Description
Lahira da al’amuranta ba a hangen su, sai dishi-dishi. Hazon son zuciya ya baibaye idanun masu idanu. Shaiɗanun mutane da shaiɗanu aljanu sun haɗa kai kullum suna ƙara nuna alamomin lahira da ƙarewar duniya kamar wata kawalwalniya ce, koma mu ce tatsuniya.
Ƴan korensu na ƙara baje kolin kayan sheƙe aya a sararin duniya. Muryoyin mawaƙa na ƙara zaƙi. Zabiya na ƙara shela a zo a hole a sha shagali. Hotunan tsiraici a tituna da fina-finai da fasadi a talabijin sai ƙara yawaita suke yi.
Rumasa’u Muhammad Kallamu –
All contents in this book have been posted.