Ciwan Kai Na Gado Wato [Migraine]

0
47

Wannan na daga cikin cutukan gado da suka fi addabar mata,saidai wasu lokutan yakan addabi wasu daga cikin maza kalilan,amma dai mata ne suka fi zuwa mana dashi asibiti,ciwon kai ne mai tsanani mai zuwa kusan wata-wata kamar al’adar wasu matan,yafi kama ɓari daya na kan mutum,kuma mace zata rika jin alamu kafin yazo wadanda ke nuni da cewa ciwon ya kusa zuwa.

Waɗannan Alamumin Sun Hada Da
  • Rashin son haske 
  • Rashin son jin ƙarar komi
  • Ganin walkiya-walkiya ko dishi-dishi.
  • Riƙa jin ƙauri-ƙauri a hanci
  • Yawan hamma ko miƙa. 

Sai sauran alamun ciwon sun haɗa da:

  • Yawan tashin zuciya, ko amai.

Awasu lokutan kuma ba alamun sai dai kurum aji ciwon kan yazo lokaci guda 

Wani Abu Da Irin Wannan Ciwan Kan Shine:

Matsalar bata cika tafiya da magungunan kashe zogi na panadol ko ibuprofen ba,dole sai anba mutum magunguna masu karfi matsalar take lafawa musamman rukunin magunguna wadanda ke aiki a ƙwaƙwalwa. 

Domin karanta Dalilan Da Suke Sanya Mace Rashin Daukar Ciki Danna nan

Don haka idan mutum na fama da irin wannan matsanancin ciwon kan dole sai yaje wurin kwararen likita musamman ɓangaren ƙwaƙwalwa (neurologist) ya rubuta masa magani mai karfi da kyau wanda ya dace da yanayin mutum,domin ciwon a wasu yakan faru akai akai ba sau 1 a wata ba. 

Meke Haddasa Ciwan

Shi ciwon har yanzu ba’a tantance me yake kawo shi ba,amma andai san yana bin zuri’a wato uwa takan sawa ƴarta Ko ƴaƴan su ɗauka daga uba,ko kakanninsu na ɓangaren uwa da uba. 

Sauran abubuwan da akan danganta da matsalar sune:

Shan kwayoyin rage haihuwa wato contraceptive pills da samun juna biyu da tsayawar al’ada a mata idan sun manyanta ko tsayawarta kafin lokacin da ya dace ta tsaya. 

Meke Yawan Tayar Da Ciwan

Triggers ma’ana: Wasu nau’in abubuwa dake yawan sashi tashi.  

  • Daga ciki kwai ire-iren  abinci dakan tayar da ciwon wadanda su masu matsalar ya kamata su lura su guje musu saboda suna stimulating din ƙwaƙwalwa kamar masu halayyar cin tafarnuwa kullum,shan ruwan kanumfari kullum,shan coffee kullum
  • Sai kuma rashin samun isasshen hutu ko bacci,da yawan kallon screen walau na waya ko a Tv. 
  • Da yawan toshe kunnuwa da eyafis ko headphones na tsawon lokaci har ya zamo halayyar mutum. 
  • Yawan shiga halin matsi,damuwa,da kuma gabatowar haila
  • Yawan caccanza lokacin kwanciya bacci.
  • Zama da yunwa,aqi cin abinci musamman breakfast sai wajen 10 ko 11 na safe. 
  • Ko magungunan shaƙawa a hanci,ko amfani da irinsu cocaine. Duk an tabbatar suna sa saurin tashin ciwon.

Illar Yin Watsi DashiI

Likitoci na gargadi akan ya kamata mai ciwon ya rika ziyartar asibiti kada yake shan magungunan rage zogi a gida kurum ko kuwa yake barin sa har yaci ya saki,domin migraine na iya haddasa abunda ake kira migrainous infarction

Wato Migraine kan iya haddasa strokes wanda hakan kan jawo shanyewar barin jiki koda mutum baida hawan jini saboda fashewar magunar jinin ƙwaƙwalwa da ciwon yasa hakan ya zai haddasa mutuwar kwayoyin halittun ƙwaƙwalwa na gurin da abun ya faru.

Domin karanta da kiyaye Halayen Dake Haddasa Lalacewar Ƙoda [Kinney Dx] Danna nan 

Saboda sanda yake faruwa talewa jijiyoyin jini keyi tare da tsukewa cikin ƙarfi fiye da yadda ya dace,kamar yadda kake hura balloons abunda ake kira (Vaso-dilatation) kaga ba ƙwari in pressure tai yawa hujewa zafin jini sai jijiyar tayi asami matsala domin shi stroke ne hemorrhagic mesa jini ya fantsama wanda galibi yafi kisa nan take saɓanin ischemic. 

Matakin  Ɗauka

Kafin akai ga likita a iya shan paracetamol don asami relief amma kar azauna,saboda inka zauna kaita shan paracetamol to fa shima zai lalata maka hanta,cikin kwana 3 rabin hantarka na iya mutuwa,sannan a iya a sami ruwan dumi adaddana sashin kan wato ai tausa a sami guri mara hayaniya a ƙwanta a kuma kashe hasken dakin musamman in dare ne,mutum ya saki jiki ya samu yai relax,sai kuma a garzaya ga likita in gari ya waye. Allah ya sauwake.

Domin karanta Amfanin Shan Ruwa Da Safiya Kafin Aci Komai Danna nan

labarin da ya wuceAmfanin Shan Ruwa Da Safiya Kafin Aci Komai
Labarin na GabaBayani Akan Gyambon Baki {Canker Sore}