Illolin Wasu Daga Kayan Ado Da Na Kwalliya

0
35

Abu ne mai kyau mu zayyana kaɗan daga wasu kayan kwalliya na tufafi da shafawa da sauransu, waɗanda za su iya zama illa ga mace don su nisance su, saboda ta yi amfani da nau’in kayan kwalliya da zabsu biya mata buƙatarta ta ado, ba ta kauce ƙa’idojin Mahaliccinta ba , kuma ba tare da ta cuci kanta da kanta ba. 

Matsattsun Kaya

Sanya matsattsun kaya ga wasu mata ya zama ruwan-dare gama duniya. Irin waɗannan mata sukan fifita kayan da za su matse jikin tamau! Yadda za a iya ganin ƙirar jikinsu. Sosai, masana da yawa sun yi tsokaci a kan irin waɗannan kaya, ta fuskokin ilmi daban- daban. 

Domin karanta bayani akan Muhimmancin Ado Da Kwalliya A Musulunci Danna nan

A ɓangaren kiwon lafiya, ana ganin irin waɗannan ɗamammun kaya suna tsananta matse jikin mace, haka kuma yana azabtar da ita sosai, ta hanyar takura ta, da rashin samun walwala, saboda haka yawan sanya irin waɗannan kayan zai sanya mace yawan jin damuwa a ranta. 

Haka kuma matsewar da tufafi ke wa jiki zai takurawa tsarin zagayawar jini a jijiyoyinta, wannan kuma zai iya sabbaba mata cutar hauhawan jini. 

Domin karanta bayani akan Tabbancin Halaccin Ado da Kwalliya A Musulunci Danna nan

  • A wani faɗin ma, wasu masana cewa suka yi; “Yawaita sanya matsattsun kaya, zai iya hana wa mace haihuwa, ko kuma ya yi sanadin samun tangarɗar haihuwar”. 

Tufafi masu Bayyana Fatar jiki

Ƙoƙarin kwaikwayon kangararrun Turawa, yasa wasu matan musulumi, suna sanya tufafi masu bayyana wasu sassa na jikinsu, yadda za a iya ganinsa ƙarara, kamar gadon baya ko faɗin ƙirji ko sha-raba, da dai sauransu.

Domin karanta cikekken littafin Danna nan 
labarin da ya wuceTabbancin Halaccin Ado da Kwalliya A Musulunci
Labarin na GabaDunƙulallun Matsaloli A Musulunci