Akwai wasu alamomi wanda mutum ya kamata ya yi la’akari da su, saboda su ne alamomin da zai iya gane cewa ya gamu da son ko soyayyar wani, waɗannan alamomin guda tara ko goma ga misalansu kamar haka: yawan kallo, yawan murmushi, yawan gaisuwa, yawan ambato, yawan faɗuwar gaba, yawan zolaya, yawan fara’a, yawan tunani, yawan magana, yawan kyauta.
1. Yawan kallo : da zarar wata ko wani yana yawan kallo wata ko wani kuma kallo mara ɗaukewa, ma’ana yana ƙura idanuwarsa a duk lokacin da suka haɗu da juna, domin ya samun damar kallace abinda ko ta samu damar kallon fararan idanuwansa haɗi da hamshaƙiyar fuskarsa.
Saboda haka za ka iya samun wasu mutanan suna zama akan hanyar wucewar abinda suke ƙauna, saboda su samu damar bai wa idanuwansu abinci, domin idan mutum ya tsunduma cikin kogin soyayyar wata ko ta faɗa cikin soyayya, to za ka iya samun idanuwarsu ya makance, sa’annan hankalin zuciyarsa ya tashi har sai sun haɗu da abinda yake ƙauna.
Saboda haka ne idan ka ga wani mutum yana kallon wani abu sama da kasa, sa’annan kuma ya ƙi kau da kansa har tsawon wani lokaci, to a nan ma akwai wani abu wanda yake shirin gudana a tsakaninsu, wanda kuma da zarar lokaci ya yi zai bayyana a fili.
Haka kuma matuƙar ka ga wani mutum yana yawan kallon wani ko wata haɗi da zama a kan hanyar wucewarta ko wucewarsa, to akwai wata magana a ƙasa.
Bugu da ƙari kuma idan ka ga wani mutum yana kallon wani ko wata har hankalinsa ko hankalinta ya shuɗe, ma’ana tunaninta ko tunaninsa ya tafi zuwa abinda yake kallo, wato da wani abu zai zo ya gifta ta gabansa ko ta gabanta ba za ta iya tantance lokacin da ya wuce ba.
Saboda abinda yake kallo ya ɗauke masa hankali, to a nan ma akwai abubuwa guda biyu waɗanda suke shirin faruwa, ko dai abinda yake kallo ne ya ɗauke masa hankali ko mamaki. Saboda ganin faruwar abin, ko abinda yake kallo ne ya burge shi, idan ko abinda yake kallo ya burge shi, to a nan ma akwai abinda yake shirin faruwa nan gaba, matuƙar hakan ya cigaba da faruwa.
Saboda haka yana da matuƙar amfani ga ma’aurata tun a farko ma su tabbatar shin irin wannan sun taɓa faruwa a tsakaninsu, saboda shi ne mataki na farko na tsundumawa cikin kogin soyayya. Allah ya sa mu dace don alfarman annabin mu.
2. Yawan murmushi: yawan murmushi ko shagwaɓa yana ɗaya daga cikin alamomin shigar so, saboda duk mutumin da ka ga da zarar kun haɗu da shi, sai ya tarbe ka da wani sutalelan murmushi mai kawar da ɓacin rai, to akwai magan-ganu a ƙasa, da zarar ka cigaba da bibiyar al’amarin za ka gano haka. Saboda haka kawai babu wata ko wani da zai jefa ka cikin kogin nishaɗi haka kawai ba tare da wani dalili ba.
Saboda haka da zarar ka ga wata mace a duk inda kuka haɗu da ita, sai ta yi ma wani irin murmushi wanda yake tafe da nishaɗantarwa ko wani abu da wanda yake nuna alamar nishaɗi, to akwai abin dubawa a nan.Saboda ba zai taɓa faruwa ba a ce mace ta aikata haka ba tare da wani dalili ba. Idan mutum ya bi al-amarin a hankali zai ga abinda zai faru nan gaba.
Haka kuma ya kamata ma’aurata su fahimci cewa yawan murmushi yana ɗaya daga cikin alamomin madarar tantagaryar ƙauna, saboda haka kawai, ba zai taɓa faru ba a ce mutum da zarar kun haɗu da shi ya jefa ma wani hamshaƙin murmushi ko fara’ah mai nishaɗantarwa haka kawai, ba zai taɓa kasancewa ba, idan kuma ya kasance to a saurari abinda zai faru nan gaba.
