Wani Lokacin Ina G.O.P.D

0
63

Wato ɗan adam bakomi bane,kana tafe ne kana mutuwa a hankali,ana haka kafafunka sai su daina iya daukarka kaga sun mutu kenan,ana nan ido sai ya rage gani,daga nan a hanaka cin gishiri,daga sanda aka fara karka ci kaza,kaci kaza…kai kasan babu randa za’a dawo ace kaci gaba da cin komi yadda kake so!

Dattijo ne ga wadata Allah yai masa alhamdulillahi,amma yana zaune bayan na dubasa sai nake faɗamasa banda zama cikin Ac,banda tsayawa inda fanka ke juyawa,sannan ƙwanakin baya can na hanasa cin nama da abu me zaƙi,cikin rawar murya ina gama bayani yace mun to dakta zan kiyaye.

Ji nai duk jikina yai sanyi,ya saki,na tambayi kaina in nine a matsayinsa ake ban wannan umarnin ya zanji? hakika akwai damuwa,musamman gashi kana da sukunin da bawai mota ba ko jirgin sama ne mutum me iya saya ne,amma hakan shine kurum mafita, sai hakuri.

Bayin Allah ku kyakkyawan kula da lokacinku,lafiyarku da karfinku, ku bi Allah,kubi annabi. Allah ka kyautata karshen mu. 

Domin karanta cikekken bayani akan Post Injection Inflammation: {Kumburi Bayan Anyi Allura} Danna nan 

labarin da ya wuceAbubuwa Wanda Yakamata Mace Ta Kiyaye Lokacin Al’ada
Labarin na GabaBreast Cancer