Yin Jadawalin Ayyukakn Rana Da Yini A Rubuce

0
26

Yin jadawali (Time-table) ga musulmi ya sha bamban da yadda yan duniya ke tsara jadawalinsu. Musulmi zai yi jadawalinsa ne yana mai rinjayar da abubuwan da za su jawo masa ribar lahira da yarda da Ubangiji. 

Ƴan duniya kan tsara lokutansu ta yadda za su sami damar yin wasanni kamar shaƙatawa a bakin ruwa, ko don yin guje-guje da tsalle-tsalle, ba tare da bawa mahaliccinsu wani kaso ba. Shi kuwa Musulmi zai tsara mafi yawan kason lokacinsa ga Ubangiji Maɗaukaki ta yadda barcinsa da shaƙatawarsa duk za su zamo ibada. 

Manzon Allah (S.A.W) ya nuna cewa, “Hatta mutum ya biya buƙatarsa da iyalinsa ma lada ne, matuƙar ya bi koyarwar Manzon Allah (S.A.W) “. 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

Da mutum zai tsara ranarsa da ayyukansa ta yadda za a ware awa guda a kowace ranar aiki daga Litinin zuwa Juma’a, da zai samu kimanin awoyi 260 a shekara. Wadda wannan ya yi daidai da kwana talatin ma’ana wata guda cur. A lokacin kuwa na tabbata mutum zai iya abubuwa masu amfani ga rayuwarsa misali: 

  • Zai iya haddace wasu sassa na Alkur’ani. 
  • Zai iya sauke wani littafi na fiƙhu ko Hadisi. 
  • Zai iya koyon wata ƙwarewa(kamar kwamfuta). 
  • Zai iya koyon wani harshe kamar Larabci ko Turanci ko Faransanci. Zai iya rubuta wani babi na littafi mai amfani ga musulmi. 

Zai iya yin kos ɗin Diploma a tsarin (Distance learning).

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceHukuncin Kiɗa A Musulunci
Labarin na GabaƘa’idoji Goma Sha Ɗaya Na Samun Nasara A Rayuwa