Gaskiyar Abin Da Ya Faru Na Shahadar Husaini [R.A]

0
24

A wannan gaɓa zan bayyana gaskiyar abin da ya faru a taƙaice dangane da shahadar Husaini [R.A] kamar yadda amintattun masana tarihi suka bayyana. 

Mutanen Iraƙi sun sami labarin cewa, Hussaini (R.A) bai yi wa Yazidu mubaya’a ba a shekara ta 60 daga Hijira, saboda haka suka yi ta aika manzanni da wasiƙu zuwa gare shi, suna gayyatar sa ya zo don su yi masa mubaya’a, saboda su ba sa bayan Yazidu, har ma da halifofin da suka gaɓa ce shi, su kawai Aliyu da jikokinsa suke buƙata, yawan waɗannan wasiƙu ya kai ɗari biyar. 

Da Husaini (R.A) ya ga haka, sai ya tura Muslim ɗan Aƙilu don ya binciki gaskiyar lamarin. Da farko da ya je, sai ya ga dubban mutane suna kan wannan ra’ai kuma da alama da gaske suke kuma gidan Hani ɗan Urwata shi ne ya zama cibiyar yin mubaya’a ga Husaini (R.A). 

Da Yazidu ya sami labari, sai ya tura gwamnansa na Basra Ubaidallahi ibn Ziyad Kufa, ya yi tawaye, amma bai ba shi umarnin ya kashe Husaini ba.

Domin karanta bayani akan Falalar Kuka Ranar Ashura Danna nan 

Da ya je Kufa, ya yi zurfin bincike, har ya gano cewa a gidan Hani ibn Urwa ake kitsa komai. 

Ubaidullah ibn Ziyadu ya yi fito-na-fito, ya yi jawabai ga waɗannan da ƙaru yana razana su da ƙarfin rundunar Sham, yana kuma lasa masu zuma da yi musu alƙawarirrika na kuɗi da muƙami indai dakaru suka rinƙa zare jiki suna komawa cikin rundunar Ziyadu. 

Kafin ƙanƙanin lokaci cikin mutum dubu huɗu sai mutum talatin kacal ne suka ragu a bayan Muslim, su ma kafin faɗuwar rana sun canza sheƙa. Shi ne ya sa aka kama Muslim, Ibaidullah ya ba da umarni a kashe shi, sai ya nemi a ba shi izini ya rubuta wasiƙa zuwa Husaini (R.A), sai aka ba shi izini ya rubuta wa Husaini cewa: “Ka koma gida da iyalanka, kada ka ruɗu da ƙarairayin mutanen Kufa, maƙaryata ne” . 

Bayan kuwa a da ya rubuta masa cewa ya yi sauri ya taho Kufa, saboda komai ya yi daidai. Ubaidullah ya sa aka kashe Muslim ibn Akli. 

Shi kuwa Husaini (R.A) tuni ya fito, duk da yunƙurin da manyan sahabbai suka yi domin su hana shi tafiya Kufa, sun yi masa iya nasiha, amma ƙaddara ta riga fata. 

Ibn Umar. (R.A) ya ce da shi “ban iya gaya maka wani hadisi, Jibrilu ya zo wurin Manzon allah (S.A.W) ya sa shi ya zaɓi tsakanin duniya da lahira, sai ya zaɓi lahira, kai kuwa tsoka ce daga gare shi, saboda haka, wallahi babu wani a cikinku, da zai sami mulki har abada, kuma Allah ya yi muku haka ne, saboda ya tanadar muku abin da ya fi alheri a gurinku. 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

Amma Husaini bai gamsu da wannan ba, ya yi gaba, sai Ibn Umar ya rungume shi, ya fashe da kuka, ya ce, “Ina bankwana da wanda za a kashe”. 

Ibn Abbas (R.A) ya ce da shi: “Ba don kar mu yi abin faɗa ba, da sai na hana ka tafiya, ko da kuwa za mu yi koda kuwa za mu yi kokawa”. 

