An karɓo daga Imani Husaini (R.A) ya ce da ƴar uwarsa Zainab lokacin da ya ga tana marin kumatunta, za ta yaga tufafinta, ta faɗi za ta suma, sai ya ce:
“Ya ke ƴar uwata, ki ji tsoron Allah, ki yi haƙuri, ki sani halittun ƙasa za su mutu, na sama ba za su wanzu ba, babu abin da zai saura sai Allah, wanda shi ne ya halicci halittu da Ikonsa, shi ne makaɗaici sanin mahaifi yana da daraja, haka Kuma mahaifiyata, haka ɗan uwana (Hassan) kuma ni da duk wani musulmi. Manzon Allah (S.A.W) ne abin koyin mu”. Sannan ya ci gaba da cewa:
“Ya ke ‘yar uwata na yi rantsuwa ka da ki karya min rantsuwata, idan na mutu KAR KI YAGA TUFAFINKI, KA DA KI YAKUSHE FUSKARKI. KA DA KI MIN KURURUWA!”.
To ɗan uwa ka ji da kansa abin da ya yi umarni, kuma har da rantsuwa kamar ya san a rina… to don Allah waɗannan koke-koke da dukan jiki, har ma da kisan kai, wasu lokuta daga ina aka samo su?
Domin karanta bayani akan Falalar Kuka Ranar Ashura Danna nan
MATSAYIN KOKE-KOKE DA KURURUWA
Manzon Allah (S.A.W) da Imaman Ahlul baiti sun yi hani ƙaƙƙarfa a kan yin koke-koke da kururuwa saboda wata mutuwa ko wata musiba. Ga kaɗan daga cikin ruwayoyin ingantattu kan haka daga littatafan Shi’a:
1-Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Kururuwa ya yin mutuwa aiki ne na jahiliyya”. 2- Imamus Sadik (A.S) ya ce: “Bai kamata a yi kururuwa ba ga wani mamaci, bai halatta ba, amma mutane, ba sa sani”.
Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Sautuka biyu tsinannu ne, Allah yana ƙin su, su ne kururuwa lokacin musiba, da waƙa lokacin samun ni’ima”.
Ruwayoyi masu ɗauke da irin wannan saƙo da hana kira kowane lokaci da kururuwa da kukan mutuwa ko musiba daga Annabi (S.A.W). Ahul baiti suna da yawa za ka iya samun su a waɗannan littatafan:
– Wasa’ilus Shi’ana Hurrul Amilij.2 sh. 915.
– Jami’u Ahadisu Shi’a-na Husaini Burujardi j. 3sh. 3sh. 488
– Biharul Anwar na Majlisi-j. 82 sh. 103.
– Mustadrakul Wasa’il na Nuri Attabrasi J. 1 sh.144.
– Alkafi na Kulaini j.3 sh. 325 da sauran su.
Waɗansu su ma daga cikin malaman nasu sun ce, akwai wani saɓani a kan haramcin yin hakan kamar su:
Muhammad bin Makki Al-amill, da Muhammadul Husaini Al-shirazi da sauran su.
Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan
HARAMCIN MARIN FUSKA DA DUKAN ƘIRJI DA ZUBAR DA JINI
Imam Ja’afarus Sadik (R.A) ya ce: Manzon Allah (SA.W) ya ce: “Idan musulmi ya bugi cinyarsa da hannunsa saboda wata musiba ladansa ya zube”. Kuma ya ce: “Baya daga cikinmu, wanda ya mari kumatunsa, ya yaga rigarsa (saboda wata masiba). Waɗannan hadisai da makamantansu da yawa a fili suna nuna haramcin abubuwan na rashin kan gado da masu da’awar son Ahlul Baiti suke yi a ranar Ashura da sauran su.
Kuma malamansu sun tabbatar da ingancin hadisan kamar yadda Muhammad Tijjani Samawi ya ce, ya tambayi Muhammad Bakir Sadr a kan wannan hadisin, sai ya ce “Babu shakka sahihin hadisi ne”. Wannan ya sa shi da kansa samawin ya ce:
“Gaskiyar magana, irin waɗannan abubuwa da waɗansu ‘yan Shi’a suke yi (ranar Ashura) samsam ba addini ba ne, duk ta hanyar sanyawa ayyukan lada mai girma, kawai al’adu ne da aka gada iyaye da kakanni a bisa tsantsar jahilci, har ma jahilai suna ganin wai mutum ya zubar da jininsa wata ibada ce kuma wanda ba ya yin hakan, wai ya zama maƙiyin Husaini”.
