Noristerat (Norist) allurar tazarar haihuwa ce wacce take ɗauke da sinadarin progesterone kaɗai kuma tana zuwa da nauyin milligrams dari biyu (200mg).
Wannan alurar ana yin ta kowacce bayan sati takwas (8weeks) domin tazarar haihuwa (ba hana haihuwa ba) musamman ga waɗanda ke da ƙananan shekaru masu buƙatar allurar tazarar haihuwa kamar me haihuwa 2 ko 3 wadda a cikin magungunan tazarar haihuwa norist tana da sauƙin sha’ani kuma ba ta ba da matsala idan aka bi dakokinta. Da zarar ranar da aka daina amfani da allurar norist ana kyautata zato mace za ta iya samun juna biyu.
Wannan allurar idan aka fara amfani da ita tana zuwa da wasu canji ga wasu matan ba duka ba, kamar yadda kowane magani tana da nata side effects din.
Domin karanta bayani akan Ciwon Suga.(Diabetes) Danna nan
Daga Cikin Canjin Da Ake Samu Akwai:
- Rikicewar al’ada
- Rashin ganin al’ada
- Ganin gudaji-gudaji lokocin al’ada.
- Ciwon Kai
- Tashin zuciya
- Ƙara jiki
- Hajijiya
Masu wannan matsalar bai kamata su fara amfani da Allurar Norist ba :
- Ciwon daji na mama
- Mace mai juna biyu
- Masu hawan jini
- Masu wankan jego.
- Masu matsalar zubar da jini.
Kamar yadda muka yi magana a baya idan aka ga waɗannan alamomin lokacin amfani da maganin planning a yi gaggawar zuwa asibiti:
- Ciwon kai mai tsanani
- Gani dishi-dishi
- Rashin ji sosai
- Ido ya zama yellow
- Ƙaiƙayin jiki
- Kumburin ƙafafuwa
- Ɗaukewar Numfashi
Abinda ma’aurata ya kamata su sani shi ne, ga kaɗan daga cikin amfanin ɗaukan matakin tazarar haihuwa da zaran an haihu:
- Yana hana mata samun cikin da ba a shirye shi ba har tsawon wata shida bayan haihuwa.
- Yana hana samun ciki idan har an sami waɗannan abubuwa uku da aka faɗa a sama..
- Za a iya farawa da zarar an haihu.
- Bashi da illa.
- Hanya ce mai sauƙi ba ta buƙatar magani.
- Yana samar da lokaci ga ma’aurata wajen zaɓen wata hanyar idan har wannan ba ta yi aiki ba.
Microgynon
Microgynon: ƙwayoyin tazarar haihu ce, wacce take ɗauke da sinadarin estrogen da progestogen a cikin ƙwaya ɗaya, za ka ganta tana ɗauke da brown colour layi daya, ana amfani da ita don dakatar da haihuwa har zuwa wani lokaci.
Kusan da cewa Haihuwa A Gida Ba Jarumta Bane Kuskure Ne Danna nan domin karanta dalilai
Akan sha shi kullum ƙwaya ɗaya, idan kika sha idan kin sadu da minjinki insha Allah babu maganar juna biyu, wannan maganin hukumar lafiya ta duniya ta amince a yi amfani da ita kuma ba ta ba da matsala idan aka yi amfani da ita yadda ya dace, idan ko kika samu matsala ya kamata ki ziyarci asibiti domin ganin masana.
Wannan maganin bayan tazarar haihuwa ana amfani da shi domin magance wasu matsalolin na mata, kamar rikicewar sinadaran hormones.
Wannan maganin idan aka fara amfani da shi yana zuwa da wasu canje-canje ga wasu matan ba dukka ba, kamar kowanne magani tana da side effects.
Daga Cikin Canji Da Ake Samu Akwai:
- Ciwon kai
- Kumburin nono
- Ciwon ciki
- Tashin zuciya
- Ƙara jiki
- Hajijiya
- Rikicewar Al’ada zuwa ɗan lokaci
- Rashin ganin al’ada.
