Yadda Sakamakon Zalunci Yake

0
384

Shi kuwa zalunci babu abin da yake haifarwa ga azzalumai da ƙasa sai musiba da bala’i a duniya da lahira.

Sakamakon Zalunci – Kowane irin zalunci babba da ƙarami gamammen zalunci wato zalunci da shugabanni suke yiwa miliyoyin mabiyansu; da kuma zalunci da ɗaiɗaikun mutane suke yi wa junansu, kamar zalunci tsakanin ma’aurata; da ubangida da yaronsa da maƙocin da malami da ɗalibansa da sauran rukunonin al’umma; duka irin waɗannan zalunce-zalunce Allah Ta’ala ba ya barinsu su wuce kawai ba tare da wani sakamako ba.

Sakamakon wani zalunci yakan kasance hallakar da gaba ɗayan al’umma; kamar yadda ya faru ga Adawa da Samudawa da mutanen Annabi Luɗu. Wani sakamakon yakan tsaya ne kawai a kan wanda ya aikata zalunci shi kaɗai.

Amma kuma idan mutanen kirki suka rungume hannu suka zura wa azzalumai ido suna sheƙe ayarsu, babu mai kwaɓar su, to sakamakon in ya zo yakan shafi kowa da har managartan, saboda ƙin ɗaukar matakin hana zalunci sakamakon zalunci yakan kasance ta hanyoyi daban-daban kamar talauci mai naci, taɓarɓarewar tsaro, yunwa, azzaluman shugabanni da koma baya da rashin ci gaban al’umma.

Alƙur’ani mai girma da hadisan manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) cike suke da bayanan mummunan sakamakon azzalumai a duniya da lahira.

A dunƙule ga abin da suke nunawa;

1. Allah Ta’ala baya ƙaunar zalunci ba ya kuma ƙaunar azzalumai, yana fushi da su yana la’antarsu.

2. Zalunci yana janyo musiba a bayan ƙasa kamar girgizar ƙasa, ambaliyar ruwa, tsawa, iska, gobara, yawan mace-mace, annoba, fari da sauransu.

3. Zalunci yana jefa mutane cikin ɗimuwa da kiɗima da rashin samun shiriya ta yadda za a fita daga halin da ake ciki, haka kuma yakan ƙeƙasar da zuciya, azzalumai su ƙi tuba har su mutu a kan zaluncin su gamu da matsananciyar azaba a lahira. Shi ne ma’anar faɗin Allah Maɗaukaki:”Allah ba ya shiriyar da azzalumai.

4. Allah Ta’ala ba ya ba da nasara da rinjaye ga azzalumai koda kuwa an ga sun ci wata nasara to ba mai ɗorewa ba ce, kuma abin da zai biyo baya na musiba da sharri ba ƙarami ba ne.

5. A lahira azzalumai ba za su ji da daɗi ba domin akwai azzaluman da za su shiga wuta har abada ba za su fita ba, waɗansu kuma za su daɗe a cikinta gwargwadon irin zaluncin da suka yi.

6. Azzalumai ba za su samu rabauta ba a lahira.

7. Ba za su samu kariyar Allah ba.

8. Ba za su shiga inuwar Allah ba.

9. Allah Ta’ala zai haɗa su da waɗanda suka fi ƙarfinsu su gana musu uƙuba.

10. ƙasar da zalunci ya samu wurin zama, sama da ƙasa ba za ta samu bunƙasa ba, ba za a samu kwanciyar hankali da zaman lafiya ba a cikinta, komai sai ya sukurkuce a yi ta ragabza ba ji ba gani ana ci gaban mai haƙan rijiya.

Domin karanta cikakken bayani a kan Nasihohi Goma Ga Masu Kula Da Dukiyar Al’umma danna koren rubutun nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Kura-kuran Masu Bayar Da Tarbiyya. danna koren rubutun nan

labarin da ya wuceƊagowa Daga Ruku’u
Labarin na GabaHalaye Da Siffofin Shugaba Nagari