Kuma ya ci gaba da cewa: “Tsikar jikina tana tashi, kuma duk mai hankali zai ƙyamaci ya ga mutum ya cire kayansa ya ɗau waya ko makami yana hauka, yana tafka wa kansa, yana kururuwa yana cewa, “HUSANI, HUSAIN, HUSAINI!” kuma an jima kaɗan sai ka ga irin waɗannan mutane sun dawo suna ta ciye-ciye da shaye-shayen kayan zaƙi, suna ta dariya da raha shi kenan kuma, komai ya wuce, kuma yawancin ma ba su da addini .
Haka nan Hasan Jawad Mugniyah ya ce, “Dukan kai da makamai da zubar da jini sam ba Musulunci ba ne, babu wani nassi da ya zo da hakan, sai dai kawai nuna ƙauna ce da tausayi ga tsarkakan jinane da aka zubar a balahirar Karbala.
Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu
Allahu Akbar, ita dai gaskiya ɗaya ce, waɗannan malamai guda biyu Tijjani Samawi da Mugniya manyan malamai ne na Shi’a a wannan zamani waɗanda sun yi fice wajen kare Shi’anci da sukar Sunna, amma ka ji abinda suka faɗa, to kai ɗan uwa ya kamata ka san na yi, ka bar al’adun maguzawa, ka koma na Musulunci.
Kuma ka yi tunani, shin me yasa su manyan malaman da jagororin ba sa yin waɗannan ayyukan na hauragiya da ji wa kai ciwo? Ko su ba sa son Husainin ne? A ƙara tunani!
MATSAYIN SANYA BAƘAƘEN KAYA
Yan Shi’a suna sanya baƙaƙen kaya ranar Ashura, waɗansu ma tun daga farkon watan Muharram har tsakiyar watan Safar suna fama da baƙaƙen kayan da baƙaƙen tutoci, tare da cewa imamai sun ce, baƙaƙen kaya shigar ‘yan wuta ce, kuma shiga ce irin ta Fir auna. Ga wasu daga cikin waɗannan ruwayoyi:
1- An tambayi Imamu Sadik a kan hukuncin yin sallah da baƙar hula sai ya ce: “Kar ka yi sallah da ita saboda (sanya baƙaƙen kaya) shiga ce irin ta ƴan uwata. 2- An rawaito daga Amirul Mumini Aliyu (R.A) ya koya wa almajiransa cewa: “Kada ku sa baƙaƙen kaya, saboda shiga ce irin ta Fir’auna”.
3- An rawaito daga Annabi (S.A.W) ya hana sanya baƙaƙen kaya, sai dai rawani da huffi da mayafi.
Wani shaihin malami na Shi’a mai suna Alhaji Muhammad Rida AI-Husaini Aha’iri ya tabbatar da imanin malamansu a kan babu wani saɓani a Shi’anci kan haramcin sanya baƙaƙen kaya, ya yi wannan magana ce a littafinsa mai suna Najatul Umma fi Ikamatil Aza’i ala! Wannan mas’ala, wato Husaini Wal a Imma”. Sh. 83″.
To saboda Allah sanya baƙaƙen kayan nan ba kangarewa umarnin imamai ba ne? To mazhabin su wa ake bi ke nan?
HARAMUN NE MATA SU HALARCI HUSAINIYYA
A baya kaɗan mun kawo wasiyyar da Imamu Husaini ya yi wa mata a gab da shahadarsa, har ila yau, a cikin wasiyyar ya ce:
Ya ke ƴar uwata, ya ke Ummu Kulsum, ya ke Fatima, ya ke Rabab, ku nutsu idan na mutu kada ku yaga tufafinku, kada ku yakushe fuskokinku.
4 Kuma Abul Hassan da Abu Ja’afar (A.S) shi ma ya faɗa a kan fassarar faɗin Allah Ta’ala, “Kuma kada su (mata) su saɓa maka a kan wani abin alhairi? ya ce: “Manzon Allah (S.A.W) ya gaya wa Fatima (A.S) cewa: “Idan na mutu kar ki yakushe fuskarki, ka da ki cizge gashinki, kada ki yi min kururuwa, kar ki yi makoki. Sai ya ce, “wannan shi ne ma’anar abin da Allah y ke faɗa”.
Abu Abdullah (A.S) ya ce: “Ma’anar wannan ayar ita ce, ka da su yaga tufafinsu, kada su mari fuskokinsu, kada su yi ihu da kururuwa, kada su tsaya a kan kabari”
An karɓo daga Abu Sa’id Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Ya la’anci mace mai kukan kera da mai sauraro”.
To ƴan uwa mata (sisters) kun ji abin da Manzon Allah (S.A.W) da imamai (A.S) suka faɗa a kan matan da suke halartar Husainiyya, shin ko za ku bi maganar Manzo da ta imamai ku hutar da kawunanku daga zaryar da kuke ba dare ba rana domin kaucewa fushin Allah Ta’ala da Manzo.
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan
Ƴar uwa ki bi gaskiya, ki bi Allah da Manzo, ba jagororin gangan ba, waɗanda su suna hutawa cikin raɓa, suna kwasar girki, ku kuma kullum kuna kan hanya. Ni dai nasiha nake yi miki. Kuma gyara kayanka ba zama sauke mu raba.
AZUMIN RANAR ASHURA
Haƙiƙa azumin Ashura shi ne ya inganta daga Manzon Allah (S.A.W) da jikokinsa Ahlul baiti kamar yadda bayani ya gabata a baya.
IMAMAI SUN HANA AYOYI SU HALATTA
Abin mamaki shi ne duk da waɗannan ingantattun ruwayoyi daga Manzo (SA.W) da kuma Imamai (R.A) kan hana da la’anatar bukukuwan da ake yi na Ashura da sauran ranakun baƙin ciki da sunan Ahlul bait, da kuma Imama ciki da sunan jajantawa da ta’aziyyar tabbatattun bayanai daga manyan malamansu cewa:
Manzon Allah (S.A.W) da Imamai ba su yi waɗannan bukukuwa ba, ba a ma fara su ba sai a farkon ƙarni na biyar, abin da aka faɗaɗa a farkon ƙarni na biyar, abin da faɗaɗa a zamanin su Majlisi (ƙarni na sha ɗaya) wanda a lokacinsa aka fara wasan kwaikwayon Ashura, sannan Turawan mulkin mallaka suka ƙarfafe su a lokacin da suka yi wa Iraki mulkin mallaka, sai kuma a kwanan nan da Amerikawa da Yahudawa suka mamaye Iraki, abin ya ƙara taɓara ya fantsama a waɗansu wurare na duniya.
Amma duk da haka, waɗansu manya-manyan ayoyi sun saki fatawowi waɗanda kai tsaye suke ƙalubalantar nassosin Imamai suna halatta duk waɗannan abubuwan da Manzo da imamai suka haramta.
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan
Hujjarsu kawai ita ce, wai aiwatar da waɗannan bukukuwa suna nuna ƙauna da juyayi ga abin da ya sami Husaini da Ahlul baiti da kuma wai busawa mutane ruhin yaƙar danniya da zalunci (tada fitina) da kuma jan hankalin waɗanda ba su shiga addinin Shi’a ba, su yi sha’awa su shiga, kamar yadda Khumaini ya ba da wasiyya da kada a yi lako-lako da bukukuwan Ashura saboda su suke riƙe da addinin Shi’a”.
Kaɗan daga cikin waɗannan ayoyi da suka ƙalubalanci Imamai su ne: Khumaini, Khu’i, Tabataba’i, Shaharwardi, Al-Kashiful Gita’i da sauran su.
To abin tambaya a nan ita ce, shin maganar Allah Ta’ala da Manzo (S.AW) da Imamai (R.A) za mu bi, ko kuwa maganganun ayoyi da Mujtahidai da Maraji’ ai da jagorori? Ƴan uwa mu yi tunani. Ya Allah ka ganar da mu gaskiya ka ba mu ikon bin ta, ka ganar da mu ƙarya, ka ba mu ikon guje mata. Amin.
Daga ƙarshe wadannan bukukuwa na Ashura sun ƙunshi abubuwa da yawa da shari’a ta hana kamar:
1) Kururuwa da kukan kira
2) Yaga tufafi da marin füska.
3) Dukan jiki da zubar da jini
4) Wuce iyaka wurin yabon Husaini (R.A)
5) Tsine-tsine da zage-zagen da yakan haɗa har ɗa sahabbai. 6) Yin bakance (Alwashi) da sunan Husaini.
7) Kyale jahilai su yi ta wauta da ɓarna ba kwaɓa.
8) Cusa gaba haddasa fitina da rarraba kan musulmi.
9) Ƙin yin azumin ranar wanda shi ne tabbatacce. 10) Cutar da mutane ta hanyar haddasa cunkoso da dakatar da harkokin kasuwanci da sauransu.
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan