Peptic Ulcer Diseases

0
28

Ciwon olsa  ta zama daya daga cikin manyan cutuka da suke damun al’ummah a kasar mu ta Najeriya.

Peptic Ulcer Disease : (Gyembon Ciki) general name na na ulcern ciki gabaki daya.

Ita Peptic ulcer ( gyembon ciki ko ciwon ulcer ) ya kasu kashi uku kamar :

1- Gastric Ulcer (Gyenbo wadda take kama Fatar ciki ciki)

2- Duedenal Ulcer ( Gyenbo wanda take kama hanji)

3- Esophagus Ulcer  (Gyenbon maqogwaro)

Domin karanta Abubuwan Da Sukan Iya Taimakawa Wajen Raguwar Warin Baki Danna nan 

Ciwon Olsa tana zuwa da alamomi diyawa gasu kamar haka: 

1- Konawar zuciya

2- Ciwon Cikin

3- Rashin cin abinci

4- Tashin Zuciya 

5- Amai

6- Ciwo har a gadon baya

7- Kashi da jini  ko bakkin kashi

8- kumburin ciki

9- ciwon cikin

10- Daukewar numfashi.

Me yake kawo ciwon Olsa ?

* Kwayar cutar bakteriya mai suna H- pylori shi yake kawo ciwon Olsa , Haka kuma yawan shan maganin dauke  ciwo kamar su  Aspirin, Shan taba (sigari) da kuma shan Giya suna taimaka sosai wajen kawo ciwon Olsa.

Sannan yana dakyau ku karanta wannan Kawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya

Ta wacce hanya ake daukan Kwayar cutar olsa ?

– Mutum yakan iya daukan wannan koyar cutar ta hanyar musyar yawu (saliva) ko lokocin kiss.

– Mutum yakan iya daukan wannan kwayar bakteriyan  ta hanyar ruwan sha da kuma abinci 

Idan ruwan sha ko abinci ya gurbanta da bayan gida ko fitsarin mai ciwon, wanda hakan yana faruwa ne ta hanyoyi da yawa.

Mesa ita ciwon olsa ba’a warkewa da wuri ?

Ba Ba’a warkewa bane , ana warkewa daga cutar Olsa ko wacce iri amma abinda yake faruwa shine :

1- Rashin shan magani yadda yakamata , yau anwayi gari shan magani barkatai yazama ruwa dare a najeriya , mafi yawa kwayoyin cutar ansaba musu da wannan maganin har yazama suna jurewa .

2- Za kaga mutum ana bashi maganin wata daya ko sati biyu a ranan da yafara shan maganin idan yaji sauki shikenan ya rabu da maganin dai lokocin da alamomin cutar yasake zuwa zaici gaba da shan magani. 

3- Misali ace kwayar cutar ana samunshi daga gurbaceccen ruwa , To ana shan magani kuma ana cigaba da shanceccen ruwan kaga babu maganar warkewa .

4- Rashin bin ka’idodin likita ya gaba gaba wajen hana warkewan wannan ciwo na Olsa.

5- Shan magunguna barkatai ba tareda Izinin likita ba musamman magungunan olsa da sunan zai warkar maka da olsa, da kuma amfani da magunguna na gargajiya wanda ba’asan kanta ba.

Shawara ga masu ciwon olsa:

1- A kauracewa wadannan Abinci :

– Abinci mai yaji

– Abinci mai daci

– Abinci Mai sami

– Abinci masu Gas

– Abinci masu dauke da Acid kakar tumaturi.

2- A daina amfani da hayaki ko wacce iri ko tabar sigari, wiwi ko shisha sabida suna daga cikin Abubuwan da suke haddasa olsa Kuma suna sananta olsa.

3-  Adaina amfani magungunan dauke ciwo irinsu Aspirin, Ibuprofen, cataflam, Naproxen, Feldene, da sauransu.

4- A rage shan giya domin yawan shan giya yana  daga  cikin abubuwan  da suke kawo olsa Kuma suke sananta Olsa.

5- A tabbatar an tace sannan a tafasa ruwan da ake da kwawato akai kafin amfani.

6- A yawaita amfani da kayan lambu musamman cavage (kabeji) yana taimaka wajen dakile ciwon olsa.

7- Sai Kuma zuwa ga likita domin Tabbatar da cutar da Kuma bada magani.

Domin karanta Damar Samun Da Na Miji Ko Diya Mace Ga Ma’aurata Danna nan

labarin da ya wuceGangliyon Sist [Ƙarin Mahaɗar Ƙashi]
Labarin na GabaTaminal Lusiditi (The Surge)