Raunin Da Namiji Da Abinda Hakan Ke Nufi

0
68

Raunin halittar da namiji wato Erektayil dayisfankshin (ED): Al’amari ne da halittar baligin namiji kan gaza mikewa ko kasa cigaba da kasancewa a tsaye bayan tashinta har ya samu ya biya bukatar sa, zai zamo da ta tashi zata kwanta, wani sai yai ta girgizata sannan tai tsauri ta mike kafin Jim kadan ta ko ma.

Topic irin wannan ba abune da kwararrun masa kan tsaya su tattaunasa ba cikin al’umma, Toh amma dole a matsayin mu na physicians ace muna samun lokaci mu haskawa al’umma irin wadannan abubuwa da kuma abinda hakan ke nufi.

Idan aka ce “Marker for Overall Health” Ana so aima nuni da cewa wannan abin fa kusan shine komi game da lafiyarka, duk me son ya tantance lafiyarka toh ya kalli wannan abin, Kamar yadda ake cewa in kana son sanin halin mutum to ka kalli abokansa. 

Zuciya tsoka ce jikin mutum da inta sami matsala dukkan jiki ya gama samun matsala…  Toh raunin gaba ko mazakuta ga mutum babbar alama ce dake nuna zuciyarsa bata da lafiya a kaso fiye da 50% na masu larurar.

Domin karanta Damar Samun Da Na Miji Ko Diya Mace Ga Ma’aurata Danna nan

Kafin gaban da namiji ya mike yakai ga ya sami lafiyayyen Erection dole sai abubuwa uku (3) sun hadu:

  1. Lafiyayyar tsokar Gaba [healthy muscle].
  2. Lafiyayyar jijiyar kai sako da sauti wato [health nerves].
  3. Lafiyayyar jijiyar jini dake kawo jini azzakari daga zuciya  wato [ healthy artery] Kamar yadda akan ga sunyi rudu-rudu sun cika da jini idan ansami erection. 

To a cikin abubuwa ukun can wato; Nerves, artery ko muscles…. duk wanda  ya sami matsala tohfa shine mutum ke fuskantar raunin mazakuta [Erectile Dysfunction].

Shiyasa daga cikin nazarin da mukan yi matsayin mu na likitoci idan mutum yazo mana da matsalar shine fara yin tambayoyi game da larurorin da kan iya lalata wadancan ababe ukun wato larurori irin su: Ciwon Sugar [Diabetes] wacce kan iya lalata jijiyoyin kai sako wata nerves, ko Hawan jini [Hypertension] wanda ke taba jijiyar jini ta artery, ko kuma Matsalar tangardar sinadaran sha’awa da jima’i da kan shafi tsokokin azzakari wato karancin sinadarin testostiron [Low testosterone].

Wannan tasa nutsuwa tare da sakin jiki a baiwa likita amsoshin tambayoyin da zai daki-daki bisa gaskiya ba tare nuqu-nuqu ko kunya ba nada matukar muhimmanci wajen fahimtar magani ko mafitar data dace da mutum.

Domin karanta Abubuwan Da Sukan Iya Taimakawa Wajen Raguwar Warin Baki Danna nan 

Kafin Azzakari ya mike yai aikin biyan bukatar da akeso… Dole tsokokin gaban sai sunyi laushi, sun saki, sun zamo relax, Sannan kwakwalwa itama ta zamo relaxed tare da tsokokin mara, Saboda idan tsokokin sukai relaxed hakan ne zaisa su iya cika da jini dam, wanda hakan zai sa tai kauri, ta bude ta tsaya cak. 

Shyasa Sam babu muhallin damuwa ko stress yayin da ake tunkarar jima’i, ana so ya zamto duk hayaniyar duniya an ajeta, sannan babu sabani ko Jin haushin juna ga Macen da Namijin. Saboda damuwa ko stress na haddasa tsukewar tsokokin gaban wanda hakan bazai ba jini damar kwaranyo ba wanda dole Gaban ba tsaya ba duk yadda kaso ya tsaya dole yaita kwanciya Kamar lawashi.

Shiyasa maganin wannan matsalar ya fara ne da fara gano tushen matsalar, idan akwai ciwon sugar dole ita za’a duqufa aga anyo control dinta da kyau tare da magance matsalolin da ta fara haifarwa, idan kuma mutum baisan yana da ita ba,toh za ai masa gwajin, idan babu sannan a tafi ga larura ta Gaba wato binkicen Hawan jini, ko yawan kitse ajika wato High Cholesterol, ko kuma binkicen sinadaran halitta ko sunyi kasa, da gwajin lafiyar zuciya. 

Daga nan sai gyara tunanin mutum, idan yana cikin hayaniyar duniya, da damuwoyi ai addressing din su, domin koda komi lafiya inde akwai stress ko depression wannan ma na kashe sha’awa murus a Maza ko Mata. 

Sai cin fruits irinsu karas, kankana, cucumber, da cin proteins irinsu gyada, naman kaji, tare da kiyaye cin jan nama. Sai kuma tabbatar da ana samun wadataccen bacci. Bacci nada matukar muhimmanci ga lafiya. 

Sai a karshe motsa jiki, KEGEL EXERCISE da nai ta bayani abaya, lallai Namijin dake son lafiya ya rungumi yinsa. 

A wannan matakin ne zaku fahimci wauta da gangancin yawan shaye-shayen maganin karfi da Mazajen mu keyi, domin Kaine kusan kullum sai kasha abu, inma baka sha ba baka iya komi… Shin hakan bai isa ka gane cewa abin nan lallai akwai wata matsala akasa ba?

Sannan yana dakyau ku karanta wannan Kawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya

Domin ai ba dede bane ace kullum sai kasha magani, kuma galibin wannan maganin shifa Erection kurum yake baka ba wai sha’awarka bace ke qaruwa, shiyasa ko babu sha’awa da kwanciyar hankali kana iya samun erection bayan shan wannan tarkacen, wannan kuma ke nuna shan maganin baida alaqa da maganin matsalar ka. 

A karshe irin wannan shaye shayen ke dada lalata zuciya, ko koda wanda a karshe zama ka daina samun erection din ne, kaga murus kenan. 

Don haka duk me irin wannan larura Ina me basa shawara yaje yaga manyan likitoci, larurarsa ta asibiti ce, ka dena asarar kudi wajen masu magungunan gargajiya ko so called islamic chemist, ko a rika fama rataya maka aljani ko ace asiri akai ma, ko ace masturbation. Kai de kaje ga Medical doctors. 

Domin karanta cikekken bayani akan Taminal Lusiditi (The Surge) Danna nan

labarin da ya wuceTaminal Lusiditi (The Surge)
Labarin na GabaPhysiology da Hausa Kashi na Biyu: Body Fluids (Ruwan Jiki) Ruwan dake jikin ɗan Adam