Amfanin Zaitun A Jikin Ɗan Adam.

0
1278

Amfani zaitun a jikin ɗan Adam wanda ya kamata mu sani, Shi dai zaitun itaciya ce mai albarka da kuma ba da cikakkiyar lafiya a jikin ɗan Adam, kamar yadda muka sani cewa, zaitun abu ne mai daraja, kamar yadda muka samu bayaninsa a cikin ALKUR’ANI MAI GIRMA

haka kuma kamar yadda aka samu daga hadisan Manzon Allah (S.A.W)
An karɓo daga sayyadina Umar yana cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce ku yi abinci da man zaitun kuma ku shafa shi a jikinku, domin haƙiƙa shi yana daga a cikin bishiya mai albarka. tirmizi ne ya rawaito
Daga Cikin aikin da man zaitun yake a jiki
CIWON CIKI 
Duk mutumin da yake ciwon ciki, sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali, ya hada da garin habbatussauda ya cakuɗa, ya sha safe da yamma. Ya samu kamar sati ɗaya yana sha ko kina sha, insha Allah zai samu lafiya.
CIWON KAI
Duk mutumin da yake ciwon kai, to sai ya samu man zaitun, yana shafawa a kansa yana kuma shan cokali ɗaya da safe da rana da dare, insha Allah zai samu lafiya.
CIWON HAKORI

Duk mutumin da yake ciwon haƙori, sai ya samo ganyen zaitun da ‘ya’yan habbatussauda, ya saka su a cikin garwashi, ya buɗa bakinsa hayakin ya dinga shiga, insha Allah.

CIWON HANTA

Duk mutumin da ya kamu da wannan ciwo, sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali ɗaya da safe ɗaya da rana ɗaya da dare.

CIWON DADASHI 

Duk mutumin da yake ciwon dasashi, sai ya samu man zaitun ya dinga wanke bakinsa da shi.

CIWON SUKARI 

Duk wanda ya kamu da ciwon sikari to sai ya samu man zaitun da tsamiya yana haɗawa yana sha, kafin ya kwanta barci insha Allah

 CIWON ASMA 

Duk mutumin da wannan ciwon ya kama shi, to sai ya samu ganyen zaitun ko ‘ya’yansa ya dinga turarawa.

CIWON KODA

Duk mutumin da yake ciwon koda, to sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali uku a Rana. insha Allah.

CIWON BAYA

Duk mutumin da yake ciwon baya, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda a kwaɓa ya dinga shafawa a bayan insha Allah.

CIWON RAMA

Duk mutumin da ya ga yana ramewa, to ya dinga shan man zaitun kullum cokali uku insha Allah zai yi ƙiba.

 ZAZZAƁI MAI ZAFI 

Duk mutumin da ya kamu da zazzabi mai zafi, to sai ya dinga shan man zaitun cokali ɗaya sannan yana karanta ayatul kursiyyu sau 7 yana tofawa a ciki, yana shafe jikinsa da shi insha Allah.

KARFIN MAZAKUTA 

Duk mutumin da ya samu kansa a wannan hali, to ya samu garin habbatussauda ya dinga zubawa a cikin ruwan ɗanyan ƙwai, sannan a Soya shi da man zaitun ya dinga ci. Kullum insha Allah zai samu ƙarfin mazakuta sosai.

Kada ka gaji duk wani magani da ka gani ka gwada za ka dace insha Allah.

 KYAWUN FUSKA

Duk mutumin da yake so fuskar sa tayi kyau, ta yi fari, wanda ba zai cutar da shi ba, to, ya dinga shafa man zaitun da na habbatussauda, in zai kwanta barci, bayan ya tashi da safe ya wanke da sabulun salo, zai yi mamakin yadda fuskarsa za ta koma.

 ZUBEWAR GASHI. 

Duk matar da gashinta ba ya fitowa sosai, ko in ya fito sai ya zube, to sai ta samu ruwan zafi, ta wanke kanta da shi, sannan bayan ya ɗan bushe, sai ta zuba man zaitun a hannun ta, sai ta shafe kanta da shi gaba daya kullum.

ƘARANCIN JINI

Duk mutumin da yake da ƙarancin jini a jikinsa, to sai ya dinga shan man zaitun cokali biyu a rana.

BASIR

Duk mutumin da yake shan wahala in ya zo zai yi bayan gida, wani ma sai ya yi kuka saboda wahala, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda ya kwaɓa sai ya tura shi a cikin duburarsa.

CIWON MARA GA MATA

Duk matar da take haila tana fama da ciwon Mara, saboda fitar jini, in tana so ta samu sauƘin wannan ciwon, sai ta samu man zaitun tana haɗawa da ruwan tsamiya tana sha, insha Allah duk lokacin da za ta yi haila ba zai mata ciwo ba.

SANYIN ƘASHI

Duk wanda ƙashinsa ya yi sanyi, ba ya iya motsa shi, to sai ya samu man zaitun da man habbatussauda ya dinga sha, yana kuma shafawa a wajen insha Allah.

