TSUMAGIYA

0
27
  1. A ci a cinye, abin da aka samu ya fi a sabunta kayan sana’a. 
  2. A wanke jiki a wanke kaya fes, amma fa gaban gida da layukan unguwa cike fal da tsibi-tsibin shara. 
  3. Abin mamaki. Daga zato sai ka yanke hukunci. 
  4. Aibata wanda ba sa so; da ɓata shi duk nagartarsa. 
  5. Ashe dama maza suna iya cakuɗa da mata, idan kallon hawan sarki ne ya haɗa su? 
  6. Assha maza da gulma, mata da tsegumi. 
  7. Ba da ni ba, yiwa mai kuskure uzuri. 
  8. Ba ku san mu ba ne, mu ne ‘yan-ina-da-laifi mu yayata. 9. Babu ruwana da ƙaramar sana’a; tun da idan na yi ‘yar murya, zan samu na kashewa. 10. Babu wani ɗa banda ɗana. 
  9. Bakin rai,bakin fama, sai mun ga bayan masu son a kawo gyara. 12. Barin ‘ya’ya sasakai suna gararanba a gari. 
  10. Barin abin da aka ci aka rage, ya lalace, ya fi aba wa mabuƙacin da zai mora. 
  11. Buƙatuna suna da yawa; me zan yi da ƙaramar sana’a. 15. Da biyan kuɗin makarantar ‘ya’ya, gara bayar da kuɗin sayen atamfar anko. 16. Da na rufa wa kaina asiri; gara na tona.( inji mutumin da ya kasa riƙe sirrinsa). 
  12. Da neman ilmi, gara zama da jahilci. ( kamar yadda aikin wasu daga cikinmu yake nunawa). 
  13. Da sana’a gara maula. 
  14. Da sayan nagari da za a daɗe ana mora, gara sayen mai arha ko da ba zai biya buƙata ba. 
  15. Da wani ya samu shi ya rasa gara kowa ma ya rasa wato (taɓare Kenan). 21. Da yafiya; gara ƙullatar abokin saɓani.
  16. Da yarda da matsayin da ake kai, gara ƙaryar matsayin da za a kere sa’a da shi. 
  17. Da zama a yi karatu, ko kwanciya a huta, gara zaman tsegumi da gulma. 24. Dokar banza, dokar wofi, ma dai tursasa a bi ta, ba dai mu mu bi ta ba, inji jami’in tsaro. 
  18. Faɗa da gaba da wanda ya fito fili ya faɗi gaskiya. 
  19. Fifita alfahari da magabata a kan yin irin abin da suka aikata har ake alfahari da su. 
  20. Gara ‘yan iskan gari su yanki ɗana; da malami ya doke shi. 28. Gara ina gefe da a ce da ni aka kama mai laifi. 
  21. Haba masu damar ƙari; a motsa ai yafi a daskare. Saƙo daga gungun zawarawa da ‘yan mata. 
  22. Haɗamar sana‘o’i da ayyukan yi, ya hana mu abin yi guda ɗaya ƙwaƙƙwara. 31. Idan kana so mu shirya; to ka goyi bayana a kan rashin gaskiya. 32. Ka gan ni nan; siyasa ce sana’ata 
  23. Ka ji da kyau, ba a komai nake bin addini ba. 
  24. Ka tausaya ka jiƙan sa, bayan ya murmure ya bi ta kanka. 35. Karatu ya koma biki a wajenmu. 
  25. Karatun boko ya fi na addini. Don na kasa biyan kwabon islamiyya na biya wa boko dubu. 
  26. Kayan aro, kasanmu na gado. 
  27. Ke yunwa amma dai da yankan ƙauna kike, ki rasa wanda za ki kayar sai malam matsolo. 
  28. Ko kun ƙi, ko kun so, mu za mu ci gaba da mulkarku.( inji honorabul a ranar zaɓen tazarce).
  29. Kowa da fagen da ya ƙware, inji mai rancen kadarar Naira dubu ya karyar da ita a kwabo, don kece raini da bushashar rayuwa. 
  30. Kowa ma ya mutu, in dai ba za a ƙara mana kuɗin alawus ba. 42. Kowa ya yi abin da ya iya, idan ka sato ka kawo min na saya. 43. Ku kai ni, yanzu zan dawo.( inji ɓarawo a hannun ‘yan bijilan). 
  31. Ku ku ci a gwamnati,mu maci a islamiyya da masallaci.( In ji limamin da ya cinye ƙudin kwamitin gyaran islamiyya da masallaci). 