Abdullahi Ibn Zubair ya ce: “Me za ka yi a wurin waɗanda suka kashe mahaifinka, su soki yayanka da wuƙa a cinya?” 

Abdullahi dan Amar ɗan As (R.A) ya ce: “Husaini ya yi gaggawa zuwa ƙaddararsa, wallahi da na tarar da shi da na hana shi tafiya, sai dai in ya fi ƙarfina”.

Tun a kan hanya Husaini (R.A) ya sami labarin an kashe Muslim Ibn Akil da kuma yadda mutanen Kufa suka ba da shi, sai ya juya akalar tafiyarsa zuwa Sham wurin Yazid, amma sai ya yi kicibus da rundunar Ɗan Ziyadu a ƙarƙashin jagorancin Umar Ibn Sa’ad da Shimmar ibn Zil Jaushan da Husaini Ibn Tamim. 

Sai Husaini ya sauka daga dokinsa yana yi musu magiya su dubi girman Allah da ya kai kansa wurin Yazidu ya yi masa mubaya’a, saboda ya san ba zai so a kashe shi ba, ko ya koma Madina ko ya tafi jihadi har ƙarshen rayuwarsa. 

Amma suka ƙi ba shi ɗaya daga waɗannan abubuwan guda uku, suka ce sai dai abin da ya ga dama ya yi da shi. Har sai da wani daga cikin kwamandojin ɗan Ziyadu mai suna Al-Huff Ibn Yazid ya ce: “Don me za ku ƙi yarda da wannan tayi da suka yi muku?” Ai ko Turkawan Lailamawa suka nemi ɗayan waɗannan abubuwa kwa yi musu? 

Amma a banza ba su saurare shi. Da ya ga haka, sai ya miƙa wuya ga rundunar Husaini (R.A) har ya kashe mutum biyu daga cikin rundunar ɗan Ziyad, sannan suka kashe shi. Ya Allah ka yi masa rahama. 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

In ana maganar yawa ne, ba za a iya kwatanta yawan rundunar dan Ziyad da dakarun Husaini (R.A) ba, amma fa duk in da jarumai suka kai sun wuce nan, sun yi bajinta sai da suka ƙare gaba ɗayansu a kan bada kariya ga Husaini (R.A), ƙarshe ya rage sai shi kaɗai kamar zaki a cikin dubban mayaƙa, ya yi kansu amma sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi. 

Duk da haka kowane ɗaya daga wannan runduna yana shayin afkawa Husaini (R.A) har sai da wani tsagera mai suna Shimmar Ibn Zil Jaushan ya yi tsaurin ido ya cakawa Husaini mashi, ya faɗo ƙasa daga kan dokinsa, daga nan suka rufar masa da sara da suka har suka kashe shi. An ce shi Shimmar ɗin nan, shi ne ya ciro kan Husaini, waɗansu kuwa sun ce, Sinan Ibn Anas Annakh’i ne. 

Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!! Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”. 

Haƙiƙa Husaini (R.A) da waɗanda suke tare da shi sun rubauta, sun kasa, sun sayar, sun ci riba. Su kuwa waɗannan ƴan ta’adda sun yi hasara. Ya Allah ka jaddada rahama ga Husaini (R.A) da waɗanda suka yi shahada tare da shi.

SAURAN WAƊANDA SUKA YI SHAHADA TARE DA HUSAINI (R.A) 

Wani abin jan hankali shi ne, sunayen waɗansu daga cikin ƴaƴan Husaini da ƙannansa waɗanda suka gamu da ajalinsu a wannan lokaci a Karbala. 

Waɗannan sunaye su ne: 

1- Abubakar ɗan Aliyu Abi Talib (R.A) 

2- Umar ɗan Aliyu ɗan Abi Talib (R.A) 

3- Usman ɗan Aliyu ɗan Abi Talib (R.A) 

4- Abubakar dan Husaini ɗan Aliyu (R.A) 

5- Umar ɗan husaini ɗan Aliyu (R.A). 

