Yadda Ake Wankan Tsarki Bayan An Gama Al’ada (2)

2
542

Shi yin wankan tsarki alama ce da take nuna cewa an gama al’ada, za ki fara sallah; wadda ya wajabta a kan ko wacce mace, idan ta gama ta yi shi.

Ruwa me tsafta, mara kala, farin ruwa a buta.

ÆŠaukan niyya, za ki fara da cewa (Bismillahi rahmanirrahim, na yi niyyar yin wanka, haila domin tsarkake kaina)

Sai ki wanke hannunki sau uku

Za ki wanke abin da ya yi daga cibiya zuwa gwuiwar ƙafa, saboda duk wata ƙazanta a tsakankanin nan take; bayan kin kammala, sai ki sake wanke hannun ki sau uku.

Za ki yi Bisimillah, sai ki yi yadda ake alwala, amma ba za ki wanke ƙafa ba.

Bayan kin kammala alwala, sai ki É—ebo ruwa, ki wanke saman kanki zuwa wuya; (wanki ba me sabulu ba, kuma ba shafawa za ki yi ba, wankewa mai kyau sau uku).

A wannan gaɓar, za ki raba jikinki gida biyu, wato dama da hagu.

Sai ki fara da wanke ɓarin dama, daga kafaɗa gaba da baya, harda hannaye zuwa ƙafafu.

Sai kizo ki wanke ɓarin hagu, daga kafaɗa gaba da baya, harda hannaye zuwa ƙafafu.

Bayan kin kammala, sai ki zo ki wanke Æ™afa (Ma’ana kin cika da alwala kenan).

Ƙarin Haske:

Alwalar da kika yi da farko, ba ki wanke Æ™afa ba, to bayan da kin gama wanka kika zo kika wanke Æ™afa daga Æ™arshe, za ki iya sallah da alwalar da kika yi, tunda tsaftatacciya ce, amma ba ta cikin Æ™a’ida, cewa sai daga baya za a dunga wanke Æ™afa.

Domin karanta cikakken bayani a kan Fara Jinin Haila Da Bayanin Siffofinsa danna nan.

2 SHARHI