Tabbancin Halaccin Ado da Kwalliya A Musulunci

0
24

Wata aya ta tabbatar da cewa ado na Allah ne, don haka babu wanda zai haramta wa bayinsa kayan da ya fitar don amfaninsu. kuma shi ado da kayan daɗin duniya na halak, duk an fitar da su domin Musulmi su more su a duniya , haka kuma a lahira su kaɗai ne za su sha daɗin waɗannan ni’imomi. Ayar tana cewa: 

“Ka ce wane ne ya haramta kayan Ubangiji na ado da kayan daɗi na halal wanda ya fitar da su ne, don amfanin bayinsa, ka ce wannan (duk) na musulmi ne duniya, kuma a lahira su kaɗai ne za su more su”.Al-A’raf:32. 

A nan za mu ga cewa, Allah Ta’ala ya yi tsawa ga wanda ke ƙoƙari haramta wa musulmi more kayan ado da na halal, kuma ya jingina ado ya zuwa ga zatinsa saboda ya ce, (ado Ubangiji), sannan kuma Allah ya tabbatar da cewa musulmi tun a duniya , ya 

halatta su more waɗannan ni’imomi, bugu da ƙari a lahira su kaɗai ne ma za su amfana da su. 

Domin karanta bayani akan Muhimmancin Ado Da Kwalliya A Musulunci Danna nan

Allah Ta’ala mai Kyau ne, kuma yana son abu mai kyau. 

Magana a kan matsayin ado da ƙaye a addinin Musulunci ba za ta cika ba, har sai an kawo Hadisin Manzo Allah (S. A.W) da ya ke cewa: 

“Haƙiƙa Allah (Ta’ala) mai kyau ne kuma yana son abu mai kyau”. (Hadisi ne ingantancce). 

Saboda haka duk abin da za a faɗa an yi ne don a hana su kyautata jikinsu da ƙawata kansu ba ne, sai dai a faɗakar da su a kan abin da zai iya zame masu illa idan sun saɓawa ladubban ado da kwalliyar tasu a Musulunci. 

Tabbas, a irin yadda kwalliyar mata ta zamani take, tana buƙatar mata Musulmi su yi mata gyare-gyare, akwai nau’o’i da yawa na kayan sawa da na kwalliya, waɗanɗa suna iya zama matsala gare su, a kan haka bai kamata garin kwalliya a jawo wa jiki illa ba, ko kuma a jawo wa aljihu ko jaka naƙasu ba! Ko Hausawa ma suna cewa: “kada garin gyaran gira a tsone ido”!

Domin karanta cikekken littafin Danna nan 
labarin da ya wuceTSUMAGIYA
Labarin na GabaIllolin Wasu Daga Kayan Ado Da Na Kwalliya