Description
An haifi Annabin rahama, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ranar Litinin sha biyu ga watan Rabi’ Awwal, shekarar giwaye, wadda tayi daidai da shekara ta ɗari biyar da saba’in (570) bayan haihuwar Annabi Isa, amincin Allah ya tabbata a gare shi, yayin da sojojin Habasha suka kawo mamaya ƙasar Makka da nufin rushe ɗakin Ka’aba, amma suka gaza cimma nasara.
An haifi shugaban halitta, mai suna Ahmad, abin yabo Muhammad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a garin Makka. Annabi Ibrahim wanda shi ne Jagoran kaɗaita Allah, shi ya gina cibiyar ƙasar Makka, wato ɗakin Ka’aba. Har wa yau kuma shi ne kakan Larabawa da Yahudawa.
Reviews
There are no reviews yet.