Abubuwan Da Suke Hana Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

0
470

Wannan muhimmin abu wanda kowa yake buri, yana gamuwa da cikas da matsaloli daga ɓangarori daban-daban. A gaskiya ma dai mutane da dama masu begen zaman lafiya da kwanciyar hankali, su da kansu suke janyo hargitsi da tashin hankali ga kawunansu da sauran mutane.

Wannan kuwa yana faruwa ta hanyar aikata abubuwan da suke hana zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ga wasu daga cikin waɗannan abubuwa:

Kafirci

Kafirci shi ne babban abu da yake hana zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma wannan yana nufin kafirai su ne manyan maƙiya ga zaman lafiya da kwanciyar hankali. Allah Ta’ala ya ce “Kuma wanda Allah ya yi nufi ya ɓatar da shi, sai ya sanya ƙirjinsa a ƙuntace, kamar mai hauhawa cikin sama” (Suratul An’am: 125).

Wannan aya tana siffanta irin damuwa da ƙunci da tsiya da kafiri yake ciki saboda kafircinsa. Ko da kuwa ya mallaki komai a duniyar nan. Dalilin wannan shi ne babu imanı tabbatacce a zuciyarsa, kuma ba shi da tabbatacciyar makomarsa.

Ga rashin ƙa’idoji da ladabai na gaskiya masu tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Misalai a nan suna da yawan gaske, amma gajeren nazari kan rayuwar kafiran Amurka da sauran ƙasashen Turai na yaɗuwar kowace irin ɓarna, kamar fashi, fyaɗe, kisan kai da baƙin zalunci da ɗimuwa da madawwamiyar firgita, zai nuna mana yadda kafirci ke hana zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya Allah ka ƙara kiyaye mu. Amin.

Saɓon Allah da aikata miyagun laifuffuka

Saɓo da mugunta su ne abubuwa masu daraja ta biyu da suke fatattakar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wannan abu a fili yake, saboda duk wani mai saɓon Allah cike yake da ɓacin rai tsoro da rashin kwanciyar hankali. Misali mazinaci yana cike da tsoro da firgita don kada a gan shi, kuma yana gamawa sai wani irin mummunan ɓacin rai ya turniƙe shi. To ka auna halin da ɓarayi, ‘yan fashi, manema maza da sauran masu saɓo suke ciki. Su da kansu sun san babu zaman lafiya da kwanciyar hankali a tare da su.

Ga abin da kafirin Bamaguje Wani mashahurin masanin falsala wato “Socrates yake cewa: “Haƙiƙa duk mai laifi ba ya rabuwa da tashin hankali da tsiya, musamman wanda ba a yi masa hukunci ba”. Ubangiji Ta’ala ya ce “Duk wanda ya kau da kai daga ambatona (Shari’ a ta) to haƙiƙa rayuwa mai ƙunci za ta tabbata a gare shi, kuma za mu tashe shi ranar Ƙiyama makaho” (Suratu Taha: 122) A wannan aya Allah Ta’ala ya tabbatar da rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali ga duk wanda ya keta hurumin shari’arsa, ya kama son zuciya ƙaunar nau’o’in saɓo da aiki da “kwance-tushe (constitution).”

Hassada da ganin ƙyashi

Hassada wani mummunan ciwo ne da yakan kama zukatan masu raunin imani da jayayya da ikon Allah. A duniyar nan babu wahalalle irin mahassadi. Saboda shi kullum baƙin ciki yake ga baiwar da Allah yake yi ga bayinsa, in tashi ne a kwace a ba shi, ko a fasa kowa ya rasa.

Asara biyu ce ke afkuwa ga mahasadi, ta farko a duniya, domin a maimakon Allah ya kwace baiwarsa ga wanda yake yiwa hassadar, sai ma dai ya ƙara antayo masa ita, shi dai sai dai ya yi ta ci baya, haka zai ƙare a tsiya ce.