Bugu da ƙari kuma murmushi da fara’ah ba sa iya faruwa a tsakanin jinsi guda biyu haka kawai ba tare da wani dalili ba, amma kuma ya kamata mutum ya iya banbance irin murmushin da aka yi masa. Saboda akwai murmushi ko fara’ah na kunyatarwa, ma’ana akwai murmushi da mutum zai yi ma don wulaƙantarwa, saboda ya aikata abinda bai dace ba ko abu mara kyau, ka ga wannan ba za iya haɗa da shi murmushi na so ba.
3. Yawan gaisuwa: da zarar wani ko wasu jinsi suna yawan gaisawa da juna sa’annan kuma ba su da wata alaƙa da juna, to akwai wani lamari wanda yake shirin faruwa a tsakaninsu, saboda haka kawai mace ba za ta dinga gaishe da wani namiji ba haka kawai ba tare da wani dalili ba. Saboda a duk inda ‘ya mace take an santa da kunya haɗii da kamun kai matuƙar musulma ce ta gari.
Haka kuma ita kanta gaisuwa tana ƙara sa shaƙuwa da fahimtar juna a tsakanin jinsi guda biyu, saboda duk wanda yake gaishe da kai, to yana ganin girman ka ne haɗi da daraja a wajansa. Saboda haka duk mutumin da yake yawan gaishe da kai ko miƙo maka gaisuwa safe da maraice, gida da waje, to akwai alamar amincewa a tsakaninku ko fahimtar juna haɗi da jituwa a tsakaninku.
Sa’annan kuma duk mutumin da kuke yawan haɗuwa da shi, sai ya duinga gaishe da kai, musammamma tsakanin jinsi namij da mace, to tana ganin darajarka ko tana buƙatar sauraran sautin muryarka. Saboda haka za ka iya fahimtar haka da zarar kun haɗu da juna ta hanyoyi da dama kamar su yawan gaisuwa ko murmushi ko kallo da dai sauransu.
4. Yawan ambato: yawan magana ko ambaton sunan mutum yana iya nuna alamar cewa kana ƙaunar wani mutum, saboda haka yawan magana akan wani mutum kuma mai daɗin sauraro yana iya nuna alamar so.
Saboda haka da zarar wani mutum yana yawan faɗar sunan wata ko wani a lokuta mabambanta, to yana nuna alamar cewa yana ƙaunarta, matuƙar faɗar sunansa da yake yi ambato ne kyakykyawa. Sa’annan kuma alamar ambato ko magana yana ɗaya daga cikin alamomin so. Saboda duk abinda mutum yake so a cikin zuciyarsa, zai dinga yawan ambatonsa ko bayyana shi, ma’ana zai dinga ambaton sunanta ko sunansa a cikin zuciya ta hanyoyi da dama.
Haka kuma duk mutumin da yake yawan magana akan wani al’amarin ɗayan biyu ne zai faru, ko dai abin yana yawan damunsa, saboda munin halinsa ko halayenta, ma’ana saboda mummunan halayensa ko halayenta yasa shi yake yawan ambatonta ko ambatonsa. Ka ga wannan ba za ka haɗa shi da alamar shigar so ba. Amma kuma idan yana ambaton ta ne saboda kyakykyawan halayenta ko halayensa, to ka ga a nan kuma, akwai wata magana a ƙasa a tsakaninsu, matuƙar haka ya cigaba da faruwa a tsakaninsu.
Bugu da ƙari kuma kamar yadda muka ce alamar so shi ne yawan ambato, saboda haka ne ma yasa a duk inda musulmai suke za ka iya samun suna yawan ambaton sunan Allah da manzon Allah, saboda me suke yawan ambaton sunayansu? Amsa saboda yawan so da suke yi musu.
Saboda haka za ka gansu suna yawan ambaton annabi muhammad (sallallahu alaihi wasallam) dare da rana, gida ko a kasuwa, a waƙe ko a zube da dai sauransu. Haka kuma duk mutumin da yake waƙe wata mace ko duk macen da take waƙe wani namiji, to akwai alamomin so wanda yake shirin faruwa nan gaba, matuƙar haka ya cigaba da faruwa.
5. Yawan faɗuwar gaba: duk mutumin da ya ji gabansa yana yawan faɗuwa, saboda haɗuwa da wani namiji ko wata mace, to akwai abinda yake shirin faruwa a tsakanin su, matuƙar haka ya cigaba da kasancewa a tsakanin su.
Lamarin da zai iya faruwa da shi kuwa shi ne ko dai don ganin masoyiyarsa ne ko masoyinta ne ya sa gabansu yake yawan faɗuwa ko abinda suke ƙauna, saboda haka akwai kyakykyawan alaƙa a tsakanin su mai danƙo. Wasu kuma mutanan da irin wannan alamar suke iya ganewa sun kusa haɗuwa da juna, ma’ana da zarar ya ji ko ta ji gabanta yana yawan bugawa ko faɗuwa za ta ko zai fahimci ya kusa haɗuwa da abinda yake ƙauna akan wannan hanyarsa.
Lamari na biyu shi ne akwai wani abu mara kyau ko abinda yake jin tsoronsa zai haɗu da shi akan hanyarsa ko yana kusa da shi, idan haka ya faru, sai mutum ya roƙi Allah ya kare shi daga wannan al’amari mara kyau wanda yake shirin faruwa da shi.
Saboda haka idan jinin mutum ya haɗu da wani mutum ko sun ɗan samu shaƙuwa sosai a rayuwarsu ta yau da kullum, da zarar wani abu mara kyau ya faru da ɗaya daga cikinsu zai ji alamar haka a jikinsa. Saboda zai ji gabaki ɗaya jikinsa babu ƙarfi ko wani ɓari a jikinsa yana yi masa ciwo haka kawai ba tare da wani dalili ba.
Misali idan mace mai shayarwa ta ajiye ɗanta ko ta kwantar da shi, da zarar ya farka daga bacci ko yana kuka za ta iya fahimtar haka a jikinta, saboda za ta ji ƙofofin nononta sun buɗe sa’annan kuma yana zuba ko ɗiga a jikinta, saboda irin shaƙuwar da take a tsakanin su hakan ke iya faruwa.
Misali na biyu idan wani abu ya faru da wani daga cikin ‘yan uwanka ko iyayenka mara kyau za ka iya fahimtar haka a tare da kai kamar yadda muka yi bayani a baya. Saboda haka matuƙar akwai shaƙuwa a tsakanin mutane guda biyu, to idan wani abu ya faru da wani zai iya fahimtar haka a tare da shi.
Misali idan wani mutum ya yi kiciɓir da abinda yake so ko ƙauna akan hanyarsa ta tafiya, to dole ne sai ya ji wani abu a cikin zuciyarsa ko gabansa yana harbawa.
6. Yawan zolaya : yawan wasa da dariya a tsakanin jinsi guda biyu namiji da namiji ko mace da mace ko a tsakanin namiji da mace hakan ke faruwa, to akwai alamar amincewa da juna haɗi da fahimtar juna a nan.
Saboda haka duk wanda ya ga wani mutum yana yawan zolayarsa da wasanni daban daban, matuƙar yana hankaɗa shi cikin tafkin nishaɗi wanda yake tafiyar da ɓacin rai ko baƙin ciki, sa’annan kuma shi yana jin daɗin haka, to akwai alamomin shigar soyayya a tsakanin su. Haka kuma ya kamata mutane su fahimci cewa yawan aikata haka yana ɗaya daga cikin alamomin shigar soyayya, kamar yadda muka yi bayani a baya.
Amma kuma idan mutum yana zolayan wani mutum da isgili ko wulaƙantarwa, ma’ana yana faɗa masa munanan kalmomi a cikan zolayansa, ka ga wannan mutum ba zai ce alamar shigar so ba ne, idan kuma mutum yace ai wannan ma alamomin shigar so ne ko wance tana ƙauna ta, yin haka kuskure ne. Saboda ba shi da alaƙa da irin wanda muka yi bayani a baya ko alamomin shigar so.
Tabbas ko haƙiƙa yawan zolaye ko wasa da dariya a tsakanin namiji da mace yana nuna alamar amincewa da juna, matuƙar akwai annushuwa a lokacin da suke zolayan junansu.
Misali wani namiji yana tsokanar wata mace da kalmomi daɗaɗa ko masu kyau har ita kanta tana jin daɗin waɗannan kalmomin da yake faɗa mata a cikin zuciyarta, to akwai alamar amincewa a tsakanin su.
Amma kuma ba duk kowane zolaya ba ne yake nuna alamar so, saboda akwai mutanan da suke abokanan juna ko abokanan wasa da juna, ma’ana waɗanda suke ‘yan uwan juna ko da namiji da ‘ya mace, sa’annan kuma akwai wasa ko zolaya a tsakanin malami da ɗalibansa ko ɗalibi da ɗaliba da dai sauransu.
