1.Kyakkyawan yanayi
Bincike ya nuna ma’auratan da suke sabunta yanayin rayuwarsu ta yau da gobe sun fi samun zaman lafiya. Misali zuwa sabbin gurare, cin abinci na musamman ko fita kallon wani abun tsoro ne ko na nishaɗi tare. Motsa jiki ko wasanni tare ziyartar wani guri da ba su taɓa zuwa ba.
2.Shafar juna
Ku kasance kuna iya kusantar junanku a kodayaushe ba wai sai lokacin kwanciya ba. Kina iya shafar wuyan mijinki idan yana miki girki. Ko shafar gashin kansa a lokacin da kuke zaune kuna kallo. Riƙe hannun juna idan kuna tafiya tare. Sumbantar kuncinsa a ba-zata. Ko shafar bayansa a lokacin da yake wani yanayi mara daɗi.
Domin karanta Yadda Za Ki San Kanki Kafin Ki Yi Aure Danna nan
3.Tattaunawa Game da kwanciyar aure
Yana da kyau kuna canza yanayin salon kwanciyarku ko tattaunawa game da abunda yake sa ku jin daɗin kwanciyar ko wani abu da yake so kina masa da zai sa ya ji daɗi misali: Chanza salon kwanciya ko ku je ɗakin hotel. Idan Kuna da yara ku ba da su inda za a kula da su don ku samu isasshen lokaci
- Yi wa juna tausa.
- Sabunta kayan bacci.
- Samun ingantacciyar kwanciya da gamsuwa ba wai yawan kwanciyar ba.
- Sumbatar mijinki tana da tasiri ƙwarai wajen ƙara danƙon ƙauna tsakaninku.
- kuma yana sa wa ki janyo hankalinsa gareki. Ki yi ƙoƙari kina sumbatar mijinki ko da na tsawon sakan 10 ne a rana.
Domin karanta Abubuwa Da Ya Kamata Mace Ta Kiyaye Lokacin Al’ada Danna nan