Ita masa’alar koyi abu ne wanda ya ke haɗe da halittar ɗan adam. A farkon rayuwar dan adam ya kan fara koyi da duk abin da ya ga ana yi, ko daga wajen wa ya ga abin.
Yayin da ya buɗe ido ya gane iyayensa, to sai kuma ya koma koyi dasu. To shi kansa wannan matakin akwai matsalarsa, idan ya zama su iyayen ba a kan shiriya su ke ba. Shi ya sa alƙur’ani ya yi ta fama da masu maƙalƙale wa iyayensu wajen koyi da su a mummunar hanya. Misali, inda Allah (SWT) yake cewa:
“Idan aka ce dasu: “Ku bi abin da Allah ya saukar. Sai suce “A’a, mu kawai za mu bi abin da muka saba iyayenmu suke kai ne. (Allah SWT yace: “Yanzu sa sa riƙa bin iyayen nasu) Ko da iyayen nasu bas u da hankalin fahimtar abubuwa, kuma basa kan shiriya?” (Suratul Baƙarah, aya ta:170).
Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan
Wani lokaci kuma mutum ya kan ga wani wanda ya burge shi a wata ƙwarewa ta rayuwa, misali: kwararren mai tunani wanda ya ƙirƙiri wata hanya ta rayuwa. (kamar kwamanisanci, ko jari hujja. Ko wanda ya ƙirƙiro wani tsari na shugabanci. (kamar damakwaraɗiyya) ko ƙwararren ɗan siyasa wanda ya yi shuhura.
Ko ma ƙwararren ɗan wasa ko ƙwararren jarimi a wani fim ko wasannin kwaikwayo. Idan ba a yi sa a ba sai mutum ya kama ɗaya daga cikin waɗan nan ya zam abin koyinsa a rayuwa. Ka ga an shiga cikin ɓata marar iyaka.
Wannan ya sa Allah (SWT) ya yi ta aiko da manzanni domin a yi koyi da su, Allah (SWT) yana cewa:
“Waɗannan su ne waɗanda Allah ya shiryar. Ka yi koyi da shiriyarsu” (Suratul An’am aya ta:90).
To kasancewar Annabinmu (S.A.W), shi ne na ƙarshe a cikin manzannin Allah, sai ya zama shi Allah ya sanya mana ya zama abin koyinmu. Allah (SWT) yana cewa:
“Haƙiƙa kyakkyawan koyi ya tabbata a gare ku, daga Manzon Allah, ga wanda ya ke ƙaunar Allah da (kyakkyawar makoma daga) Allah da ranar lahira, kuma, ya ambaci Allah da yawa” (Suratul ahzabi, aya ta:21).
Wannan ya nuna wajibcin sanya shi abin koyi a dukkanin hanyoyin rayuwa.
Koyi da Annabi Muhammad (S.A.W) a dukkanin tsare-tsaren rayuwa:
Duk Wanda yace shi Musulmi ne, to lallai ne abin koyinsa ya zamo Manzon Allah (S.A.W), a dukkanin tsare-tsare na rayuwarsa. Misali: Tsarin Ilimi, tsarin zamantakewa, tsarin tattalin arziƙi, tsarin siyasa (shugabanci) da tsarin shari’ah.
Abin nufi a nan shi ne, duk waɗan nan tsare-tsare na rayuwa su zamo a kan tsarin alqurani da sunnah, bisa fahimtar magabata na ƙwarai. Ka da mutum ya zama sai a sallah, Azumi, aikin Haji kaɗai, ya ke Musulmi. Watau ya zama yana bin tsarin da ya saɓa wa na Allah. Allah (SWT) Yana cewa:
“Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku shiga Musulunci gaba ɗaya (watau ku miƙa wuya gaba ɗaya). Kada ku bi takun sheɗan, ba na Allah ba). Shi abokin gaba ne a gare ku, bayyananne” (suratul BAƙarah, Aya ta: 208).
Abin takaici shi ne, a halin da muke ciki a yanzu, za mu ga cewa a dukkanin tsare-tsaren nan na rayuwa babu wanda muke tafiyar da shii a kan tsarin da Annabi Muhammad (S.A.W) ya zo da shi. Misali: Tsarin Iliminmu ba ya koya mana tauhidi da tsoron Allah da ranar lahira da tarbiyyar Musulunci.
Domin Karanta Bayani akan Yin Jadawalin Ayyukakn Rana Da Yini A Rubuce Danna Nan
A tsarin zamantakewa. Idan muka ɗauki zamantakewarmu ta aure da zaman iyali, ba akan alƙur’ani da sunnah take ba. Tsarin Tattalin arzikinmu cike yake da cin hanci da rashawa, cin riba, gululu’ (Watau satar dukiyar jama’a) da sauransu.
Tsarin siyasarmu (shugabanci) tsari ne na Damakwaraɗiiyya, wanda babu Allah a cikinsa. Shi kuwa tsarinmu na shari’ah kowa ya san dokokin ƴan adam mu ke fifitawa a kan dokokin Allah (SWT). Abin nufi a nan shi ne, son Annabinmu na baka ne kawai. Ba a aikace ya ke ba. Gashhi kuwa Allah (SWT) yana cewa:
“Gaya musu, idan kuka kasance kuna son Allah, to ku bi ni, sai Allah ya so ku, ya gafarta muku zunubanku. Allah mai gafara ne, mai rahama” (Suratu Ali Imrana, Aya ta:31).
