Babban Dalinlan Dake Kawo Rashin Haihuwa [Infertility]

0
28

Rashin haihuwa shine rashin samun ciki (juna biyu) bayan shafe watanni goma sha biyu “wato shekara guda” ana samun jima’i tsakani batare da amfani da wata kariya ba ko maganin hana daukar ciki.

Saidai Abun Lura Shine

Rashin haihuwa ba matsalar mace bane ita kadai,namiji ma matsalar na iya kasancewa daga gareshi,wanda kuma da yawa mazan Kan zargi matan,saide akan zargi matsalar daga mace idan matan mutum suka kasance biyu ne kuma dayar a ciki ya zamto tana haihuwa to shine sai ai tunanin matsalar daga macen ne.

Saidai baza a iya cewa mutum baya haihuwa ba koda anshafe watanni 12 ba,har sai bayan shekara 5 tukun.

Yana dakyau ku karanta menene Ƙurjin Farji da kuma maganin sa

Me Ke Jawo Infertility

A dangane da namiji duk wadannan abubuwan na iya hana sa haihuwa

  • Karancin kwayayen halitta,ko sakamakon haka mutum ya tsinci kansa,ko asakamakon yawan masturbation,hatsari,da sauransu.
  • Rashin kwarin kwayayen halitta
  • Cuta me karya garkuwar jiki,ko ciwon asthma.
  • Ciwon sanyi wato fitar farin ruwa daga gaba,musamman masu saduwa da mata barkatai
  • Idan golon mutum suka zamto kananu ko daya yafi daya musamman in suna ciwo
  • Ko wata matsala data shafi mazantakarsa wacce ta zamto ta gado ce,kamar kankantar azzakari ya zamto ba tsayi
  • Cuttuka irinsu ciwon suga.
A Mata Kuma
  • Ciwon sanyi dake sa fitar ruwa daga gabansu musamman in anyi sakaci batare da neman magani ba,zuwa PID,UTI da cervical cancer.
  • Kumburi awani sashi na cikin mahaifa wato (polyp)
  • K’arin cikin mahaifa (fibroids),mace na iya kaucewa wannan ta hanyar yin aure da wuri,yan mata musamman ayanzu da yawa na haduwa da wannan larurar tare da ovarian cyst.
  • Fara sha ko yin allurar magungunan hana daukar ciki kafin haihuwar farko ko kafin fara samun ciki
  • Idan mace ta taba samun ciki awajen mahaifarta (uterus) memakon cikin mahaifa kamar yadda yake.
  • Idan mahaifar mace ta samu matsala kila ko sakamakon operation da aka taba mata abaya.
  • Cuttuka masu wuyar sha’ani kamar asthma ko ciwon suga ga mace.
  • Haihuwarta da wata nakasa wacce bazata iya bari ta sami ciki ba (birth defects).

Wadannan sune mahimman abubuwan daka iya hana shigar ciki,saidai kamar yadda nace baza ace gaba daya mace ko namiji baya haihuwa ba sai ansami kamar shekara 5 toh sannan ne lallai za’a fara tunanin haka,sannan atashi tsaye wajen neman mafita idan matsalar wacce za’a iya gyarawa ce.

Domin karanta bayani akan Fibroid (Karin Mahaifa) Danna nan 

Alamomin Dake Nuwa Mace Na Iya Fuskantar Wannan Matsala Ta Rashin Haihuwa

  • Rashin ganin jinin al’ada akai akai kowanne wata sama da ƙwana 28.
  • Jin zafi tare da ganin jinin al’ada na fita me yawa (heavy bleeding)
  • Rashin al’ada din ma baki daya.
  • Jin zafi yayin saduwa ko yaushe
  • Canzawar sha’awa taji bama ta so akusanceta wani lokacin

Da dai sauransu,don haka wannan matsala ce da sai an dangana ga kwararrun likitocin mata,daukar ciki da raino wato (Obstetrics and Gynaecologist) aikinsune ba kowanne irin likitane ke handling wannan case din ba.

Domin sanin menene Zazzabin Typhoid Danna nan

labarin da ya wuceƘurjin Farji
Labarin na GabaPelvic Inflammatory Disease (PID)