A lokuta da dama zamantakewar aure takan zama batada tasiri ga ma’aurata saboda wahalhalun yau da gobe da dawainiyar Yara takan sa a manta da soyayya.
Idan kun taba samun kanku a irin wannan yanayi ko Kuma Kuna son qarawa zamantakewar ku armashi zaku iya bin hanyoyi Kamar da dama. Wajen inganta aurenku da Kuma qara yadda da juna ta hanyoyi Kamar
haka:
1.Fita shakatawa
Kuna iya fita misali gurin cin abinci ko wani guri Mai kyakkyawan yanayi, zaki iya fada masa cewa yau ranarku ce ki biyu ba’a bukatar kowwa har yaranku ma zaifi kyau ace kin badasu ajiya inda za’a kula dasu.
Domin karanta bayani akan Pelvic Inflammatory Disease (PID) Danna nan
2.Canza yanayin Shiga
Yana da kyau ace dukkan ma’aurata su dinga bawa abokan zamansu damar ganin irin kwalliyar da Suka iya ko tanan ne zaku gane me kukafi sha’awa a tsakanin Kuna.
3.Canza yanayin kwanciya
Yana da kyau ace ma’aurata suna sabunta gurin kwanciyarsu da wani Abu na kyale-kyale.Sannan Kuma ita kanta salon kwanciyar aure Yana da tasiri sosai,ya kamata ace kullum ana samun sabon salo domin qarawa abun armashi.
Domin karanta bayani akan Zubar Jinin Haila Sosai Fiye Da Ƙima wato “Rushing” [Heavy Bleeding] Danna nan