Allah (SWT) yana cewa: “Ka ce musu Idan iyayenku da `ƴa`ƴanku da ‘yan uwanku, da matanku, da danginku da dukiyoyinku da kuka nema da hanyar samunku da ku ke gudun ka da ta yi tasgaro da gidajen da ku ke jin daɗinsu, su suka fi soyuwa a gare ku, maimakon Allah da Manzonsa, da ƙoƙarin tabbatar da tsarinsa, to ku zauna, har sai Allah ya zo da lamarinsa (Mutuwa ko halakarwa). Allah ba ya shiryar da mutane fasiƙai” (suratul Taubah, Aya ta:24).
Wannan duka yana nuna cewa ba za mu zama Musulmi ba sai mun gudanar da kowane ɓangare na rayuwarmu bisa tsarin Allah. Wannan kuma ba zai samu ba sai ta hanyar koyi da Annabi Muhammad (S.A.W), watau ta hanyar riƙo da alƙur’ani da Sunnah. Annabi(S.A.W) ya ce:
“Na bar muku nauyaya guda biyu, ba za ku ɓata ba, matuƙar kun yi riƙo da su: Littafin Allah da sunna ta”
Yadda Sahabbai Suka Yi Koyi Da Annabi Muhammad (S.A.W):
Sahabban Annabi Muhammad (S.A.W) sun yi koyi da shi a cikin dukkanin harkokin rayuwarsu. Ba kawai sai a salla, Zakka, Azumi da Hajji kaɗai ba. Ga wasu misalai `ƴan kaɗan da za su nuna mana haka.
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna Nan
Dab da Annabi Muhammad (S.A.W) zai yi wafati ya zartar da wata runduna ta yaƙi, ƙarƙashin shugabancin Usamatu bin Zaid. Bayan wafatin annabi Muhammad (S.A.W) sai wasu su ke ganin ya kamata a dakatar da wannan runduna tukunna, kasancewar an sami wasu suna ƙin bayar da zakka. Har ma aka zama cikin tsoron kawo hari cikin Madina. Me Abubakar yayi a matsayinsa na shugaba? Abubakar bai yarda a dakatar da wannan runduna ba. Cewa ya yi:
“Ba za ta yiwu ba a gare ni na kwance tutar da Manzon Allah (S.A.W) ya qulla”.
Haka nan sauran sahabbai suka goyi bayan Abubakar, Usamatu ya shugabanci wannan yaƙi kuma aka yi gagarumar nasara.
Game da Madina kuwa, abin da Abubakar ya yi shi ne, sai ya sanya wasu daga cikin manyan sahabbai suka shugabanci wata runduna domin ba ta kariya, kamar su: Aliyu bin Abi Ɗalib, zubairu binil Auwam, sa’adu bin Abi Waƙƙas, Abdullahi bin Mas’ud da abdur Rahman bin Aufin12.
Wani abin da sayyidina Abubakar ya yi (na ruƙo da tsarin Annabi) bayan wafatinsa (S.A.W), wanda ya ke nuna dagewarsa, shi da sauran sahabbai, a kan Sunnar Annabi Muhammad (S.A.W) (wato tsarin sa na rayuwa) shi ne, wasu Larabawan ƙauye sun ƙi bayar da zakka bayan wafatin Annabi Muhammad (S.A.W). A wannan lokacin cewa ya yi:
“Wallahi! Idan da za su hana ni dabaibayi, wanda suka kawo wa Manzon Allah (S.A.W), da sai na yaƙe su”.
Wani abin da za mu sa ke lura da shi shi ne, yanayin da Nana faɗimah `ƴar Manzon Allah (S.A.W) ta nemi gadon Annabi Muhammad (S.A.W), a nan ma sai ya ce mata ya ji Manzon Allah ya ce:
“Mu jama’ar Annabawa ba a gadon mu. Abinda muka bari, sadaka ne” (Bukhari da muslim ne suka ruwaito).
Wani misali shi ne, wata rana sayyidina Umar ya zo zai sumbaci Hajarul Aswadi sai ya tsaya ya ce: “Ni na san kai dutse ne. Ba ka cutarwa, ba ka amfanarwa. In ba domin na ga Annabi (S.A.W) ya sumbacce ka ba, da ba zan sumbace ka ba”. (Bukhari ne ya ruwaito).
Wata rana Abdullahi bin mas’ud ya zo zai shiga masallaci sai ya ji Annabi Muhammad (S.A.W) yana cewa: “A zauna”. Sai ya zauna a kan dokin ƙofar masallaci. Bai ƙara yin gaba ba ko kaɗan, sabo da cika umarni.
Haka nan sahabbai suka yi ta koyi da Annabi Muhammad (S.A.W), a dukanin tsare-tsaren rayuwa.
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna Nan