Wannan yana nuna yadda Ahlul Baiti (R.A) suke matuƙar ƙaunar waɗannan sahabbai har suke sanya wa ƴaƴansu sunayensu, wannan bai tsaya kan Sayyidina Aliyu da Husaini ba, a’a kusan dukkan imamai sha ɗaya sun bi sahu. Dan uwa karanta waɗannan sunaye: 

1- Umar ɗan Aliyu ɗan Abu Ɗalib (Al-atraf)(R.A) 

2- Umar ɗan Muhammad ɗan Umar dan Aliyu(R.A) 

3- Umar ɗan Husaini ɗan Au (R.A) 

4- Umar ɗan Ali ɗan Husaini ɗan Ali (AlAshraf)(R.A) 

5- Umar ɗan Aliyu (Al-asgar) ɗan Umar (Alashraf) ɗan Aliyu zainul Abidina ɗan Husaini (R.A) 

6- Umar ɗan Hasul Aftus ɗan Aliyul Asgar ɗan Aliyu Zainul Abidin ɗan Husaini (R.A) 

7- Umar ɗan Husaini ɗan Zaidu ɗan Aliyu dan Husaini dan Aliyu (R.A) 8- Umar ɗan Msal Kasim ɗan ja’afarus Sadik (R.A) 

9- Umar ɗan Husaini Sibti ɗan Aliyu ɗan Abu Talib (R.A) 

10- Umar ɗan Ja’afar ɗan Muhammad ɗan Umar Al-traf ɗan Aliyu (R.A) 11- Umar ɗan Muhammad ɗan Umar ɗan Aliyu ɗan Husaini Asshadi (R.A) 12- Umar ɗan Yahaya ɗan Husaini ɗan Zaid (R.A) 

13- Umar ɗan Hasan ɗan Aliyu ɗan Husaini ɗan Aliyu thin Abi Talib. 14- Abubakar ɗan Aliyu ɗan Abu Talib (R.A) 

15- Abubakar ɗan Husaini ɗan Aliyu (R.A) 

16- Abubakar ɗan Hasan ɗan Aliyu (R.A) 

17- Abubakar ɗan Abdullahi ɗan Ja’afar ɗan Abu Talib (R.A) 

18- Usman ɗan Aliyu ɗan Abu Talib (R.A)

19- Usman ɗan Akilu ɗan Abi Talib (R.A) 

20- Usman ɗan Akilu ɗan Abi Talib (R.A) 

21- Aisha ƴar Musal Kazim ɗan Ja’afarus Sadik (R.A) 

22- Aisha ƴar Aliyu Rida ɗan Musal Kazim (R.A) 

23- Aisha ƴar Aliyu Abul Hasan ɗan Muhammad Jawad ɗan Aliyu Rida(R.A) 24- Mu’awiya ɗan Aliyu ɗan Ja’afar ɗan Abu Talib (R.A) 

25- Dalha ɗan Hasan ɗan Aliyu ɗan Abu Talib (R.A) 

Ya ɗan uwa mai karatu ka dubi yadda waɗannan bayin Allah suka sanya wa ƴaƴansu sunayen waɗannan manyan sahabbai musamman Umar domin su nuna wa kowa cewa, su fa ba sa gaba da su ko a kusa ko a nesa, saboda ai babu yadda za a yi mutum ya yi ta sanya wa ƴaƴansa sunayen waɗanda yake ganin su a matsayin maƙiya, koma munafikai ko kafirai. 

A nan na ƙara kira ga ƴan uwa masu da’awar son da bin Ahlul baiti da su yi koyi da su, su daina ƙin sahabbai, musamman Abubakar, Umar, Usman, Aisha, Ɗalha da Mu’awiya, su daina zagin su da tsine musu, su daina yi musu ƙage, saboda su Ahlul baitin (R.A) ba su yi haka ba. Ya Allah ka ganar da mu, ka ba mu ikon bin gaskiya. Amin. 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceWasiyyar Imamu Husaini (R.A)
Labarin na GabaWa Ya Kashe Husaini (R.A)