Aure shi ne ginshinƙin rayuwar mutane haɗi da yaɗuwar jinsin mutane, sannan kuma dukkanin mutanan da basa yin aure ko gari ko jiha ko ƙasa za ka same su da raunin tunani da hankali haɗi da rashin sanin ingantacciyar rayuwa. Aure yana da falaloli masu girma ga waɗanda suka yi shi a matsayin sunnar ma’aiki (Sallallahu alaihi wasallam) kuma suka kiyaye dokokin shi, ga kadan daga cikin su:
Manzon Allah (sallallahu alaihi wasallam) ya ce “Wanda ya yi aure, haƙiƙa ya kammala rabin addininsa, to ya ji tsoron Allah a sauran rabin” Wato ibadar da aka halicce ka don ka yi ta, idan ka yi aure, Allah SWT ya ba ka rabin ta kyauta.
Mu’azu bn Jabalin (R.A)wani Sahabin Manzo (Sallallahu alaihi wasallam) yace; “Sallar mai aure ta fi sallar marar aure sau arba’in”. Wato sai marar aure ya yi sallah sau arba’in sannan za ya yi daidai da sallar mai aure guda ɗaya.
Ibn Abbas (R.A) sahabin Annabi SAW, yace; “Ku yi aure, domin kwana guda da aure shi ne mafi alheri daga ibadar shekara dubu”. Waɗannan hadisan akwai su cikin Buguyatul Muslimina. Waɗanda ba su da aure, su yi ƙoƙari su yi aure kafin duniyar ta tashi.
Bukhari da Muslim su fitar da hadisi daga Ibn Mas’ud (R.A) ya ce: Manzon Allah s.a.w ya ce “Ya ku taron samari! Duk wanda ya sami iko daga cikinku; to ya yi aure, domin shi ya fi taimakawa wajen rintse gani, kuma shi ya fi taimakawa wajen kare farji. Wanda bai sami iko ba, to ya yi Azumi, domin Azumi garkuwa ne”.
Muslim ya fitar da wani hadisin daban daga Abu-Huraira (R.A) ya ce: Manzo s.a.w ya ce “Idan ɗayanku ya ga wani abin da ya burge shi a jikin wata mace, to ya koma zuwa ga iyalinsa, yin hakan zai mayar da abin da ke ransa na sha’awa”. Waɗannan hadisai biyu sun nuna zahirin falalar da ke cikin aure da kuma amfaninsa. Babbar falalar da ke cikin aure ita ce kare mutum daga faɗawa cikin saɓon Allah ta hanyar kallon haramun ko aikata laifin zina. Haka nan yana daga falalar yin aure akwai lada da Allah zai bai wa ma’aurata a duk lokacin da suka biya buƙatarsu ta saduwa.
Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) yana faɗa a cikin wani hadisi cewa “A cikin tsokar ɗayarku (wato, saduwa) akwai ladan sadaka”, sai wani Sahabi ya ce “Yanzu ɗayanmu ya biya sha’awarsa, sannan ya samu lada” sai Manzon Allah s.a.w ya ce “Shin idan ya sanya ta a haramun zai samu zunubi? (wato idan ya yi zina)? Sai ya ce “Ƙwarai!” Sai Manzon Allah s.a.w “To haka idan ya sanya ta a halal zai samu lada”.
Na daga cikin falalar yin aure; samun ladan ciyarwa, Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce “Ciyarwar ɗayanku ga iyalinsa ladan sadaka ne”. To kun ga waɗannan falaloli ba wanda zai samu sai wanda ya yi aure. Don haka na ke jan hankali samari da ‘yan mata da a zage damtse wajen yin aure domin riskar waɗannan falaloli.
Ubangiji ka bai wa gwauraye cikin maza da mata damar yin aure. Ya kuma sanya albarka cikin aurarrakin da aka yi da waɗanda za a yi. Ya Allah ka sa mu auri masu taƙawa da kwantar mana da hankali a duk lokacin da muke cikin wani hali sannan su zamto hanyar shigarmu aljanna ameen.
Don karanta alamomin shigar so danna nan
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu