Vaginal Infection

1
78

VAGINAL INFECTION: Wata cuta ce da mafiya yawan jama’a suna kiranta da vaginal Infection,masana kiwon lafiya suna kiranta (Vaginitis) sabida wannan matsalar tana addabar gaban mace, hmma a hausance ana kiranta da ciwon sanyin mata.

Wannan cutar wasu ƙwayoyin cutane Irinsu bakteriya,fungus,virus masu illartarwa su suke kawo shi babban mutum sai iya kamuwa da shi haka yara ma zasu iya kamuwa da wannan cutar.

Ba wai kawai ta hanyar jima’i ake daukan wannan Infection ba

 Ga Kadan Daga Hanyoyin 
  • Amfani da kayan aiki ba tare da an tsaftace shi ba lokocin haihuwa ko wanke ciki.
  • Tsaftace gaba ta hanyar amfani da sabulu mai kashe kwayoyin cuta
  • Tusa hannu ko yatsa a gaba
  • Amfani da wandon wata musamman pant
  • Barin wadon yadauki datti (pant)
  • Rashin canza pad akai akai lokocin al’ada 

Yana dakyau ku karanta Babban Dalinlan Dake Kawo Rashin Haihuwa [Infertility]

Kadan Daga Cikin Ƙwayoyin Cutar Da Suke Kawo Wannan Matsalar:

Bacteria Vaginosis: Wannan wata ƙwayar cuta ce dake rayuwa  cikin farji yakan haddasa matsalar sanyin mata .

Candidiasis: Wannan wata ƙwayar cutace wanda yake haddasa sanyin gaba,wadannan ƙwayoyin cutar suna zama cikin farji kuma basu cika cutarwa ba,wadannan kwayoyin cutar suna son waje mai gumi domin su girma dan yaduwa.

Trichomonas Vaginalis: Wannan itace wacce take yaɗuwa ta hanyar jima’i,ita wannan ƙwayar cutar parasite ce take kawoshi

Irritation Vaginitis: Ita wannan ana kiranta da allergic,wasu abubuwan da jikin mutum bai dauke su ba,anasamunsa wajen amfanida kamar su condom, sabulu,ko maganin shafawa.

Alamomin Ta:

  • Kuburin gaba
  • Canza Launin gaba zuwa Ja
  • Ƙaiƙayin gaba
  • Warin gabs
  • Ƙurajen gaba
  • Zubar da farin ruwa a gaba
  • Zafin lokacin Jima’i
  • Zafin fitsari.
Yadda Mace Za Takare Kanta Daga Vaginal Infection:

Kada  a Tsaftace daba da sabulai masu kashe ƙwayar cuta: A cikin farji akwai wasu ƙwayoyin bakteriya waɗanda basa cutarwa kuma sunada amfani,amfaninsu shine suna taimakawa wajen bada kariya ga farji,sai kaga wasu matan sukan wanke farji da sabulu ko dettol haka,wadannan abubuwanda ake amfani wajen wanke farji yakan kashe bakteriya masu amfani na farji,sai masu cutarwa su samu daman shiga,abkiyaye wanke farji da sabulu dakuma wadansu abubuwa wanda bamusan kansu ba.

Domin sanin menene Zazzabin Typhoid Danna nan

A Tsaftace waduna: Amfani da wandon pants,wasu matan sukan bar wandonsu yayi datti,barin datti ko amfani pant masu datti yakan bawa ƙwayoyin cuta daman shiga farji,atsaftace wanduna.

A kula wajen wanke bahaya: Mafi yawa mata sukan dauki ƙwayar cutar da take dubura zuwa farji,wanda basa yiwa dubura illa amma sukan yiwa farji illah,shawara shine a fara wanke farji kafin a wanke dubura.

Amfani da pants na wassu: ta yiwu wacce kuke amfani da pants daya tanada cutar sanyi idan kinyi amfani da nata kema zaki iya dauka,sai a kiyaye.

Mutum yakan iya daukar wannan cutar lokocin saduwa da namiji idan namijin yana dauke dashi,hanayar mariya itace amfanida condom lokocin saduwa.

A kiyaye amfani da magungunan gargajiya musamman wanda ake cusa su a gaba,suna taimakawa wajen samun ƙwayoyin cuta.

Mesa Korafin Rashin Warkewa Yayi Yawa 
  • Idan namiji da matar sa suna dauke da wannan cutar,abinda ya dace dukkansu biyu za sufara shan magani,bawai matar kadai ba,muddin shi kadai ne a cikinsu ne yake shan magani akwai matsala.
  • Duk matar da aka ɗaurata akan magani duk sanda ta cire wandonta yakamata ta wanke da antiseptic kafin ta maida wannan wando hakan yana taimakawa wajen warkewa .
  • Idan akaci gaba shan magani kuma ba’a kiyaye wasu hanyoyin da suke kawo wannan cutar ba shima akwai matsala sosai.

Domin karanta bayani akan Pelvic Inflammatory Disease (PID) Danna nan

labarin da ya wucePelvic Inflammatory Disease (PID)
Labarin na GabaNoristerat (Norist)

SHARHI ƊAYA