Bayayanar Nau’in Abinci Mai Gina Jiki A Cikin Fitsare (Proteinuria)

0
49

Protein nau’in abinci ne da ya kunshi su wake,nama,kwai,madara,kifi,gyada dadai sauransu.

Presence of protein in urine a lamace dake nuni da kodar mutum na fuskantar kasawa wajen tacewa da fitar da gurbatattun products ajika, hakan na nuni da akwai matsalar kidney damage Ko kuma ta Urinary Tract infection wato (hanyoyin mafitsara).

Ciwon suga da kuma hawan jini kan taka rawa wajan dagula ayyukan koda ta yadda bata iya saisaita protein din. 

Sannan idan akasami irin wannan yanayin ajikin mace mai juna biyu (Pregnancy) toh alamace dake nuna zata iya fiskantar matsalar jijjiga yayin haihuwa wato (pre eclampsia) saboda cikin datake dauke dashi kansa matsi yadda tace fitsarin kan yi ma kodar wahala musamman yayin da ya fara girma shi yasa zakuga masu ciki na da yawan fitsari akai akai saboda jaririn ya fara danne mafitsararta ta yadda ya taru dole sai ta fitar bazai riku ba fitsarin, ballantana kuma Allah ya kare ace ga protein ga kuma hawan jini kai tsaye ya zamo eclampsia 

Domin karanta bayani akan Family Planning Injection (Noristerat) (Norist) Danna nan

Amma dai anfi alakanta hakan da kidney damage domin rashin aikinta yadda ya kamata kesa ta kasa tace protein din kodai ga mai ciwon suga, hawan jini, ko kuma wanda jikinsu ke over  production na proteins contents.

Sannan Yawan Protein Din Ajika Ka Iya Haddasa:
  • Kidney damage. 
  • Karancin ruwa ajika.
  • Tara nauyi.
  • Rai a hannun Allah yake,  amma hakan na jawo saurin mutuwa abisa binkice
  • A rika jin zafin ciki.
  • Karancin sinadaran enzymes da jiki ke buƙata wanda hakan kansa mutum da kansa yake jin jikinsa ba haka ya kamata ya kasan ce ba. 
Shawara
  • A takaita cin abinci nau’in protein, atsara yadda ya kamata ake cin abinci kamar yadda yake da rukunai 6.
  • A kuma kecin fruits da vegetables wadannan abubuwa basai masu yawa ba Yar kankanarka ta Naira 20 da lemon 6awon goma a kullum ya isa.
  • Sannan arika motsa jiki, akuma guji kwanciya da zarar an kammala cin abinci.
  • Kada ka maida cikinka bola ya zamto komi ka samu danna masa kurum kake. Yawan cin naman nan da kifi kullum kullum matsala ne bayin Allah wallahi ba gayu bane, hasali ma daurema cin naman gindi shi kadai ma ka iya ɓatama koda. 
  • Shi rika motsa jiki koda kuwa akwai juna biyu ga mata kada ai wasa wajen motsa jiki ayi daidai misali.

Wannan shine! Allah subahanahuwata’ala yai mana albarka a rayuwar mu ya karemu daga cuttuka masu wahala Amin.

Domin karanta yadda ake Tsayar Da Zubar Jini (Agajin Gaggawa) Danna nan 

labarin da ya wuceTsayar Da Zubar Jini (Agajin Gaggawa)
Labarin na GabaNausea (Tashin Zuciya)