Wannan Ita Ce Mace Tagari

0
1860

Gidan miji masarauta ce ga mace, shi yasa mace tagari ke sarrafa dukkan abin da ta mallaka na ilmi, hankali, wayewa da ƙwarewar rayuwa, ba domin komai ba, sai don ganin ta mayar da masarautarta aljannar duniya wajen kwanciyar hankali, more rayuwa da cikakkiyar nutsuwa ga uban ‘ya’yanta.

  1. Mace tagari ita ce wacce ta yi fice da ƙwarewa tare da yauƙaƙa soyayyarta wajen inganta bangorori 15 kamar haka:
  • Iya kwalliya
  • Girki, tarba
  • Murmushi
  • Magana
  • Kallo
  • Rakiya
  • Kwanciya
  • Hira
  • Tafiya
  • Raha
  • Rarrashi
  • Da kwantar da hankali.

2. Mace tagari a matakin farko tana kusantar mijinta ne domin ta fahimci ɗabi’u, halaye        da buƙatunsa, domin ta san yadda za ta zauna da abinta.

3. Mace tagari babban burinta cika siffofin da Manzon Allah Sallallahu alaihi wa sallam ya        siffanta mace tagari da su. “Khairu nisaa’ikum allatiy izaa nazara ilaiha zaujaha        sarrathu, wa in amaraha adaa’athu, wa izaa ghaaba anha hafizathu fi nafsiha        wa maalihi’’4

4. Mace tagari tana zaman aure ne domin samun yardar Allah Jalla wa Alaa, lazimtar            addu’o’i da kyautata ladubban tarbiyya ta addinin Musulunci a gidanta da ‘ya’yanta, ta       na kiyaye ibadu da kamanta tsoron Allah jalla wa Alaa a dukkan al’amuranta.

5. Mace tagari tana fifita ilmi fiye da komai na rayuwarta, tana mayar da hankali a kan            kyakkyawar rayuwar ilmi a cikin gidanta da yaranta domin samun albarka da hasken          rayuwa.

RUFEWA

Kiyaye ladubban zamantakewar aure shi zai bai wa auren armashi da sakamako mafi inganci, wanda wannan sakamakon shi zai sanya al’umma ta zama a kan saiti da ci gaba wanda akasin haka zai jefa al’umma cikin mummunar makoma. Allah Jalla wa Alaa ya kiyaye. Dr. Muhammad Sani Umar yana cewa:

“Masu miyagun tunani sun ɗago kai, suna aiki dare da rana, domin ganin cewa sun rushe ginin wannan al’umma wanda farkon tubalinsa an gina shi ne daga gida.

Idan miji da mata suka sami haɗa kansu bisa turba ta Musulunci, to sai ka samu ‘ya’yansu sun taso cikin kyakkyawar tarbiyya, To amma da zarar aka samu kishiyar haka, wato miji da mata suka gina rayuwa ba a kan turba ba, to lamarin ‘ya’yansu ba zai yi kyau ba”.

Rabbana hab lana min azwaajina wa zurriyyatina qurrata a’ayunin waj’alna lil muttaqina imaama. Wa antal musta’aan wa alaikal balaagh wala haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem. Wa sallallahu wa sallam alaa nabiyyina Muhammad wa aalihi wa sahb ihi ajma’in.

Subhanakallahumma wa  bihamdika asshahadu an laa ilaha illa anta astaghfiruka wa atuubu ilaika.

karanta yadda za ki mayar da gidanki masarautarki  ko ladubban tarewa a gidan miji ko Muhimmancin Aure a rayuwa domin sauke cikakken littafin ladubban zamantakewar aure danna koren rubutu

labarin da ya wuceMuhimmancin Aure A Rayuwa
Labarin na GabaWannan Shi Ne Miji Nagari