Saboda haka ka ga waɗannan ba za ka iya haɗa su da alamomin so ba, ko da yake ta wata fuskar akwai alamar haka, amma dai ba irin wanda muke magana ba ne a kai ba. Saboda haka shi ma wannan yana da fannoni da yawa ko zurfi, sai mutum ya yi tunani sosai kafin ya yanke shawarar irin son da ake yi masa, Allah ya sa mu dace.
7. Yawan fara’a : yawan fara’a yana iya zama ɗaya daga cikin alamomin shigar so, ma’ana yawan sauraran zantukan ka ko zantukan ki, saboda za ka iya samun wani mutum duk abinda yake yi da zarar ya ji maganar abinda yake so ko ƙauna ko kuma ya ji wani mutum ya ambaci sunanta ko sunansa, sai ta yi wata fara’ah ko murmushi, to idan haka tana faruwa a tsakaninsu akwai alamar shigar so a nan.
Saboda haka duk mutumin da suke haɗuwa da shi ko kuke mu’amala da shi, sai ka ga a duk inda kuka haɗu da shi, sai ya jefo ma wata hamshaƙiyar fara’a, ma’ana fuskarsa cike take da wani annuri hadi da wasa da dariya ,to akwai alamar zaman lafiya a tsakaninsu ko alamar shigar so.
Saboda dole ne mutum sai yayi la’akari sosai zai iya gano haka, misali, idan saurayin mutum kuma matashi mai jini a jika haɗi da halaye masu kyau sosai, sai wata mace ko idan suka haɗu da wata mace sai ta dinga nuna masa fara’arta haɗi da farin cikinta a gare shi, ka ga akwai alamar tambaya a nan.
Amma da hakan za ta iya kasancewa a tsakanin wasu jinsi ko mutane guda biyu, to mutum ba zai iya saurin yanke hukunci ba, saboda dole sai ya binciki tsakaninsu babu wata alaƙa a tsakaninsu,kamar yadda muka yi bayani a baya. Bugu da ƙari kuma dukkanin mutane sun tabbatar cewa fara’ah tana ɗaya daga cikin halaye masu kyau, saboda haka kuma tana nuna alamar amincewa da juna ko soyyaya a tsakanin mutane da dai sauran su.
Haka kuma ita fara’a ba ta fita haka kawai, face sai da wani dalili na aikata haka ko faruwan haka, sa’annan faraa tafe take da alkhairi, saboda za ta iya kau da dukkanin ɓacin rai a jikin mutum, saboda haka za a iya cewa duk wanda yake yi ma yawan fara’a, to akwai alamomin tambaya shi ma a nan.
Sa’annan kuma akwai wasu mutane waɗanda a haka suke, ma’ana haka halayensu yake, a duk inda suka haɗu da mutum sai sun yi masa fara’a ko wasa da dariya, amma kuma hakan ba zai iya kasancewa akan kowane mutum ba. Saboda haka ko da ma halayensu ne yin haka ko aikata haka, ya kamata mutum yayi la`akari sosai da idan haka tana faruwa da shi,idan ma akwai wani abu boyayye zai fahimci haka,matukar ya yi la’akari sosai a lokacin da hakan take faruwa ko ya fahimci waɗannan bayanai na mu waɗanda muka yo bayaninsu a cikin wannan babi.
8. Yawan tunani : matuƙar wani jinsi yana yawan tujnanin wani jinsi, to akwai alamar shigar so a nan, sai dai abinda ya kamata mutum yayi la’akari da shi, shin akwai wata alaƙa a tsakaninsu, ma’ana dangartakar da su ke da juna. Saboda dole ne ɗa na gari mai cikakken hankali ya dinga tunawa da waɗanda suka yi masa halacci, ma’ana iyayensa haɗi da ‘yan uwansa baki ɗaya, ko da yake ita ma wannan alama ce ta shigar so amma ba wanda muke magana a kai ba, saboda shi so ya kasu fanni-fanni da yawa na rayuwa.
