Hukuncin Kallon Talabijin Da Fina-Finai

0
26

Idan aka kau da ido daga irin asarar da mutum ke yi a sababin kallon talabijin da fina-finai, sai mu ga shin mene ne hukuncin kallonta ne a musulunci? 

Hukuncin kallon talabijin da fina-finai na komawa ga hukuncin abin da ake gani a cikin akwatin talabijin. Idan dai kallon matar da ba muharrama ba haramun ne a fili ko kan hanya, to babu kuwa yadda za a ƙura mata ido cikin talabijin kuma ya zama halal. 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

Ubangiji Maɗaukaki na cewa: “Ka faɗa wa muminai maza su runtse ganinsu kuma su kiyaye al’aurarsu, kuma ka faɗa wa muminai mata su runtse ganinsu kuma su kiyaye al’aurarsu”. Suratul Nur 

Nisa’i ya ruwaito Hadisi cewa dangogin mutane uku ba za su shiga aljanna ba (Thabarani ya ce ba za su taɓa shiga Aljanna ba”); 

  • Mai saɓa wa iyaye. 
  • Dayyus. 
  • Mai kwaikwayon mata. 

Dayyus shi ne mutumin da bai damu da kamewa ko rashin matarsa ko `ƴarsa ko `ƴar uwarsa ko mahaifiyarsa ba. Dayyus ba ya damuwa in an ga maharramarsa tana yawo babu hijabi ko kuma tana cuɗanya da waɗanda bai halatta ta cuɗanya da su a shar’ance ba. 

Ko kuma tana kallon mazaje daban-daban cikin fina-finai. Dayyus ba ya damuwa muharramarsa ta ƙosar da sha’awar masu fasadi da a adonta da muryarta ballatana ma ya yi kishin `ƴa`ƴan wasu ko matansu.

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna Nan 

labarin da ya wuceSahihin Sirrin Iza Ja’a
Labarin na GabaHukuncin Kiɗa A Musulunci