A nan Bahaushe ya yi gaskiya, inda ya ce, “Hassada ga mai rabo taki ce”.

Asara ta biyu ta shafi addini, da farko dai ga zunubin fushi da jayayya da hukuncin Allah, Ga zunubin gaba da musulmai, ga koyi da shugabannin mahassada wato Shaiɗan, Kabila da Arna, sannan kuma uwa-uba, hassada tana cinye lada kamar wuta da shiba. Ya ɗan uwa in dai kana son zaman lafiya da kwanciyar hankali, to ka wanke zuciyarka, ka saki ranka ka yarda da ikon Allah, in ka ga Allah ya yi ni’ima ga wani kada ka yi fushi, in kai ma kana so, ka roƙi Allah kuma ka bi halaltacciyar hanya domin neman abin. Sai ka huta da wahalar banza.

Gaba da riƙo

Gaba da mutane da matsanancin riƙo a cikin zuciya, su ma suna kandagarki ga samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wannan shi ya sa kafin muminai su shiga aljanna sai an wanke zukatansu tas, an kawar da duk wani fushi da gaba daga zukatunsu, saboda ita aljanna gida ne na zaman lafiya da kwanciyar hankaii, mai gaba da riƙo kuwa ba shi da wani rabo a cikin wannan babbar ni’imá ta Allah. Saboda haka ɗan uwa ka so ‘yan uwanka musulmai, ka yi musu afuwa ka mance baya, domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Fushi

Duk mutumin da ba shi da haƙuri, mai saurin fushi bini-bini ya tada jijiyar wuya yana huci, to haƙiƙa wannan mutum ba shi ba zaman lafiya ballantana kwanciyar hankali.

Dalilin wannan kuwa a fili yake saboda ita wannan rayuwa cike take maƙil da abubuwan haushi a kewaye da ɗan Adam, dole ka ji ko ka gani ko ka shaƙa, a gida ko a hanya ko a kasuwa kai har a masallaci da makarantu, to in ba ka yi haƙuri ba yaya za ka yi? Sai dai in za ka iya zama kurma kuma makaho, in kuwa ba haka ba, to ka yi haƙuri, in duk ka ƙi wannan to ka yi sallama ke nan da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Zalunci

Allah Ta’ala ya ce: “Haƙiƙa azzalumai ba za su rabauta ba (Suratu Yusif: 23). Wannan aya ta tabbalar ƙarara cewa ko a duniya ko a lahira da azzalumai ba su taba samun zaman lafiya da kwanciyar hankali ba.

A halin yanzu babu buƙatar dogon bayani a kan wannan magana. Babbar shaida ita ce irin matsanancin tashin hankali da firgita da manyan azzalumai suke ciki a ko’ina a duniya. Duk inda za su za ka gansu a guje, suna kulli-kurciya da wasan ɓuya da jama’a. kai da dama daga cikinsu ba sa iya barci, sai sun sha ƙwaya, kuma duk inda za su, sai ka ga tsaro da muggan makamai kamar za a yaƙin duniya. Daga ƙarshe Allah yakan ƙarbi rayukan azzalumai cikin ƙasƙanci da wulaƙanci da tozarta. Kai Allah wadaran azzalumi. ɗan uwa a guji zalunci babba da ƙarami domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali

Tsoron wanin Allah

Duk mutumin da baya tsoron Allah, to lallai zuciyarsa za ta cika da tsoro da fargaba, mai dalili da mara dalili. Duk lokacin da mutum ya shiga cikin irin wannan hali to shi da zaman lafiya da kwanciyar hankali sai yadda ta yiwu.

Imamu Malik (Radiyallahu Anhu) ya ce “Ka ji tsoron Allah sai komai ya ji tsoron ka, in kuwa ba haka ba sai ka yi ta jin tsoron komai har inuwarka”
To ɗan uwa ina ka nutsuwa ga wannan mutum?

