Tsarin Tazarar Haihuwa Mara Amfani Da Magani

0
61

Wannan tsari shi bature ya kira da calendar method ko calendar period wanda akan ƙauracewa saduwa a wasu keɓantattun kwanaki a yayin da ake neman kaucewa shigar juna biyu saboda wasu dalilai.

Wannan hanya ta ‘family planning abin da bincike ya tabbatar shi ne tana da sahihanci na kaso 88-95% cikin ɗari na hana shigar ciki. To sai dai duk da haka Allah yakan iya canja ikonsa koda an yi hakan kuma a samu haihuwa, Amma Insha Allah ba a cika samun ciki ya shiga ba idan aka kiyaye hakan. 

A jikin mahaifar mace, (Uterus) akwai wasu abubuwa kamar hannu guda biyu, ɗaya gefen dama dayan kuma gefen hagun wato bututun da ake cewa (FOLLOPIAN TUBE) a turance wanda ta ciki a rarake yake kamar pipe ɗin ruwa… to a can ƙarshe a bakin kowanne follopian akwai wani kwanson abu ƙullutu (Ovary) wanda a cikinsa ne akwai wasu ƙwayaye.

Duk sanda Mace ta yi haila bayan Jinin ya ɗauke da kwanaki 14, wancan abu da muka ambata da ƙullutu yana sakin waɗancan ƙwayayen, waɗanda su ne sinadarin da ake haɗawa a samu ɗa wato juna biyu.

Waɗannan ƙwayaye idan aka sake su sukan biyo bututun su shigo cikin mahaifar mace su yi kwanaki 2 wato awanni 48′ daga nan idan babu abinda ya zo ya taɓa su wato na daga maniyin namiji (sperm) to za su mutu. 

Toh sai dai kafin a saki waɗannan ƙwayayen su tafi mahaifa jiran maniyyin domin samar da ciki, akwai abinda Allah ya halitta a cikin mahaifar mace wanda kan zo ya share mahaifarta sosai (estrogen), domin mahaifar za ta yi baƙo, wanda baƙon kuwa shi ne wannan ƙwan.

Akwai wasu jijiyoyi guda biyu na jini, a gefen dama da hagu na mahaifar mace, idan aka zo aka share mahaifar to waɗannan jijiyoyin za su cika da jini sosai, sai su koma ja-ja-wur, suna jiran wannan baƙon da zai shigo mahaifa saboda su yi amfani da wannan jinin da suka cika kansu da shi su ba wa baƙon a matsayin abinci na tsawon awanni 48 da ƙwan kan iya rayuwa. 

Wanda in ƙwan ya zarce haka ba tare da maniyyi ya zo ya same shi ba, to lalacewa za yi ya mutu. Shi kuwa maniyyin namiji yana yin kwanaki 3 wato awanni 72 a cikin mahaifar mace kafin ya mutu, saɓanin na mace da ke kwana 2 (48hrs). Idan mun fahimci waɗancan bayanan da suka gabata, to yanzu sai mu haɗa su waje ɗaya mu ga yadda abin yake. 

Idan mace ta gama haila da kwanaki 14 to wancan abun mai kamar tiyo wato bututun (follopian tube) da ya haɗe kwanson OVARY zuwa cikin mahaifa (UTERUS) waɗannan ƙwayayen da ke cikin OVARY ta cikinsa suke shigowa cikin mahaifarta su jira maniyyin namiji ya zo ya same su wanda ake kira (OVULATION).

Idan sanda suka shigo mahaifa akai dace namiji ya sadu da mace dama ya zuba mata maniyyi ko da kuwa kwanaki 2 da suka wuce ne aka yi saduwar to komi ƙanƙantar maniyyin nan ya wadatar da su. maniyyin zai zamo musu kamar taki don haka za su baibaye shi su haɗu su yi ta girma babu zancen mutuwa kuma wanda da haka ne kuma Allah zai ta sarrafa shi har ya mai da shi jariri ya zamo mutum.

To idan kuwa sanda ƙwan ya shigo cikin mahaifa babu wani maniyyi da ya shigo gurin a dalilin rashin saduwa da macen da ba ai ba to waɗannan ƙwayayen za su mutu bayan sun yi awa 48 (kwanaki 2) kamar yadda na faɗa a baya cewa ƙwan mace bai wuce kwana 2 zai mutu in bai haɗu da maniyyi ba. 

Toh idan kuma suka mutu to za su biyo cikin al’aurar mace sai su fito, shi ne sai ka ji mata na tambayar sukan ga wani abu mai kamar majina-majina yana fito musu a al’aura ta wani lokaci, wanda wannan shi ne abinda ke fitowar ba wai infection ba ne. Kuma in ‘yan mata ne da za ku lissafa za ku ga sanda yake fitowar a ƙalla lokacin kun yi ko kun kusa sati 2 da gama haila.

Wannan yasa malaman mu a misulunci ke cewa babu komai akan wannan abun in mace ta  gani kawai ta wanke shi ba shida wani hukunci, ba wanka ake ba. Amma indai ba sau 1 a wata take ganin wannan ba kuma ya zamto ba irin wajen sati 2 ne da gama haila ba to ƙila abinda kike fitarwa wannan yana da alaƙa da INFECTION musamman idan dususu yake ko kuma kika ji ma yana ƙarni. 

Duk hakan ya faru ne a dalilin rashin shigar maniyyi da zai girmar da wancan ƙwan, tunda kun ga budurwa dama ba aure gare ta ba. 

