Hausawa na cewa “Tun kafin a haifi uwar mai sabulu, balbela take da farinta”. Makaranta Alƙur’ani sun daɗe da mallakar kayan karatu da matallafa koyo (lnstructional/Teaching Materials).
Bugu da ƙari, makaranta a tsangaya na da fasahar sarrafa waɗannan matallafan yadda za su dace da buƙatarsu. Alal misali, yadda suke feƙe alƙalami ya zama kafe ko jirge, ƙaramin baƙi ko babba da dai sauransu.
Zai yi kyau, mu ɗauki waɗannan matallafan koyo a tsarin tsangaya domin mu yi musu nazari na musamman.
Allo: “Faskaren gwani”, ko da yake dai ba alaramma ne ke sassaƙa alluna ba, amma duk da haka ba don su ba, da an daina sassaƙa shi. Kalmar allo ararriyar kalmar Larabci ce “Allawh” aka mayar da ita Bahaushiya da cikakkiyar ma’anarta ta Larabci ba tare da wani canji ba. Allo “Turmin dakan tilawa!” Kamar yadda wasu ke masa kirari, shi ne matallafi na farko da makaranta ke runguma a dukkan matakan karatu. Da yawa manyan makaranta ko alarammomi ke rubuta allunansu, alhali sun ma rubuta Alƙur’ani sau barkatai.
Tun daga kan ƙananan almajirai masu ƙananan alluna, har zuwa kan samari masu rubuta sumuni ko rubu’i ko ma izu gaba ɗayansa, allo shi ne abokin karatu. A baya-bayan nan an gano cewa, haddar da aka samu ta hanyar allo tafi ƙwari a kan wadda aka yi da Alƙur’ani da takarda a hannu.
Amfani da allo bai taƙaitu ga tsangayu a Arewacin Najeriya ba, har ma da ƙasashen Larabawa irin su: Sudan da Mauritaniya da Libya, duk suna amfani da alluna. Domin kuwa tin zamanin Sayyadina Umar aka fara yi wa yara rubuta kan alluna a makaranta. Duba Sashe na Farko, Babi na Ɗaya kan koya da koyar da Alƙur’ani zamanin Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) da Sahabbai (Radiyallahu Anhuma).
Alƙalami:- Makaranta na sarrafa gamba ta hanyar feƙe ta gwargwadan yadda za ta ba su girman baƙin alƙalamin da suke so. Misali:
Kafe: Shi ne alƙalamin da aka datse kansa a kwance ba tare da karkacewa ba. Alƙalami kafe shi ne mafi yawan lokuta, aka fi amfani da shi wajen rubutu, kuma yana ba da baƙaƙe masu zubin dakali-dakali (blocks).
Jirge: Shi ne alƙalamin da aka datse kansa a Karkace. Ma’ana a jirge. Galibi gwaninta ke sanya iya rubutu da Jirge. Da makaranta sun ga rubutu za su iya gane cewa da wane irin alƙalami aka yi shi.
Tawada:- Makaranta kan haɗa tawada ne da zuge da ƙaro. Koda yake tawadar da ake yi ta hanyar wanke ta fi kyau musamman in an gamu da gwanin haɗa ta. Irin wannan tawada ita ake kira zege da barbarci.
Yambari:- Da yawa za a ga ado mai launi daban-daban cikin Alƙur’ani rubutun hannu. Wani rawaya wani kore da sauransu. Sirrin wannan shi ne amfanin da makaranta ke yi da wasu abubuwa su yi tawada mai launi. Yambari ɗaya ne daga cikin nau’o’in tawadun da makaranta ke amfani da shi; wajen yin rubutu mai ban sha’awa da ɗaukar ido.
Adadin ayoyi a farkon kowace sura akan rubuta shi da jan rubutu. Wasali kan zo daga ƙarshe, shi ma ana yin sa da jar tawada (Yambari) Nau’ukan Yambari a wajen Bare-bari; sun haɗa da Kimeyaram don yin wasali Zarni; rawaya don yin hamza, Maririma (kore) don laftra.
Korami:- Wani kwaroro ne da ake yi da kaba don sanya alƙaluma. Korami kan kare alƙaluma daga karyewa ko ɓata.
Takarda:- Makaranta kan yi amfani da Takarda wajen rubuta wata bara ko laƙani. Su kuwa masu rubuta Alƙur’ani kan yi amfani da takarda ta musamman mai tsirkiya da ake kira Holoma.
Bukari:- Wannan wani abin aiki ne da ya keɓanci marubuta Alƙur’ani. Bukari wani ɗan ƙarfe ne mai ƙafafu guda biyu, ƙafa ɗaya da bakin alƙalami ɗaya kuma mai tsini. Marubuta na yin amfani da Bukari wajen zana da’ira a matsayin kuri; ko alamar izu ka sabu’u ko kuma alamar sujjadda. Marubuci kan buɗe ƙafafun bukari gwargwadon yadda yake son girman da’ira a cikin rubutunsa.
Domin karanta cikakken bayani a kan Tsarin Karatu A Tsangaya danna nan.
Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’o’i Domin Neman Tsari Daga Azzalumai danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.