Alamomin Shigar So 1

0
41

TSAKURE
So wata tsoka ce ko jijiya ce a cikin zuciya wanda Allah yake halittar bayinsa ko ɗan Adam da ita, don haka so wata ƙaramar tsoka ce wadda kowane ɗan Adam yake da ita, sa’annan shi so ba a ganin sa saboda sirri ne wanda Allah ya ɓoye a zuciyar kowane mutum sai dai kawai alamunsa ne za ka iya ganewa da zarar wani ko wata ta kamu da son wani, saboda haka shi so daga ƙarami yake farawa sai ya ci gaba da girma da faɗaɗa saboda yawan tunanin abin da kake so ko kike so.

Alamomin shigar so
Marubuta da mawaƙa haɗi da mutanan gari sun taimaka wajen bincike akan so, amma har yanzu binciken su bai gama cika ba, saboda sun ce wai so makaho ne, sa’annan kuma wai ba ya ji ba ya gani. To ni a ɗan bincike na, na gano cewa so ba makaho ba ne, hasali ma yana da ido yana da ƙafa, kamar yadda za mu yi bayanin sa a cikin wannan littafin.

Amma kuma kafin mu yi bayani akan wannan darasi, za mu leƙa hanyoyin sanar da mace irin ƙaunar da mutum yake yi mata amma fa ba ta hanyar magana ba kamar haka: su yawan tambaya, jan aji ga namiji da mace, hidima, hakuri,iya kalaman soyayya, gaskiya, rarrashi da dai sauran su:-

Farkon haduwarku: yanzu lokaci ya canza an daina furtawa ‘yan mata kalmar so a haɗuwar farko, lallai ne idan kana so ka samu karɓuwa wajen mace, to ka samu wata hanya wadda za ku dinga haduwa kuna hira. A cikin hirar kada ka kuskura ka nuna mata alamomin so, ka ƙyale ta zuwa gaba za ta sani. Ka yi ƙoƙarin saka ta dariya a lokacin da kuke tare.

Idan kuka fara shaƙuwa ka ringa nuna mata duk duniya ba ka ga macen da ta tsaru ba kamar ta, amma kada ka zaƙe a wannan fannin. Sannu a hankali sai ka fara aika mata sakon wasiƙa ta ido kuma zuwa lokacin ka ɗan ringa tambayar ta cewa, wai waye mai tsananin sa’a ne ya mallaki zuciyar wannan tsadaddiyar yarinyar ? Idan har ta basar da zancen, to fa ka ci gari ko kuma ta ce ma wani ne kuma ta ƙi faɗa maka sunansa to kai ɗin take nufi.

Akwai wasu halaye da ya kamata ka daina lokacin da za ka je wajen mace, domin neman soyayyar ta da kuma lokacin da ka zama wanda take so. Halayen su ne kamar haka:
1. Yawan tambaya:-mai yawan halayya na tambaya yakan saurin fita daga zuciyar mace.
2. Hidima:-ka sani dole ne ka ɗan yi wa wacce kake so hidima ko da kuwa ba auren ta za ka yi ba, domin kuwa mata ba su son marowacin saurayi.

3. Jan aji ga namiji:-idan ka tabbata ka zama wanda take so sosai, to kai ma sai ka ɗan ja naka ajin. kamar ka daina bari kuna haɗuwa kodayaushe, domin ko abinci ne kake cin shi kullum to sai ya ishe ka, ita ma mace ai haka take.

4. Iya kalamai na so:-yana da kyau ƙwarai ka zama gwani wajen furta kalaman so, su ma suna taka muhimmiyar rawa, ka zama mai matuƙar tsafta, dan kuwa kamar yadda kake ganin ‘yan mata idan sun ɗau wanka ka ji sun birge ka, haka su ma matan kalar waɗannan samarin ke birge su.

A gaskiya sace zucciyar mace abu ne mai sauƙi ga wanda ya gane, sannan kuma abu ne mai wuya ga wanda bai gane ba. Tabbas idan dai har kana so ka yi wa mace satar zuciya, to dole ne sai ka bi dokoki kamar haka:

5. Jan aji ga mace: ka sani fa mace ba za ta iya mallaka maka kanta hakan nan kawai ba, dole ne sai ta ja maka aji dan ta gane halayenka da haƙurinka sannan kuma za ta so ta gane ko da gaske ne kake sonta ko ba da gaske ba ne. Saboda mata sun tsani duk wani saurayin da ke shirin yaudararsu, idan har ka ga ka zo wa mace kai tsaye ta amince da kai ba tare da jan aji ba, to fa ka tsoraci lamarinta domin mace idan har cikakkiyar kuma gogaggiyar mace ce to za ta ja maka aji sosai har sai ka kusan yin kuka tukunna.

6. Haƙuri:- tabbas dole ne sai ka zama mai haƙuri, idan ba haka ba to ba za ka samu damar lashe jarabawar da mace za ta yi maka ba, saboda za ka ga ababe da dama masu gasa zuciya, idan har ba ka zamo mai haƙuri ba, to kai da yin soyayya da mace sai dai a hankali.

7. Gaskiya:- mace ta fi son saurayin da ke gaya mata gaskiya kai tsaye, idan har kai maƙaryaci ne to ina mai tabbatar ma da cewa idan har ta zo ta gane sirrinka za ka sha kashi, domin haka ake kwatanta gaskiya dai-dai gwargwado.
8. Kulawa: dole ne idan dai har kana son zaman ka da mace ya ɗauki tsawon lokaci kuma ya sa ta soka sosai fiye da kima, to lallai kuwa dole ne sai ka kula da ita tamkar yanda za ka kula da kanka a lokacin da kake cikin rashin lafiya. Kulawa yana ɗaya daga cikin siffofin abin da mata suke so.

9. Rarrashi tare da girmamawa: mace ta fi so idan har ka san ya ta yi fushi to ka rarrashe ta tamkar yanda za ka rarrashi jaririya. Kuma mace za ta ji daɗi sosai fiye da kima idan dai har kana girmamata, ta fannin yabon halayenta na kirki tare da nuna mata cewa babu wanda ka fi so a duniya tamkar ita saboda tana da halin kirki.

Akwai wasu halayyar da mace idan kana mata su, to ba za ta taɓa mantawa da kai ba. Duk namijin mai waɗannan halayya zai yi wuya mace ta manta da shi ko da kuwa sun rabu. Waɗannan halayya dai su ne kamar haka:

1. Namiji wanda ya san kimar mace da kuma darajar ta.
2. Namiji da yake yabon mace da ririta ta da ɗaukar ta da mahimmanci.
3. Namiji mai riƙon amana wanda ba ya juyawa matarsa baya.
4. Namiji da yake ba wa mace cikakken lokaci, domin sauraron ta da jin ra’ayin ta.

5. Namiji mai kyauta.
6. Namijin da yake ba wa mace haƙuri kuma ya lallashe ta idan ya ɓata mata rai ko kuma lokacin da ta shiga wata damuwa.
7. Namiji da ya tseratar da mace daga wani haɗari da ta fuskanta a rayuwa.

8. Namijin da mace ta san zai iya mutuwa saboda ita.
9. Namiji mai fara’a da murmushi da sakin fuska da kuma tafiye-tafiye da mace.

10. Namiji mai tsafta da kwalliya da lafiyar jiki musamman wajen biyan buƙatar iyali.

Domin Karanta yadda ake yi wa megida a lokacin fushi danna nan

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceAbin Da Zai Faru Gobe
Labarin na GabaAlamomin Shigar So 2