Description
Bayan haka, Allah Maɗaukakin Sarki ya sanya wannan addini ya dace da rayuwa
da juyawar halaye na ɗan Adam. Komai yana da hukuncinsa da matsayinsa a cikin
Shari’ar wannan addini. Saboda Allah Maɗaukaki shi ne ya halicci ɗan Adam kuma
shi ya saukar da Shari’ar (Al-A’raf:54; Al-Mulk:14).
Nassoshin da a ka saukar ƙididdigaggu ne, sai dai abin da suka ƙunsa kuma yana
da faɗin da zai amsa duk tambayoyi-waɗanda su kuma ba su da iyaka kullum cikin
faruwa suke1
– da za su tasowa mutane a kowane lokaci. Wannan shi yake
tabbatar da cewa Ijtihadi-ko na ɗaiɗaiku ko na jama’a- ba zai tsaya ya dakata ba a
cikin wannan al’umma
Reviews
There are no reviews yet.