Sujjadar Rafkanuwa

0
30

Sujjadar rafkanuwa sujjadu ne guda biyu da ake yi a madadin mantuwa da aka yi a cikin sallah saboda dalilin yin ƙari ko ragi. 

Matsayin sujjadar mantuwa ko rafkanuwa (sahwu) a cikin sallah sunnah ce, saboda hadisin Ibn Mas’ud رضي هلال عنه Manzon Allah وسلم عليه هللا صلى Ya ce: “سجدتين إذا نسي أحدكم فليسجد” Ma’ana “idan ɗayanku ya yi rafkanuwa a sallah, ya yi sujjadu guda biyu” (Muslim, 402). 

A cikin hadisin Dhul-Yadaini, Annabi وسلم عليه هللا صلى Ya yi sallah tare da sahabbai رضوان هلال علهبم da yammaci (Azahar ko La’asar), Ya sallace ta da raka’a biyu, ya yi sallama. Sai wani mutumin ya tambayi Manzon Allah وسلم عليه هللا صلى a game da rage sallah. 

Domin Karanta Bayani akan Yin Jadawalin Ayyukakn Rana Da Yini A Rubuce Danna Nan

Sai Shugaba وسلم عليه هللا صلى Ya tambayi sahabbai kan abin da Dhul-Yadhain ke magana a kai, suka amsa da cewa, E! AI AN RAGE SALLAH. Sai Manzon Allah هللا صلى وسلم عليه Ya yi kabbara ya cika raka’o’in da Ya bari, ya yi sujjada guda biyu bayan sallama (ba’adi), Ya sallame2صلى هللا عليه وسلم

A (wata) ruwayar ta Abdullahi bin Buhainatu ريض هلال عنه, Annabi وسلم عليه هللا صلى Ya sallaci sallar Azhar tare da sahabbai رضوان هلال علهبم, sai ya wuce bai yi tahiya ta farko ba. Bayan ya yi tahiyar ƙarshe, sai ya sake kabbara, ya yi sujjada (qabli), ya sallame3صلى هللا عليه وسلم

Ibn Mas’ud رضي هلال عنه ya ce: Manzon Allah وسلم عليه هللا صلى Ya yi sallar Azhar raka’a 5, sai sahabbai suka tambaye shi “shin ko an qara sallah ne?” Sai ya yi sujjadu biyu (2) bayan sallah (ba’adi)

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna Nan

labarin da ya wuceKoyi Da Annabi Muhammad (S.A.W)
Labarin na GabaNau’o’in Sujjadar Rafkanuwa