Camfi

Wani Shaihin malami mai nazari kan ɗabi’ar ɗan Adam Dokta Aziz Farid ya ce: “Mai imani da camfe-camfe yana faɗawa cikin musibu fiye da waɗanda yake tsoro”!

Wato duk mutumin da ba zai yarda da tsarin Allah ba cikin rayuwarsa, a’a ya miƙa wuya ga camfe-camfe sai an yi kaza-kaza zai faru, in ba a yi kaza ba kaza ba zai faru ba, to wannan shi ma ya yi sallama da zaman lafiya da kwanciyar hankali. In kana so ka tabbatar da wannan magana, ka yi nazarin rayuwar mutumin da ya yi imani da camfi ka ga ruɗu da firgici, ɓacin rai, wahala, tashin hankali iri-iri rashin zaman lafiya da kowa. Ya Allah ka tsare mu.

Mummunan zato

Allah Ta’ala ya ce “Ya ku waɗanda suka yi imani, ku nisanci yawancin zato saboda wani sashi na zato zunubi ne” (Surat Al-Hujrat: 12). Kuma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ku guji zato, saboda zato shi ne mafi ƙaryar zance” (Bukhari da Muslim ne suka rawaito).

Idan mutum ya kasance kullum cikin mummunan zato ga kowa to zai rasa abokin zama, saboda da haka sai ya kasance cikin tsoro da tashin hankali, daga nan sai ya yi ban kwana da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Girman kai

Mai girman kai yana rayuwa cikin tsiya, nunƙufurci da ɗacin rai, kafin kuma ya tunkuyi burjı (mutuwa) ya madawwamiya. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: game da rayuwar ƙasƙanci “Wanda yake ɗauke da ƙwayar zarra na girman kai a zuciyarsa, ba zai shiga Aljannah ba” (Bukhari).

Mutum mai girman kai, yakan take gaskiya, ya rinka wulaƙanta mutane, kuma duk da haka shi yana so a girmama shi, amma sai burinsa ya kasa cika, daga nan sai fushi da damuwa ya kama shi, sai zalunci shi ke nan shi ma sai ya nemi zaman lafiya da kwanciyar hankali ya rasa. Allah ya jiƙan Ɗan Maraya inda yake cewa “Girman kai rawanin tsiya”.

Rataya zuciya da wanin Allah

Wannan ya haɗa ka ƙwallafa rai, ka da wannan ya haɗa sakankancewa da samun wani abu daga wani mutum ko abu, ko makauniya kuma matsananciyar soyayya ga wanin Allah. Yin haka yana jawo ɗimbin wahala da ɓacin rai da tashin hankali. Ya ɗan uwa domin tabbatar da haka yi ƙoƙari ka karanta labarin nan na soyayya na Majnun Laila ka ga irin rayuwar wahala da tsiya da ya yi, kuma duk a banza. Ko kuma ka yi nazarin rayuwar wani wanda ya ƙwallafa ransa kan wani mutum ko albashi ko sana’a ya mance da Allah, ka ga yadda suka yi hannun riga da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Shan abubuwa masu sa maye.

Waɗansu ƙidahumai sokwaye sukan danƙarawa kansu ƙwayoyi da sauran abubuwa masu daɗin rai da nutsuwa, sa maye wai don su sami daɗin rai da nutsuwa, amma ina! Sai ka ga kamar mai ihun gobara ne, kuma ya tuttula fetur a cikin wutar. To yanzu mai karatu ka taɓa ganin wani ɗan ƙwaya cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali? A yi hattara.

Waɗannan kaɗan ne daga cikin abubuwan da suke hana zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma.

Wataƙila mai karatu ya ce, to shin waɗanne abubuwa ne suke tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali na gaskiya? To mai karatu ya gyara zama ka sha karatu.

Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Suke Kawo Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Sakamakon Zalunci Yake danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Hanyoyin Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali; wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceRuɗani Game Da Hanyoyin Samun Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali.
Labarin na GabaShirye-Shiryen Gidajen Rediyo A Kano Da Tasirinsu Ga Tarbiya