Akwai wasu wanda ba a amince da su yi amfani da maganin tazarar haihuwa mai suna microgynon, daga cikin su akwai:
- Masu ciwon kai ɓangare ɗaya (migraine headache)
- Masu hawan jini.
- Masu ciwon zuciya
- Masu shanyewar ɓangaren jiki (stroke)
- Masu ciwon hanta
- Masu Ciwon nono (Breast cancer)
- Masu Shayarwa (da haihuwa zuwa sati shidda)
- Waɗanda shekarun su ya haura 35 zuwa sama.
Binciken masana ya nuna cewa amfani da microgynon tare da waɗannan magunguna yakan iya kawo matsala, ga su kamar haka:
- Rifampicin
- Primidone
- Griseofulvin (Fulcil)
- Nevirapine
Waɗannan magunguna suna rage ƙarfin maganin ne. Haka wani binciken ya nuna ampicilin ma yakan iya rage ƙarfin maganin.
Akwai wasu alamomin da idan aka gani lokocin amfani microgynon a dakatar da amfani da maganin, ga su kamar haka:
- Ciwon kai mai tsanani
- Gani dishi-dishi
- Rashin ji sosai
- Ido ya zama yellow
- Ƙaiƙayin jiki
- Kumburin ƙafafuwa
- Ɗaukewar Numfashi.
Gargaɗi:
Kada a yarda a karɓi maganin a chemist saboda sai an yi gwaje-gwaje da bincike kafin a ba da maganin.
Contraceptive Implants: ana kiranta ashanar fata da Hausa, wannan wata hanya ce da ake dasa wata roba ƙarama a hannun mace.
Domin karanta bayani akan Warin Baki (Mouth Odour) Danna nan
Ita wannan roba za ta riƙa fidda wani hormone da ake kira da suna progestin a cikin jini ne da zai hana mace ɗaukan ciki.
Yana iya zama a jikin mace har na tsawon shekara 3. Amma ana iya cire shi duk lokacin da ake buƙata a asibiti.
Ashanar fatan yana sakin sinadarin Progestin a hankali. Sinadarin zai sa ƙofar mahaifa (cervix) ta yi kauri da majinan gamsai domin hana maniyin namiji haɗuwa da ƙwan mace, wannan sinadarin kuma na hana fitowar ƙwan mace.
Waɗanda Bai Kamata Su yi Amfani Da Implant Ba:
- Idan mace tana fuskantar ko fama da zubar da Jini daga farji ba tare da sanin dalilin sa ba.
- Idan mace tana da alamar cutar dajin nono ko kuma akwai tarihin masu cutar dajin nono a cikin zuriyar su.
- Idan mace tana shan maganin farfaɗiya ko maganin TB kaman rifampicin. Saboda maganin zai iya rage ingancin aikin implant.
- Idan mace tana ɗauke da ciwon daskarewar jini.
- Mata masu ciwon hanta mai tsanani.
Wasu daga cikin matan bayan an saka musu implant suna fuskantar waɗannan matsalolin:
- Tashin zuciya
- Ciwon Kai
- Hajijiya
- Ciwon ciki
- Pimples
- Kumburin Mama
- Fitar da ruwa a farji.
Idan aka ga waɗannan alamomi a yi gaggawa a koma asibiti:
- Rashin warkewar ko kumburi a gurin da aka saka implant din.
- Alamar fitowar implant daga hannu.
- Idan ana son a cire ashanan fatar yayin da mace ta kara ƙiba, kada a yi gangancin cirewa a gida.
- Fuskantar rashin kuzari da ƙoshin lafiya
- Tunani kamar kina ɗauke da ciki.
Note:
Ingancin implant yana raguwa a jikin mata masu ƙiba da nauyin jiki. Mata waɗanda nauyinsu ya wuce 80 zuwa sama, Irin waɗannan mata ya dace su sake wani bayan shekaru 3 (kada a bari zuwa shekaru 5) implanon bayan shekaru 2 kada a bari zuwa shekaru 3.
Yana dakyau ka karanta bayani akan Fitsarin Jini (BLOOD IN UTRINE)
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu