Abubuwa Wanda Yakamata Mace Ta Kiyaye Lokacin Al’ada

0
27

(1)  A kiyaye barin audiga (pad) ta dade a jiki,koda jinni baya ta kiyayei amfani da  ruwan kankara ko ruwan sanyi lokocin al’ada sabida amfani da ruwan kankara yakan sa jini ya daskare a mahaifa bazai fita ga baki daya ba,bayan shekaru 5 zuwa 10 sai yakawo ciwon daji na mahaifa.

(2)  Ta kiyaye saka shampoo a kanta lokocin al’ada sabida a wannan lokocin kofar gashi a bude take kuma shigar shampoo kofar gashi yana kawo ciwon kai mai tsanani.

(3)  Ba’aso mace tayi amfani da gurji (cocumber) lokocin al’ada sabida akwai sinadarai a jikinta wanda zai iya hana jinin yafita gabaki daya,wanda daga karshe zai kawo ciwon daji na mahaifa.

Koda wasa kada kiyarda a daki cikin ki,kuma ki kiyaye duk abinda zai daki cikin ki sabida dukan ciki a wannan lokocin zaijiwa mahaifa rauni wanda daga karshe zai zama ciwon daji, kuma yana kawo aman jini lokoci guda.

Domin karanta cikekken bayani akan Post Injection Inflammation: {Kumburi Bayan Anyi Allura} Danna nan 

(4)  A kiyaye amfani da  gishiri mai yawa amfani da gishiri (manda) diyawa yana kawo yawan zubar da jini kuma yakan sa ruwa ya taru a mahaifa,akiyaye amfani da ƙwaƙwa (coconut) lokocin al’ada sabida tana tsananta alamomin al’ada kamar ciwon ciki da sauran su.

(5)  A kiyaye amfani da barasa (giya) lokocin al’ada duk da bincike ya nuna tana rage radadi lokocin al’ada,to akwai matsaloli diyawa da zai iya kawowa zuwa sosai Kada ayarda abar pad a jikinki samada awa 3-4 lokocin al’ada.

(6) A kiyaye amfani da tabar sigari, dukkan mu munsani tabar sigari tana da illa ga lafiyar jikinmu bayan haka bincike ya nuna amfani da shi lokocin al’ada tana saka alamomi suyi tsanani.

Abubuwa Wanda Ake Tunanin Za Su Iya Kawo Jinkirin Al’ada:

  • Juna Biyu
  • Shayarwa
  • Shigan ƙwayar cuta
  • Magungunan tazarar haihuwa
  • Kunburin kwan mace (ovarian cyst)
  • Rashin kwanciyar hankali (Stress)
  • Motsa jiki mai tada hanakali.
  • Rashin samun lafiyayyan abinci da isheshshen
  • Cututtuka kamar zazzabin typhoid.
  • Matsalar sinadaran hormones.
  • Magunguna irinsu maganin cancer.

Domin karanta bayani a kan wani lokacin ina G.O.P.D ko breast cancer ko HIV/AIDS danna wannan koren rubutun 

Karanta cikekken Mataki Domin Kare Kanka Daga Kamuwa Da Ciwon Ƙoda Danna nan

labarin da ya wuceMataki Domin Kare Kanka Daga Kamuwa Da Ciwon Ƙoda
Labarin na GabaWani Lokacin Ina G.O.P.D