Hawan Jini (Hypertension)

0
25
Menene Hawan Jini?: hawan jini ciwo ne da yake samuwa sakamakon karuwa ko hawa da jinin mutum keyi fiye da kima (persistent rise in blood pressure).
Yayin Kamuwa Da Cutar

Jijiya, wato makwarara kokuma hanyoyin da jini ke bi (blood vessels),sukan zama kanan kokuma su toshe saboda wasu dalilai da suma wasu cututtuka ke kawo su to da zarar jijiyoyin jinin sun matse sai yanayin ya haifar da haurawar jini,wato (increase in blood pressure),wannan haurawa na jini din yakan karawa zuciya dawainiya.

Sabida da wannan dawainiya da zuciya ke yi sai jijiyoyin zuciyar su rika samun rauni akai-akai har a karshe sai a samu matsalar ciwon zuciya, (wato cardiac falure )

Alamominsa

Alamomin hawan jini sun dan ganta ne daga mutum to amma akwai wasu manyan alamomi da ake samunsu ga kowa 

  • Matsanancin ciwon kai
  • Ciwon kirji
  • Matsalar gani
  • Ciwon jiki
  • Numfashi dakyar
  • Faduwar gaba 
Abubuwan Dake Haifar Da Ciwon

Yanayin rayuwar mutane da dabi’un su na yau da kullum suna taka rawar gani sosai wajen haifar ko kawo masu wannan ciwo na hawan jini kamar su.

  • Shan taba 
  • Shan giya
  • Yawan cin abu mai gishiri

masu wannan dabi’a suna cikin hadarin kamauwa da cutar hawan jini.

Hanyar Kariya
  • Rabuwa da shan giya: Shan giya na da matukar hadari ga lafiyar mai ta’ammuli da ita kwarai ainun ciki harda kara ruruta wutan ciwon hawan jini.
  • Motsa jiki akai-akai (regula excersise): Motsa jiki na da muhimmanci ga rayuwa sosai haka nan ma yake da amfani wajen yakar ciwon hawan jini.
  • Cin abinci mara gishiri: Wannan irin abinci na taimakawa wajen daidaita electrolyte a jiki sannan zai yi controlling blood pressure.
  • Yawan cin ya-yan itace da ganyeyyeki (fruits and veggies): Yawan cin ya-yan itace da ganyeyyeki wato vegitables na rage cholesterol wadda ke taimakawa wajen rage hauhawan jini.
 Jan Hankali

Mai hawan jini ya kamata ya kiyaye umarnin likita na shan magani, kiyaye amfani da gishiri kadan, hakura da amfani da kanwa, sannan da zuwa asibiti domin ganin likita ba sai lokacin da matsala da faru ba.

Rashin kula da ka’idar da likita ya shimfida kan iya haddasa matsalar zuciya a karshe.

Domin karanta bayani akan Kawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya Shiga nan

labarin da ya wuceKawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya
Labarin na GabaCiwon Zuciya Tsantsa (Heart Failure)