KYAWUN FATA DA LAUSHINTA

Duk mutumin da yake so fatarsa ta yi laushi da kyau, to sai ya sami man ya dinga shafe jikinsa da shi, bayan ya yi wanka da ruwan ɗumi, zai yi mamaki yadda fatarsa za ta koma insha Allah

 ƘURAJEN ƘARZUWA

Duk mutumin da yake da ƙarzuwa ko wasu ƙuraje ko sabon miki, to sai ya samu ganyen zaitun ya kirɓa shi ya hada da garin habbatussauda yana shafawa a wajen har ya warke.

 CIWON KUNNE

Duk mutumin da yake ciwon kunne, to sai ya bari in zai kwanta barci, sai a dinga haɗa man zaitun da na habbatussauda yana ɗigawa a kunnensa insha Allah.

 CUTAR KYASBI

Duk mutumin da yake da KYASBI a jikinsa, to sai ya samu ganyen zaitun busasshe. Ya daka shi, ya yi laushi sai ya haɗa shi da man zaitun ya cakuɗa, ya dinga shafawa a wajen lokacin da zai kwanta barci, sai ya wanke.

SHAFAR ALJANU

Duk mutumin da yake so ya rabu da aljanu, to ya dinga amfani da man zaitun, saboda aljanu ba sa son shi, shida habbatussauda. Don haka yana da kyau, mutum ya lazimci amfani da su a kowane hali, in da hali ma ya mai da su mansa na shafawa, amma yana da kyau kafin a Fara shafawa a karanta ayoyin rukya sai a nemi addu’a.

CIWON KARKARE

Duk mutumin da ciwon karkare ya same shi, to sai ya samu man zaitun, sannan a samu lalle a kwaɓa, sai a zuba man zaitun ɗin a cikin lalle a gauraya, sannan a karanta (AYATUL KURSIYYU) sau 7 a tofa a ciki, sannan sai a tofa a jikin wannan karkare insha Allah.

CIWAN NONO

Duk matar da take fama da ciwan nono, saboda rashin zubar, to ana haɗa man zaitun da garinsa, a barbaɗa  a kan nonon saboda samun damar zuba, don ƙofofin su bude.

MOTSA SHA’AWA 

Man zaitun yana motsa sha’awa, in an shafa shi lokacin da ake yin wasa.

CIWON SAIFA

Duk mutumin da yake ciwon saifa, sai ya haɗa man zaitun da garin habbatussauda da kuma zuma farar saƙa ya sha, insha Allah.

TSUTSAR CIKI

Duk mutumin da yake da tsutsar ciki, to sai a samu man zaitun da garin habbatussauda da zuma ya kwaɓa su ya sha, wannan tsutsar za ta mutu.

CIWAN HANJI (ULCER)

Duk mutumin da yake da gyambon ciki, to sai ya samu garin habbatussauda kamar cokali ɗaya sannan ya samu garin (kumasari)da ganyan zaitun mai laushi ya jiƙa su ya dinga sha har sai ya warke.

FITSARIN KWANCE

Duk yaron da yake fitsarin kwance, to sai a samu garin zaitun Da na habbatussauda a zuba a nono a dinga ba shi yana sha, zai daina. Insha Allah

MUTUWAR JIKI(KASALA)

Duk mutumin da jikinsa yake yawan mutuwa, to sai ya dauwama yana shan zuma da garin habbatussauda zai ji ƙarfin jikinsa.

YAWAN ZAZZAƁI

Duk mutumin da yake yawan yin zazzaɓi. To sai ya samu garin habbatussauda kamar cikin ludayi ya kwaɓa da ruwan zafi. da kuma zuma marar haɗi, ya dinga sha. insha Allah

CiWON GAƁOƁI

Duk mutumin da gaɓoɓinsa suke ciwo, to sai ya samu garin habbatussauda da zuma ya dinga sha, sannan kuma ya zuba garin habbatussauda a cikin man zaitun ya dinga shafawa a gaɓoɓi.

KWARKWATA

Duk matar da take fama da kwarkwata, kuma har take son rabuwa da ita. to ta samu man zaitun da garin habbatussauda ta kwaɓa, sannan sai ta bari sai rana ta take, sai ta zuba wannan man a kan nata, ta bar shi ya yi kamar minti (20), sannan sai ta wanke insha Allah za tai ban kwana da kwarkwata.

CIWAN TARI

Duk mutumin da ya kamu da kowane irin tari, to sai ya samu garin habbatussauda da man zaitun da  citta da tsamiya da zuma. sai ya haɗa su guri ɗaya, ya cakuɗa, ya dinga ci insha Allah.

MAJINAR ƘIRJI

Duk mutumin da yake yawan majinar ƙirji to sai ya samu man zaitun. da garin habbatussauda ya haɗa ya dinga ci kullum sau biyu (2) safe da yamma.

TARIN FUKA

Duk Wanda yake tarin fuka to sai ya dinga shan man zaitun cokali ɗaya kullum.

DOMIN KARIN BAYANI A KAN MAGUNGUNA  DA AMFANIN SU DANNA KOREN RUBUTUN NAN

labarin da ya wuceYadda Ɗabi’un Maza Suke
Labarin na GabaHadisi Na Goma Sha Biyu A Kan Falalar Adalci Da Tausaya Wa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu
BHM Ninja
Sunana Buhari Ibrahim Aliyu [Googler] dalibin computer, digital marketer, technical crew a wikihausa dalibi mai kokarin yada ilimi na na'aura mai kwakwalwa tare da tabbatar cigaban kasuwancin zamani.