Hadisi Na Goma Sha Biyu A Kan Falalar Adalci Da Tausaya Wa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

0
470

An karɓo daga Ibn Abi Aufa (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Haƙiƙa Allah yana tare da alƙali matuƙar bai yi zalunci ba. Idan kuwa ya yi zalunci, sai Allah ya rabu da shi, sai shaiɗan ya naniƙe masa.
Tirmizi da Ibn Majah da Ibn Hibban da Hakim ne suka rawaito shi. Sai dai a ruwayar Hakim ya ce: “Idan ya yi zalunci sai Allah ya yi watsi da shi”.

ƘARIN BAYANI
Allah Ta’ala yana taimaka wa shugabanni da alƙalai masu adalci, yana kuma ba su kariya, yana rufa musu asiri, ya ɗaukaka su. matuƙar sun kama hanyar zalunci da rashin gaskiya, sai Allah ya yi watsi da su, ya bar su da dabararsu, su yi ta ɗimuwa da shirme, ga rashin ƙima a idon mutane, sannan in suka tafi a haka, a lahira su haɗu da matsananciyar azaba.

Domin karanta cikakken bayani a kan Hadisi Na Goma Sha Uku Kan Falalar Adalci Da Tausaya wa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu A kan Shugabanci) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikaken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceAmfanin Zaitun A Jikin Ɗan Adam.
Labarin na GabaHadisi Na Ɗaya A Kan Haramcin Goyon Bayan Azzaluman Shugabanni