Yadda Ake Tafiyar Soyayya

0
2450

 


Yadda ake tafiyar soyayya shine ka yi kyakkyawan shiri don tarairaya, Kulawa ,da shagwaba Amarya. Ita Wannan tafiya ana yinta na kwanaki ko wuni guda. A tafi wani waje na Musamman. Wanda ya ke Dausayi ne. Akwai shuke-shuke, ruwa, dabbobi, kayatattun gine-gine da dai Sauransu.
Wasu na Tafiyar soyayya da masoya ke yi don nuna soyayya ga juna kwanakin farko da tarewarsu.

A wannan tafiya zasu tsara rayuwar aurensu gaba daya.

Ammafa ba sai sabon aure ba. Wannan tafiya na da muhimmacin gaske ga Tsofaffin ma’aurata. Sai akai yara gidan kakanninsu su zauna .Ko kakarsu ta zo ta zauna da su kafin ku dawo.

Ga tsoffin Ma’aurata ita ce kebantacciyar tafiya da wadanda suka yi auren soyayya ke yi don samun kebewa, sakewa, Nishadi da jin dadi.

A irin wannan tafiya ne za su sami damar gyara soyayya, duk yar wata rashin jituwa, ko kura kuren da aka yiwa juna. Wato tafiya ce ta sabunta soyayyya.

Ga wanda ba su da lokacin yin kwanaki. To sai su dinga tattalin ranakun hutun aiki (weekends) .Wajen Yini cur a wuraren shaqatawa. Ko da kuwa lambu, gidan Dabbobi (zoo), ko Minjibir park Kano .

MATAKAI NA TAFIYAR SOYAYYA.

1- Na farko ya zama akwai kyakkyawar niyya ta karfafa soyayya .

2- A tattauna tare Ango da Amarya. Ko Maigida da Uwargida kan zabar Lokaci da wurin da za’a je.

3- Ango/Maigida ya yi aski. Ya zabi kayan ado ma su kyau, da turare Don mallake zuciyar Masoyiyarsa.

4- Amarya/Uwargida ta yi gyaran jiki, kunshi, da gyaran gashi. Ta dauki turare da humra.

5- Ango/ Maigida zai tanadi kudi wadatattu. Don biyan dakin kwana, abinci, kayan marmari da zuwa wuraren ziyara.

6- Inda hali ana iya tanadarwa juna Kyautar bazata.

7- Ma’aurata su saki ransu. Cin abinci, wanka, tsere, rawa da wasanni tare.

  1. Bashakka duk Ma’aurata da ke irin Wannan tafiyar soyayya . Su Ka bi wadannan matakai na yadda ake tafiyar soyayya . Za ka ga rayuwarsu na cike da tsantsar soyayya da Begen juna.
    Zaka iya danna wanna koren rubutun nan domin sanin yadda ake gyara soyayya.

BAR AMSA

Please enter your comment!
Please enter your name here