Taminal Lusiditi (The Surge)

0
28

Wannan wani yanayi ne me kamar  almara dakan faru dab da mutuwa. da akanga mara lafiyar dake fama da matsananciyar jinya doguwa ko gajeruwa…. wacce dalilin ciwon ƙila ko tashi baya iya yi, ko kuwa baya iya cin abinci, ko mutum ya kasance sai ana juyasa tare da ɗaga ana canza masa kwanciya…. Ko kuwa ma baisan waye kansa ba sam, magana ma in yana yi ba’a gane abinda yake cewa saboda zafin ciwo.

To amma kwatsam sai aga canji daga yanayin wannan mara lafiya, aga sauƙi ya samu na ban mamaki, akan iya ganin ya tashi da kansa ya zauna ko ya taka batare an taru andagasa ba, ko aga yaci abinci da kansa sosai, ko ya tattaka da kafafunsa, kuma yana iya gane kowa, ana magana yana dariya ma. Kaga ƴan uwa nata murna sauƙi ya samu, ariqa wanne ai yau har abinci yaci da kansa.

Domin karanta Damar Samun Da Na Miji Ko Diya Mace Ga Ma’aurata Danna nan

Allah sarki! amma bayan wasu awoyi, yini guda, kwana uku ko sati ɗaya zuwa huɗu kwatsam saide aji anfasa kukan wane ya rasu. A riqa mamaki bayan ga alamun sauƙi anganki saɓanin da ƙila kowa na kawo mutuwa zai to amma ganin yadda wannan sauƙin ya samu yasa yanzu mutuwarsa ta zama abin mamaki. Shine ma zaka ji Hausawa na cewa ashe wane sauƙin bana tashi bane, Allah sarki.

Ya ku ɗaliban ilimi…. wannan yanayin na ganin alamun sauki ga majinyacin da ada ba’a tunanin zai tashi haka… Amma kuma kwatsam aga ya kwanta ya mutu shi muke kira terminal lucidity ko end of life rallying ko the surge. Duk mara lafiyar da akaga irin wannan saukin ba zato ba tsammani alama ce ta mutuwarsa ta kusanto 

Domin karanta Abubuwan Da Sukan Iya Taimakawa Wajen Raguwar Warin Baki Danna nan 

Ga manyan likitoci munsan hakan alamun mutuwa ne, shiyasa bama ruɗuwa koda iyalan mara lafiya sun fara zancen neman sallama daga asibiti, haka koda agida mara lafiya yake abin ke kasancewa. Don haka a duk sanda kuka ga irin wannan saukin inda hali kui masa ku nemi wasicci, ku tambaye sa abinda zaku so sani, yana dab da gargara.

Hakazalik akwai yanayin da akanga Mara lafiya na nuni da hannu, ko aga yana ɗaga hannu sama daga kwance kamar me kokarin kamo wani abin ko karɓa ko ɗaukar wani abu. Wanda shine a masu jinya zaka ga mutum na tasowa yana tambayar me kake so? Amma sai aga mara lafiyar ya kau da kai. A riqa wani abin yake son faɗa amma ya kasa… Wannan shi muke kira “REACH OUT” da wuya mutum ya qara awa 72 a raye. Don haka wannan na daga alamun mutuwa shima. Sai ai kokarin fara bawa mutum kalmar shahada.

Shyasa wasu lokutan wani kan ga ya biya likitoci kudin aiki amma suna jan ƙafa wajen yin aikin, karshe ace mutum ya mutu basui aikin ba. Wani abin ba fitowa za ai ace muku ga abinda aka gani ba, sai ya zama rigima. 

Allah ka jikan mu, kai mana kyakkyawan ƙarshe. A hankali zan cigaba da nusar damu alamomin gane tunkarowar mutuwa musamman don masu jinyar marasa lfy daga ilimiin da Allah ya bamu.

Sannan yana dakyau ku karanta wannan Kawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya

labarin da ya wucePeptic Ulcer Diseases
Labarin na GabaRaunin Da Namiji Da Abinda Hakan Ke Nufi