Pelvic Inflammatory Disease (PID)

0
54

PID: wata cuta ce wacce take addabar bangaren da ta shafi mahaifar mace, da dama a nahiyan africa suna fama da wannan ciwon.

Wasu ƙwayoyin cututtuka ne idan sun samu sunshiga mahaifan mace (uterus, fallopian tubs, ovaries) sai ta haifar da cutan PID. 

Daga Cikin Alomaminta Akwai:
  • Ciwon ƙasan cibi (ciwon mara).
  • Fitar da ruwa mai wari a gaban mace
  • Ganin jini a gaban mace musamman lokacin jima’i da bayan jima’i.
  • Zafi lokacin jima’i.
  • Zazzabi da jin sanyi.
  • Zafi lokacin fitsari ko wahalar fitsari.
  • Kaikayin gaba.
  • Rashin daidaitawar jinin haila. 
  • Tashin zuciya 
  • Ciwo lokacin jima’i
  • Ciwon baya 
Hanyoyin da ake daukar wannan ciwon sun hada da:
  • Jima’i da namiji mai dauke da cutar gonorrhea ko clymadia 
  • Amfani da kayan karban haihuwa wanda tsafta bai ishe su ba
  • Yawan kai dan yatsa cikin farji
  • Amfani ni da wando (fant) wanda mai dauke da wannan cutar tayi amfani dashi
  • Rashin amfani da condom lokocin jima’i
  • Yawan tsaftace gaba da sabulu musamman masu dauke da sinadaran kashe ƙwayoyin cuta.
  • Yawan amfani da maganin kashe ƙwayoyin cuta irin su ampiclox da muka dabi’untu da shan su kullum.

Yana dakyau kusan Babban Dalinlan Dake Kawo Rashin Haihuwa [Infertility]

PID idan ba’a magance shi da wuri ba tana kawo wadannan matsalolin

  • Rashin haihuwa 
  • Zaman ciki wajen mahaifan (entopic pregnancy) 
  • Yakan kawa bari (Abotion ko Miscarriage)
  • Ciwon mara da baya mara jin magani
Hanyoyin Kariya Daga Wannan Ciwon Sun Hada Da:
  • Amfani da condom lokocin jima’i yana rage yaɗuwar PID kashi 95%
  • Mace tasaya akan namiji guda daya kuma a tabbatar anyi gwaji kafin saduwa ko suyi aure. 
  • A kiyaye yawan saka hannu a farji
  • A tsaftace wandon sakawa musamman pant,kuma a kiyaye amfani da pant na wata. 
  • A dinga tsaftace kayan karbar haihuwa da kuma wanke ciki.

Wannan ciwo ta PID tana da magani idan akabi hanyoyi mekyeu

  • Da zaran mace taga alamun da muka lissafa a sama ta gaggauta zuwa asibiti,daganan likita zaiyi gwaje gwaje da yakamata a ayi an tabbata menene matsalar sannan subada magani.
  • Idan kina da miji shima yakamata yaje a gwada shi abaku magani tare
  • Daga nan sai a Kaurecewa Jima’i sai likita ya tabbata muku kun warke. 
GARGADI 

Idan mace tana tareda wannan cutar kuma tayi shiru ta zauna sabida kunya ko makamancin haka yakan jawo mata matsala a mahaifarta daga nan zatafara gamuwa da matsalar zubar da ciki (miscarriage) zaman ciki wajen mahaifa (Ectopic pregnancy) ko kuma rashin daukan ciki gabaki daya.

Domin karanta bayani akan vaginal infection ko Noristerat (Norist) ko abubuwan daya dace a sani akan allurar artemether danna wannan Koren rubutun

Domin sanin menene Zazzabin Typhoid Danna nan

labarin da ya wuceBabban Dalinlan Dake Kawo Rashin Haihuwa [Infertility]
Labarin na GabaVaginal Infection