Misali akwai so na halaye ko na ɗabi’u, akwai so na kuɗi, sa’annan akwai na ilimi, jarumta, kyau (jiki ko fata) da dai sauransu. Saboda haka wani saboda kyawawan halayen wani ne yake yawan tunawa da shi, misali wani mutum mai yawan haƙuri da tausayi ga mutane, da zarar ya ga wani abu mara kyau ya samu mutum, sai ya tausaya masa haɗi da nuna alhininsa akan faruwar wannan al’amarin, shi yasa yake yawan tunawa da shi ko sun yi mu’amala da shi cikin lumana, shi yasa yake yawan tunawa da shi ko ita, ka ga ba za ka iya haɗa shi da alamar da muke magana a kai ba, amma shi ma dai alamar so ne.
Saboda haka ne ma yasa mu musulmai mu ke yawan tunawa da annabi Muhammad (sallallahu alaihi wasallam) da matayansa da sahabbansa haɗi da bayin Allah na gari waɗanda suka rasu, domin a yi koyi da halayensu, saboda haka duk wani dalili da yake sa a so mutum annabi Muhammad yana da su, shi ya sa muke yawan tunawa da shi safe da rana.
Saboda waɗannan dalili duk wanda ya ji a cikin zuciyarsa sai ya ga yana yawan tunawa da shi, to idan haka tana faruwa akwai wani lamari a tsakaninsu wanda yake shirin faruwa.
Bugu da ƙari kuma duk wanda yake yawan mafarki da wani mutum, sa’annan kuma mafarki mai kyau, to shi ma akwai magana a ƙasa a tsakanin su, saboda yawan tunawa da abinda mutum yake so yana iya sa wa mutum ya yi ido biyu da shi a cikin mafarkinsa.
Sa’annan kuma yawan tunawa da wani al’amari a cikin zuciya, ma’ana idan wani mutum yana san wani abu a rayuwarsa, to yake yawan tunawa da shi a cikin zuciyarsa, to akwai alamar wani abu a ƙasa a tsakaninsu. Misali, ka lura sosai ka gani a cikin misalan mutane daban-daban za ka iya gane hakan, saboda shi tunani yana tafe ne da abubuwa guda biyu so ko kiyayya.
Saboda idan wani mutum yana yawan tunawa da wani mutum, saboda yana ƙaunarsa ko sunyi mu’amala mai kyau a tsakaninsu, amma kuma wani mutum yana tunawa ne da wani mutum saboda rashin mutunci da ya yi masa ko wani abu wanda bai ji daɗin faruwar sa ba.
Saboda haka shi ma sai mutum ya yi tunani a kai kafin ya yanke hukunci akan wannan al’amarin.
9. Yawan magana : duk wanda yake yawan yi ma magana akan wani ko wata, to akwai alamar shigar so a nan, saboda ba zai taɓa faruwa ba ko kasancewa ba haka kawai wani mutum ya dinga yin magana akan wata mace ko wani namij haka kawai ba tare da wani dalili ba, dalilin kuwa shi ne so ko ƙiyayya, kamar yadda muka yi bayaninsu a baya.
10. Yawan kyauta : yawan kyauta na ɗaya daga cikin alamomin shigar so, saboda duk maƙiyin ka ba zai taɓa ba ka kyauta ba, saboda ita kyauta tana ƙara danƙon ƙauna, musamman ma a tsakanin masoya. Saboda haka duk wanda yake yawan yin kyauta ga wani mutum haka kawai babu wata alaƙa a tsakanin su ko kuma ma akwai alaƙa a tsakanin su, to akwai alamar yarda da amincewa haɗi da ƙauna a tsakanin su.
Sa’annan kuma ana iya ba mutum kyauta don halayensa masu kyau ko iliminsa ko kyansa da dai sauransu, amma kuma su ma suna nuna alamar ƙauna, amma kuma akwai kyauta a tsakanin malami da ɗalibai ka ga wannan yana da bambanci da wancan, amma ta wata fuskar akwai alamomin tambaya a nan, da dai sauransu.
Haka kuma duk wanda yake yawan magana ko siffanta wani namiji ko wata mace ko yawan faɗar sunansa ko sunanta haka kawai shi ma ba tare da wani dalili ba wanda yake nuna alamar haka, to akwai alamar shigar so. Bugu ga ƙari kuma duk waɗannan abubuwan da muka yi bayaninsu a cikin wannan babi suna da kishiyoyi, saboda haka dole ne sai mutum ya yi bincike sosai akan su haɗi da yadda suke gudana a tsakaninsu, domin gane gaskiyar lamari. Allah ya sa mu dace don alfarman annabi Muhammad (sallallahu alaihi wasallam ).
Don karanta yadda za ki sa mijimki ya ƙara son ki danna nan
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu