Halaye Da Siffofin Shugaba Nagari

1
987

Shugaba Nagari – Ya kamata kowane Shugaba daga sama har ƙasa ya sifantu da waɗannan halaye:

1) Adalci shine tushen samun nasarar kowane Shugabanci adalcin Allah Ta’ala shi ne yake riƙe da sammai da ƙassai; da duk wanda yake ƙarƙashinsa yake bai wa kowa haƙƙinsa babu nuna wani bambanci.

Amr ibnul As Radiyallahu anhu yana cewa; mulki ba ya yiwu wa sai da tsayayyun jami’ai, su kuma ba za su samu ba sai da kuɗi, kuɗi kuma ba ya samuwa sai ana raya ƙasa, raya ƙasa ba ya yiwuwa sai da adalci.
Yana daga adalci shugaba ya hana azzalumai zalunci yana hana maɓarnata ɓarna, kada ma ya bari sai talakawa sun fara kokawa, saboda in har aka kai matsayin da suka fara kokawa to za su iya ɗaukar doka a hannunsu.

2) Lallai ne shugaba ya kasance mai nisantar zubar da jinin mutane kada ya yi kada ya bari a yi.

3) ya kasance mai magana ɗaya babu ƙarya babu yaudara.

4) ya zauna lafiya da mutanen kirki masu tsoron Allah; kada ya saki fuska ga azzalumai da ashararai kada su samu sakewa a ƙarƙashin ikonsa.

5) Shugaba ya kasance mai cika alƙawari mai faɗar gaskiya in ya san ba zai yi ba; kada ya ce zaiyi, kada kuma bai yi ba ya ce ya yi.

6) Kada ya raina abokin gaba komai rauninsa ya yi masa maka ido.

7) Lallai ne ya sami likita na musamman ƙwararre mai amana masoyi na haƙiƙa; kuma kada ya dogara da likita guda ɗaya, a’a ya sami wadatattun likitoci waɗanda in wani gagarumin ciwo ya same shi za su haɗu a kansa in bakinsu ya zo ɗaya akan irin maganin da za’ayi masa to sai a yi bayan shawartar waɗansu amintattunsa keɓaɓɓu.

8) ya bai wa mataimakinsa muhimmanci sosai, kada ya ture shi gefe guda ta yadda zai zama kamar ɗan kallo a harkar mulki; amma kuma kada ya bari ya sake ya miƙe ƙafa har ya fi shi ƙarfi ya zama kamar shine shugaban shi kuma ya zama hoto.

9) Haka kuma ya samar da kyakkyawar jituwa tsakaninsa da ‘yan majalisarsa ya ringa zama dasu akai – akai yana shawartarsu kowa ya ji cewa ana yi da shi; babu ɗan mowa a cikinsu, babu kuma waɗansu fulogai waɗanda su kaɗai ne suke jan mai kuma in babu su babu inda za a je. Wannan zai haifarwa da shugaba babbar matsala.

10) Shugaba ya kula da tattalin arziƙi sosai musamman sana’o’i da harkokin kasuwanci ya buɗawa mutane hanyoyin samun arziƙi da ayyukan yi musamman ga matasa; ya ringa tallafawa ‘yan kasuwa, kada ya ɗora musu haraji mai yawa ko ya basu bashi da kuɗin ruwa. Lalle ne shugaba ya kiyayi abin hannun mabiyansa. Ya guji karɓe- karɓe da cin hanci da rashawa.

11) Ya kasance mai tattali da tsimi da tanadi da shirin ko- ta- kwana; musamman tanadin abinci da kayan masarufi saboda ba da agajin gaggawa a lokacin da wata musiba ta afko kwatsam ta; yadda ba sai an fita waje da ƙoƙon bara ba.

12) Ya kasance mai alƙawari ya yi kyakkyawan sakamako ga duk wanda ya taimaka masa; musamman a lokacin da yake neman mulki. Kada su tura mota ta tashi ta bar su da hayaƙi.

13) Kada ya bari wani talaka ya san wurin hutunsa da shaƙatawarsa ballantana ya je wurin; wannan zai janyo raini manyan mutane kaɗai zai bari su ringa halartar irin wannan wurin; in ya buƙaci zuwansu domin tattauna muhimman al’amari cikin nutsuwa.

14) Ya yi ƙoƙarin aikata duk abinda zai jawo masa baƙin jini da maƙiya.

15) Kada ya naɗa ‘yan uwansa a manyan muƙamai saboda gudun hassadar ‘yan uwa. Amma ya kai matuƙa wajen kyautata musu da mutunta su; sannan kuma ya sa ido a kansu ya yi kaffa – kaffa da su, ya yi haƙuri kan cutarwarsu.

16) Lallai ne shugaba ya riƙe halaye guda uku;
1. kyauta 2. Haƙuri 3. Da tabbatar da gaskiyar komai kafin ya ɗau mataki akansa.

17) Ya ringa yabo da zargi daidai ƙurji daidai ruwa. Wato kada ya yi yabo fiye da ƙima kada ya yi ta zargi, faɗa, ko mita fiye da ƙima. Haka kuma ya daidaita tsakanin alƙawarurrukansa da barazanarsa. Kada barazana ta fi yawa, kada kuma alƙawari yafi rinjaye.

18) Ya kasance mai halin ba-sani-ba- sabo duk wanda ya taka doka, doka ta taka shi.
A dunƙule dai abubuwa uku ne suke tabbatar da nagartar mulki;
1- Ɗaukaka da inganta addinin mutane
2- Tabbatar da tsaro da zaman lafiya
3- Inganta rayuwar al’umma.

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan 

labarin da ya wuceYadda Sakamakon Zalunci Yake
Labarin na GabaSahihin Sirrin Ƙulhuwallahu Ahad

SHARHI ƊAYA