Dalilin rashin maniyyin bayan ƙwan ya lalace ya fita su kuma waɗancan jijiyoyi da suka tara jini a cikinsu, sai su yi wani abu da ake kira fushi, ba su ji daɗi ba, a dalilin haka sai suke kartar jikin mahaifar mace, sai ka ji mace tace maka tana yawan fama da ciwon mara (lower abdominal pain) musamman idan ta gama Haila. A nan za mu fahimci rashin aure na daga abunda ke jawo wannan, kuma maganin haka shi ne aure duk da akan samu masu auren na fuskantar hakan.

Don karanta lokacin da ya dace mace ta yi amfani da tazarar haihuwa danna nan

Idan karce jijiyoyin nan ya yi yawa kuma aka yi rashin sa’a sai su fashe, idan kuma suka fashe sai jini ya yi ta fita ba tsayawa a wasu, wannan shi ne ake kira da jinin Istihada, daman Manzon Allah (SAW) ya taɓa gayawa wata mata cewar ai wannan jinin na jijiya ne. 

Dan haka idan mace me aure ce kuma tana son yin ‘family planning da mijinta, to hanya mafi sauƙi ita ce; kamar yadda muka ji bayan gama hailar ta da kwanaki 14 ake sakin waɗancan ƙwayaye zuwa mahaifa, kuma sukan yi kwanaki 2 kafin su mutu, shi kuma maniyyin namijin yakan yi kwanaki 3 kafin ya mutu. To su ma’auratan kada su yi jima’i tun ranar 11 da gama hailar ta, har sai bayan ranar 17 da gama hailar ta. 

Ku ɗan tsaya kaɗan a nan kafin ku cigaba ku yi tunanin me yasa nace haka??

Dalilin hakan kuwa shi ne; ranar 14 ƙwai ke zuwa, to idan suka sadu ranar 12, kada mu manta maniyyi sai ya yi kwanaki 3 kafin ya mutu, to kun ga idan suka sadu ranar 12, maniyyin namijin na nan a mahaifar a raye har ranar 14 da za a sakin ƙwan, zai zauna na tsawon kwanakin 12,13,14 kafin ya mutu, to kun ga za su ci karo ranar 14, kuma babu abinda zai hana shi sarrafa ƙwan nan. 

An ce kar ku sadu har sai bayan ranar 17 ne saboda shi kuma ƙwan yakan yi kwanaki 2 kafin ya mutu. To waɗannan kwanaki 5 ɗin-12,13,14,15,16 da gama Hailar mace, su ake kira da ‘DANGER PERIODS’ Ma’ana kwanaki masu hatsari, an kira su da haka ne saboda idan dai aka sadu da mace a waɗannan kwanakin to kuwa tabbas za ta samu ciki, sai dai idan mulkin Ubangiji ya shigo ciki ko kuma in dama cikin ma’auratan akwai larurar da ke hana ɗaukar ciki. 

Amma idan har ma’aurata na son yin ‘family planning’ ba tare da sa ko shan komi ba waɗannan kwanakin za su kaucewa saduwa a ciki wato tun daga ranar 11 da gama haila har sai ranar 17 da gama haila, sati 1 kenan.

Sannan kuskuren dakan faru wasu na zuwa da sunan a sadun amma in ya ji zai kawo sai ya zare. Ina mai tabbatar ma wannan ruwan me santsi na maniyyi da kan fara fitowa ka zaci maziyyi ne shi kansa ya wadatar yasa ciki ya shiga domin akwai maniyyi daga ƙarshensa. Wannan tasa ‘yan matan da kan auka tarkon samari ke ƙarewa da ciki a zaton ba ai release jikinsu ba, don haka in dai za a yi to a kiyayi kusanta kurum.

Kuma irin hakan yasa ba a ba hanyar inganci 100% ba domin ko yaya maniyyi yake ya wadatar. Haka kuma wasu matan duk sati 3 suke haila don haka kwanakin fara ovulation ɗinsu ba zai kai har 14 ba, galibi bayan kwana 10 ovulation na iya faruwa, kun ga ita sai dai a ƙaurace mata kwanaki 8 zuwa 13.

Sannan wani abu; a yayin da ƙwan can ke tafiya a cikin FOLLOPIAN TUBE daga ovary zuwa cikin mahaifa idan ya maƙale a hanya kuma aka zo aka sadu da mace toh shi ne maimakon ciki ya kasance a cikin mahaifa sai ya kasance a wajen mahaifa wanda shi muke kira ECTOPIC PREGNANCY.  Wanda dole sai dai a yi aiki a cire. Kuma wannan follopian tube ɗin ya samu matsala kenan har abada. Sai dai da yake biyu ne, to ɗaya ya isa ta samu ciki da shi. Wata hikima ta Allah shi yasa ya yi biyun. To inko duk biyun suka ta6u aka kuma samu ectopic to fa shi ne ciki sai dai a yi wa mace dashensa, gaskiya ba za ta iya ɗauka ba. 

Wanda Pelvic inflammatory disease na daga kan gaba abinda ke jawo tangarɗar Follopian tube ɗin don haka mata ku daina sake da infection, a kuma daina amfani da wani maganin matsi ko tsarki da ruwan sassake-sassake in kun ƙi kuma to jiki magayi. A kuma lura da tsafta.

Danna nan don karanta yadda za a magance ɓallewar jini bayan haihuwa

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

 

labarin da ya wuceAuren Sayyadi Abdullahi Da Sayyada Aminatu
Labarin na GabaHani Akan Yin Duba 1