  32. Ku ƙari kururuwarku, an ce da mai neman haram; Allah yana madakata. 46. Kuna ina? Na ɗauke muku yadda za a yi a samu cikin, ku kuma ku tsaya min da ƙudin hayar gida da ragon suna. 
  33. Kushe abin alherin da baƙo ne ya fare shi. 
  34. Kwabon da zan samu, ya fi raina da lafiya ta.( inji mai bara da mai sana’a tsakanin motoci). 
  35. Mafarkinmu a kullum gwamnati za ta bi mu gida-gida tana raba mana ƙwaryar zuma da nono. 
  36. Mai abin ba shi, shi ne mutum, mara abin ba shi, kuma banza ta fi shi. 51. Mai sata ya yi satarsa; in dai a ranar hawan sarki ne. 
  37. Matsalar wani ce abar tattaunawa, ba tamu matsalar ba. 53. Me ka taka ne? da ka dage sai ka taɓa haƙƙin waninka, ka zalunce shi. 54. Mu iyayen ‘ya’ya, irin wasan da ‘ya’yanmu suke yi ne ya fi dacewa da mu.( inji magidanci a ranar bikin hawan kara). 
  38. Mu muna da inda za mu tare; tun da namu ya samu. 
  39. Mun ƙi mu daina ɗaukar doka a hannunmu, tun da in mun danƙa shi a hannunku, sakin sa za kuke yi. 
  40. Na ga wajen zuwa, inji wanda aka yiwa kyauta ko sadaka. 58. Na sani ku tambayi matata, an ce da ɗan boko, me yake faruwa a gidanka?. 59. Na wani banza namu dukiya. 
  41. Ni kake cewa ci-ma-zaune; don na ƙi sana’a?
  42. Ƙanƙanta laifin da yake yi komai girmansa, da kambama laifin waninsa duk ƙanƙartarsa. 
  43. Karfin halin ba wa mai laifi kariya da ganin bakin mai hukunta shi. 63. Ƙarfin halin tattago aure, ana tsaka da ƙaƙa-ni-kayin samo abin da na gida za su ci. 
  44. Ƙarya da yaudara ce takenmu. (inji ɗan takara a ranar kamfen). 65. Ƙwarewa ce ta sa haka, ni ba na duba mara lafiya, sai yana halin gargara, wato (jawabin likita ga mara lafiyar da ya kai kansa asibiti). 66. Ƙwarewarmu da sanin makamar aiki ce ta sa ba ma ba wa mai neman aiki (offer), har sai ya sakar mana albashinsa na wata biyu. 67. Ran talakanmu ba komai ba ne; hawan sarki ya sa an kashe mutum. 68. Ribibin sana’ar da take ci har sai ta durƙushe. 
  45. Sabon yayi; yin ƙarya a tsakanin ‘ya’ya. 
  46. Samunsa shi ne samu, samun wani ba samu ba ne. 
  47. Sangarta ‘ya’ya da dasa musu aƙidar aiki da aike da wanki da kuma shara; aikin almajiri ne. 
  48. Shi kaɗai aka tsana. (inji uwar da aka yi wa ɗanta faɗan ya yi ba daidai ba). 
  49. Shiri da ni da kai ya ƙare, tun da ka soma irin sana’ata. 
  50. Sokon banza, lusarin kawai, inji matar wanda ba ya tsari da wanda maza suke dabdala a gidansa. 
  51. Tsine wa shugaba duk kirkinsa, idan bai biya musu buƙatar kansu ba. 76. Ya raina ƙadan; ga shi kuma babu hanyar samun mai yawa. 77. Ya yarda da babunsa, amma bai yarda da babun wanda ya saba ba shi ba. 78. Yabon wanda suke so da wanke shi tas, duk rashin kirkinsa. 79. Yara ke neman ilmi ba manya ba. 
  52. Yekuwa jama’a! Takenmu shi ne, rashin shiri da ‘yan uwa da maƙwabta.
  53. Yin gayya a kan abin tsiya; ya fi yin gayya a kan abin kirki. 82. Yin halin ko-in-kula da jaririyar ɓarna har sai ta girma ta ƙazanta a yi ta salallami da tafa-tafa. 
    Domin karanta cikekken littafin Danna nan 
labarin da ya wuceMutuwa Da Rabon Gadon Bahaushe
Labarin na GabaTabbancin Halaccin Ado da Kwalliya A Musulunci