanda mutumin kufa ne, dan shi’a ne tun zamanin sayyidina Ali, ta yiwu ma yana daga cikin waɗanda suka rubutawa Husaini wasiƙar gayyata, amma sai ga shi ya tsaya a gaban rundunar Husaini (R.A) yana cewa: “ya Husaini ina yi maka bushara da wuta” subhanallah! Wa iyazubillah!
To ɗan uwa ka ji yadda gaskiyar magana ta ke, amma kuma daga baya su waɗannan mutane sai suka dawo suna koke-koke suna zage-zage da tsine-tsine suna jigan waɗanda ba su ji ba ba su gani ba da laifinsu.
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan