Cututtuka Da Ake Dauka Ta Jima’i

0
67

Cututtuka Da Ake Dauka Ta Jima’i: Akwai cutuka da dama da ake dauka ta hanyar jima’i masu matukar lahanin gaske ga lafiya.

Ga kadan daga cikinsu

 1 Gonorrhoea:Ciwon sanyine mai ta’adi wanda yakan kama mace ko namiji ta hanyar jima’i da wanda ke dauke da ƙwayar cutar,masu aure ko wadanda basu da aure.

  • Tana da alamu kamar haka tana haifarda fitar farin ruwa ga al’aura,wani lokaci suna da wari kamar na danyen kifi.
  • Tana sanya fesowar ƙuraje ga matse matsi ko a gaban mace,ga ƙaiƙayi ko yaushe hannu a cikin wando.
  • Tana shanye ni’imar mata ya kasance mace bata da wani ni’ima na zamanta ‘ya mace.
  • Tana zuƙe girma da kaifin takobin namiji,takobin mai gida zai kasance baya da kaifin yankan ko albasa balle nama.
  • Tana janyowa mace ƙyama ga mijinta,Idan ba’a yi saurin maganceta ba kuma tana hana haihuwa(sterile)
  • Tana tsinke maniyin namiji ya koma ruwa zalla(watery sperm fluid)
  • tana sanya ciwon gabobin jiki da yawan ciwon kai,dama ƙugin ciki

 2 CHLAMYDIA:Kamar ciwon sanyi yake amma ya banbanta kadan da sanyi kuma ƙwayar cutar dake kawo su ba iri daya bane.

  • Yana haifarwa mace zubar fararen ruwa,watarana harda jini,da ƙaƙayi da zafin saduwa da kuma yayin fitsari,shima idan ba’a dauki mataki ba to yana hana haihuwa ga mace ko namiji (infertility)

Yana dakyau ku karanta dalili dake jawo karancin numfashi ga jarirai bayan an haifesu 

3 Syphillis: Da hausa ana kiransa da suna tunjure,ya janyo ƙurajen gaba ga mace ko namiji,ko kuraje ga dubura,ko baki,tana shafuwar ƙwaƙwalwa da idanu da kunnuwa da zuciya

H.I.V/AIDS: Dan kasan ƙanjamau yana janyo rama,gudawa,ƙuraje a cikin baki,ƙuraje ga al’aura,ga kasala,tari da yawan rashin lafiya da makamantansu

5 HERPES SIMPLEX VIRUS: wato wasu ƙurajene zasu iya fitowa a wajaje daban daban kama daga cikin baki,ko akan lebɓa ko a cikin hanci ga al’aura ko maƙogwaro,suna da zafi kuma suna mata jin ciwo a yayin saduwa.

6 CANDIDA BALANTIS Wani ƙurji ne dake fitowa akan zakari ko kaciyar namiji ya girma,ya janyo zubar ruwa yayin fitsari da jin ciwo

Domin karanta Menene Yake Jawo Fitar Farin Ruwa Daga Gaban Mace,Wannene Na Cuta Wannene Na Lafiya Shiga nan

labarin da ya wuceLarurar Dannau [Sleep Paralysls] Da Yadda Za’a Magance
Labarin na GabaCiwon ƙaba (Hernia) Da Yadda Za’a Kare Kai Daga Hernia