Kawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya

0
15

Wani lokacin indan a kace za a sanyawa mutum robar hanci a rinka bashi abinci tanan yan uwansa wasu basa yadda yau akan hakan xa muyi bayani 

Robar hanci, wato (Nasogastric tube) a turance, wani siririn tiyo ne na roba wanda ake zira shi ta ƙofar hanci har zuwa cikin tunbi. Manufar ita ce domin a samu kaiwa ga cikin tunbi.

Sanya robar hanci na iya zama cikin muhimman ayyukan taimakon gaggawa yayin da aka garzaya da mara lafiya zuwa asibiti. 

Haka nan, sanya robar hanci na da muhimmancin gaske ga mara lafiya 

Kamar haka:
  • Ana amfani da robar hanci domin ciyar da abinci ko shayar da abinsha ga mara lafiya, musamman a halin da mara lafiya ba zai iya cin abinci ta baki ba. Ko dai saboda mara lafiya ya ƙi ci ko sha, miki/rauni a baki, ko kuma bayan tiyata a baki ko maƙogaro.
  • Ana amfani da robar hanci domin bai wa mara lafiya magunguna kai tsaye zuwa cikin tunbi, musamman ga mara lafiya da ke fuskantar wahalar haɗiya ko kuma ba zai iya karɓar magani ta baki ba.
  • Ana amfani da robar hanci ga mara lafiyan da ya fita daga cikin hayyacinsa. Ko dai saboda wata larura ko kuma saboda da allurar kashe-ciwo da ake yi kafin tiyata.
  • Haka nan, robar hanci na amfani domin kiyaye wa mara lafiya shaƙar abinci, abinsha, majina ko yawu zuwa cikin huhu, musamman ga mara lafiyan da ke gaza haɗiya yadda ya kamata kamar masu shanyewar ɓarin jiki, bugu a kai, da dai sauransu. 
  • Domin shaƙar abinci/abinsha, majina ko yawu zuwa cikin huhu na da haɗarin gaske. Sau da yawa, ba larurar da ta kwantar da mara lafiya ce ke sababin mutuwarsa ba face illolin shaƙar waɗannan abubuwa zuwa cikin huhu. Domin hakan na nufin wahalar shaƙar oksijin.
  • Har wa yau, ana amfani da robar hanci domin zuƙe gurbataccen abinci/abinsha, iska, ɗiwa ko jini daga cikin tunbi. 
  • Bugu da ƙari, robar hanci na amfani wajen buɗe hanya bayan toshewar hanyar maƙoshi daga baki zuwa cikin tunbi.
  • Bayan nan, ana amfani da robar hanci kafin ko bayan tiyata a ciki, da dai sauran dalilai.

Domin karanta Bayani Akan Tsarin Abinci Ga Masu Ciwon Suga (Diabetes Mellitus) Danna nan

Sai dai, sanya robar hanci ga mara lafiya na daga cikin abubuwan da ke sanya tsoro da fargaba a zukatan ‘yan uwa da abokan mara lafiya. Saboda yadda ake zaton cewa ba a sanya robar hanci ga mara lafiya har sai ya kai gargara.

Sau da yawa ma, wasu na canfi cewa matuƙar aka sanya wa mara lafiya robar hanci to ba ya dawowa gida, wato mutuwa zai yi.

Amma kwata-kwata abin ba haka yake ba. Domin ana sanya robar hanci ne kaɗai idan buƙatar hakan ta zama dole. Kuma sanya ta ga mara lafiya gagarumin taimako ne da kuma ceton rai.

Haka nan, ana sanya robar ne na wani ɗan lokaci kawai gwargwadon buƙata. Sannan a cire ta bayan buƙatar ta gushe.

Daga ƙarshe dai, babu wani dalilin tsoro ko fargaba idan aka sanya wa mara lafiya robar hanci, domin yin hakan shi ne abin da zai fi amfanar lafiyarsa a lokacin.

Domin karanta Tsarin Iyali { Family Planning) Rubutu Na (2) (Intrauterine Device Danna nan

labarin da ya wuceTsarin Iyali { Family Planning) Rubutu Na (2) (Intrauterine Device
Labarin na GabaHawan Jini (Hypertension)