Amana: Wani zance ne ko magana ne, kaya ko dukiya wanda wani mutum ya ɗauka ya ba wani mutum ko ya faɗa masa, saboda amincewar da ya yi da shi.
Cin Amana: Zambo cikin aminci, yaudara ko ha’intar wani mutum akan wani abu wanda wani mutum ya ɗauka ya ba shi ko ya faɗa masa, saboda yarda da ya yi da shi.
Saboda haka, addinin musulunci ya hana mu cin amanar juna ta kowane irin siga ko hanya, saboda addinin musulunci, addini ne na tausayawa juna, kulawa da juna, kare mutuncin juna haɗi da dukiyar juna da dai sauran su.
Haka kuma cin mutuncin juna, wulaƙanta juna, cin amanar juna ta kowane gwadabe, to ba halaye ba ne na addinin musulunci, ɗabi’a ce ta mutane marasa tunani da hankali.
Bugu da ƙari kuma, duk inda mutum musulmi yake, to ya san akwai waɗansu dokoki wanda Allah ya tsara, domin kula da rayuwar sa ta yau da kullum tare da tunani da hankali mai kyau haɗi da amfanin rayuwar sa.
Saboda haka yana da matuƙar mahimmanci akan kowane musulmi ya yi iya ƙoƙarin sa wajen bin dokokin addinin musulunci haɗi da al’adar sa, matuƙar addinin musulunci bai hana aikata haka ba.
Sannan kuma cin amana laifi ne mai girma haka kuma yana ɗaya daga cikin manya-manyan laifuffuka, wanda ya kamata musulmi ya yi la’akari da su sosai, saboda sun iya katange mutum daga shiga gidan aljannah .
Saboda ita amana malamai sun ce za ta zo ta tsaya akan siraɗi ranar lahira duk wanda ya ci amana, to za ta kama shi ta yi ƙasa da shi da dai sauran su .
Misali, idan wani mutum ya ba ka amanar wani abu, sai kai kuma ka ci amanar wannan abun, to ranar lahira wancan amanar da ya ci za ta zo ta tsaya akan siraɗi, idan ya zo zai wuce, sai ta kama shi ta faɗa da shi cikin wani rami mai zurfi sosai. Sai a ce da shi waccan ita ce amanar da ya ci.
Saboda haka sai ya bita ya kamo ta, idan kuma ya tafi zai ka mota, sai ya kamota ya kusa fito da ita waje, sai ta ƙwace ta sake komawa cikin rami wanda shi zurfin ramin tafiyar shekara ɗari biyar ne (500), haka kum mutum zai ta yi, ita kuma tana ƙwacewa.
Saboda haka mutum ya yi tunani sosai akan aikata haka, kada ranar lahira ya taho da aikin lada mai ɗimbin yawa, amma kuma ya ci amanar mutane, ka ga wannan amanar da ya ci, to sai ta hana shi shiga gidan aljanna.
Bugu da ƙari kuma riƙon amana yana ɗaya daga cikin abin da yake nuna ilimin mutum haɗi da tunanin sa da hankalin sa. Saboda Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) yace “mutane uku munafikai ne ko da ko sun ambata suna yin sallah, aikin hajji da ummara (su ne waɗanda) idan sun yi alƙawari da wani mutum sai sun saɓa, idan kuma mutum ya amince musu sai su yi ha’inci (cin Amana) da dai sauran su.
Saboda haka a nan ma ka ga cin amana yana kai mutum zuwa munafunci, sannan kuma shi munafiki idan bai tuba ba, ya mutu a wannan hali, to Allah (Subhanahu wata’ala) yace a cikin Alƙur’ani mai girma “su munafikai suna cikin ƙarƙashin wutar jahannama “. Suratul Ma’ida.
Saboda haka idan mutum yana aikin gina-ginai, sai wani mutum ya kira shi zai yi masa aikin ginin gida, to wajibi ne a kansa, idan an gama gina gidan, kada ya faɗawa ɓarayi ko kuma waɗansu ɓata garin mutane yanayin ginin gidan, saboda su samu damar shiga cikin gidan a cikin sauƙi, domin su samu damar yin sata.
Sannan kuma idan mutum yana sana’ar kafinta ko rafta ko kuma saitin setilait, to kada ya yi amfani da wata hanya mara kyau wajen rage katako ko kuma fallasawa waɗansu mutane yanayin tsarin gidan, domin samun damar yin aika-aika, to aikata haka, laifi ne mai girma.
Misali idan mai dukiya ko wani Alhaji ya kira wani mutum ya yi masa aiki a cikin gidan sa, to wajibi ne akan mai aikin ya kiyaye amanar da aka ba shi ma’ana kada ya ɗauko ɓata gari ko ɓarayi, sannan ya fayyace musu sirrin cikin gidan baki ɗaya, to aikata haka laifi ne mai girma, saboda dai-dai yake da wanda ya ci amana.
Sannan kuma Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) yana cewa “Dukkanin ku (mutane) masu kiwo ne, sannan kuma za a tambaye ku akan irin kiwon da aka ba ku “.
Saboda haka mutane ya kamata mu fahimci cewa dukkanin abubuwan da muke aikatawa a rayuwar mu, to mu sani fa amana ce a gare mu, saboda za a tambaye mu ranar lahira yadda muka gabatar da rayuwar mu.
Haka kuma idan wani mutum ya ba wani mutum wani ko ya faɗa masa wata magana bisa ga sharaɗi ba zai faɗawa kowane mutum ba, to idan ya faɗawa wani mutum wancan magana, bisa ga wannan sharaɗi, to shi ma ya ci amana, saboda wanda ya faɗa masa maganar bai aminta wani mutum ya san wancan maganar ba.
Saboda haka ita riƙon amana tana da mugun sha’ani kuma ga sanya takura a cikin al’amuran rayuwar wanda yake ɗauke da ita. Misali wani mutum ya ba ka ajiyar waɗansu kuɗi da niyyar zai karɓe su zuwa wani lokaci nan gaba, domin biyan waɗansu buƙatun sa, to kuma sai wata matsala ta samu wanda ya ba shi ajiyar kuɗin.
To idan ya ɗauki kuɗin ya yi amfani da su ba tare izinin wanda ya ba shi ajiyar kuɗin ba, to ya karya ƙa’idar musulunci, sai dai idan lokacin da zai karɓe kuɗin yace da shi, to fa idan wata matsala da same shi zai yi amfani da kuɗin, sannan kuma sai shi wancan mutumin ya amince akan haka, to babu komai a kansa.
Sannan kuma idan wani mutum ya ba wani mutum ajiyar dukiya ko kuma kadara, sai kuma a samu wata matsala wacce ta hallaka dukiyar ko kadarar ko kuma ya yi amfani da ita, to sai ya yi saurin sanar da wanda ya ba shi dukiyar, ma’ana halin da ake ciki, domin samun mafita akan wannan matsala .
Saboda haka dukkanin wanda akwai wani abu wanda yake shugabanta kamar su shugabanci, koyarwa ko aikin gwamnati, jinga ko ƙwadago, kafinta, wanki, direba, gyara da dai sauran su, to yana da matuƙar kyau ko amfani a gare su, su kula da su da idon basira sosai, saboda ranar lahira za a tambaye su akan yadda suka gudanar da su a cikin gidan duniya.
Bugu da ƙari kuma, dukkanin wanda ya ci amana, to amana shi ma za ta ci shi, wanda kuma ya kiyaye amana a nan gidan duniya, to ita ma za ta kare shi daga shiga wuta, muna roƙon Allah(Subhanahu wata’ala) da ya ba mu ikon sauke amanar da ke kan mu.
Danna nan don karanta Hanyoyin Tabbatar Da Adalci
Edita; RMK