Inganta Rayuwar Ma’aurata Ta Hanyar Karin Magana

0
1321
INGANTA RAYUWAR MA’AURATA TA HANYAR AMFANI DA KARIN MAGANA
A cikin wani littafi da na rubuta mai suna,“Kimiyya Da Fasahar Zaman Aure’ na yi wani fasali da na kawo karin magana guda ɗari da ashirin da takwas a cikinsa, waɗanda nake ganin da ma’aurata za su yi amfani da su a rayuwarsu ta aure, da sun warware masu matsaloli masu yawa; da kuma sun zauna lafiya cikin jin daɗi da rufin asiri.
Ganin irin muhimmancin karin magana yake da shi a kowane fanni na rayuwa, na ga ya kamata na ɗan tsakuro kaɗan daga cikinsu, domin faɗakarwa da hannunka mai sanda ga yan’uwa musamman ma’aurata.
1.GANI GA WANE, YA ISHI WANE TSORON ALLAH.
GANIN BUZU A MASALLACI, YA ISHI AKUYA TSORON ALLAH
Tsokaci:
Ya kamata idan wani ya yi wani kuskure a zaman aurensa, mace ko namiji, kuma har wannan kuskuren ya haifar da damuwa da ɓacin rai da nadama da wani mummunan sakamako ga ma’aurata, to  sai ku kuma da ba ku shiga irin wannan taskun ba, ku kaucewa aikata irin wannan kuskuren, wannan ya zama wa’azi a gare ku.
2.YANZU YANZU SAI ALLAH.
Tsokaci:
Duk abin da kuke so, ko kuma wanda ba kwa so, ba za ku iya tabbatar da shi ko kawar da shi nan take ba, dole sai a hankali, saboda cuta lokaci guda take shiga, amma waraka sai a hankali. Kuma ɓarna ce ake yin ta yanzu, amma gyara sai an ɗauki lokaci. Sai ka ga an yi shekaru ana gini, amma a ‘yan awanni sai a iya rusa shi, a sake wasu shekarun ba sake gina shi ba.
3. BA A ƁARI A KWASHE DAIDAI.
In dai aka yi wa rayuwar aure sartse, kamar aka yi saki aka dawo, ko aka yi wata hatsaniya aka daidaita ,to fa yana da wahala a koma kamar yadda ake a da. Saboda haka a guji abin da zai kawo fitina a rayuwar aure, In kuma ta faru, an daidaita ,to sai a yi haƙuri da abin da ya samu.
Misali wacce rikici ya kai har sai da aka sake ta, aka auri wata sannan aka dawo da ita, to ka ga ai ta rasa matsayinta na uwargida, kuma in ta ce lallai sai ta koma kamar yadda take a da, to fa kamar tana neman ɗaukar Dala ne ba gammo.
4.HANA WANI, HANA KAI
Tsokaci:
Kada garin fushi ka hana matarka haƙƙinta, ko ki hana mijinki haƙƙinsa. Misali ki ce ba za ki yi abinci ba, ko kai ka ce ba za ka ba ta abinci ba, sabo da yin hakan ba zai damu wanda aka yi don shi ɗin kaɗai ba, a’a, har shi ma wanda ya yi, sai abin ya dame shi. Saboda haka kada a je garin ramuwa a rame.
5.ALLAH ƊAYA GARI BAMBAN
Ya kamata ma’aurata su fahimci halayen junansu, su yi haƙurin zama da halin juna, saboda Allah bai yi mutane ɗaya ba, kuma In ka san halin mutum, tabbas ka sha maganin zama da shi.
Bari in tsaya a nan ,sai a faɗaɗa tunani, ni kam sai wani jiƙon, wai kare ya zubar da tsamiyar kura.
labarin da ya wuceMummunan Ƙarshe Da Kyakkyawan Ƙarshe
Labarin na GabaYadda Ake Haɗa Fondant