Tsarin Allah Ne Kishiya Ta Fi Kishiya

0
26

Daga cikin tsare-tsaren Allah a kan bayinSa, don akwai tsarin fifita wani a kan wani, don haka babu wata kishiya da za ta yi dadai da kishiyarta a halitta da kyan ɗabi’u. 

A sakamakon haka, so da ƙaunar da miji yake yi wa matansa ba zai taɓa zama daidai ba. Duba da haka ne ma Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce: 

“Ba za ku sami ikon yin (cikakken) adalci ba a tsakanin matanku; ko da kuwa kuna da kwaɗayin yin hakan, saboda haka, kada ku karkata gaba ɗayan karkata (ga ɗayarsu), to sai ku bar ɗayar kamar ratayayya (wato babu kulawa)”. (Suratun Nisa’i, aya ta 192). 

Da wannan ne Allah ya haramta wa magidanta yin watsi da ɗaya daga cikin matansu, don ba ta yi daidai da abokiyar zamanta ba. 

Sannan kuma an wajabta wa maigidanta yin adalci gwargwadon ikonsa cikin abubuwan da aka tilasta musu yi ga matansu; irin su ciyarwa, tufatarwa, rabon kwana, samar da makwanci, da kuma kyautata halayyar cuɗanya da su, da kula da sha’anin addininsu. 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

Ya ‘yar’uwa mai kyawun halitta! Kar ganin kina da kyawun halitta ki ringa ji-ji-da-kai ga miji, sai jiji-da-kanki ya hana shi ganin kyawun halittarki. 

Sannan kuma kada kyawun ɗabi’unki ya sa ki sakaci da kula da tsaftar jikinki da suturarki da matsugunanki, sai ƙazantarki ta disashe kyawun ɗabi’unki. 

Idan kishiyarki ta tsaya da ƙoƙarin kyautata halittar jikinta da ɗabi’unta don faranta wa miji, to ke ma ki jajirce ki faranta masa rai da abin da za ki iya yi na gyaran jiki da halayyar ƙwarai. 

Ƙauyanci ne da sunan kishi yake sanya kishiya kushe da hassada, faɗa da baƙaƙen maganganu ga kishiyar da ta yin abubuwan da suke faranta ran miji.

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

Kuma kuskure ne kishiya ta ɗauki matakin ɓarnata abin alherin da kishiyarta ta yi wa miji, kamar yadda ba daidai ba ne ta bi hanyoyin hana miji morar abin da kishiyarta ta yi wa mijin. 

Kamar yadda Allah (Subahanahu Wata’ala) ya yi wa Nana A’isha da Nana Hafsa matan Manzo jan kunne a lokacin da suka yi ƙoƙarin hana Manzon shan zumar da matarsa Zainab ‘yar Jahshi take ba shi idan ya shiga ɗakinta. Karanta aya ta (1 – 2) cikin Suratut Tahrimi. 

Bayan haka, wata rana A’isha (Radiyallahu Anha) ta taɓa tankwaɓe abincin da kishiyarta Ummu-Salama ta aiko wa Manzo a ranar kwanan A’isha har ta fasa akushin da abincin yake ciki. Sai Mazon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ɗauki nata lafiyayyen akushin ya ba wa Ummu-Salama a madadin nata da aka fasa mata. (Imamu Nasa’i ya ruwaito shi). 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceHadisai Uku Akan Haramcin Goyon Bayan Azzaluman Shugabanni
Labarin na GabaHaramun Ne Aibata Halittarkishiya Ko Cin Mutuncin Ta Ko Gulmar Ta Ko Kuma Yi Da Ita Ko Kuwa Isgili Da Ita