Alamomin Shigar So 3

0
34

SO wata jijiya ce ko halitta ce wacce Allah (Subhanahu wata’ala) yake halitta a cikin zukatan mutane. Saboda haka, akwai abubuwa guda huɗu wanda kowane mutum yana yin su daga cikin su akwai; soyayya da ƙiyayya, sannan kuma, SO shi ne sinadarin da ke sanyaya zuciya kamar yadda firji ke sanyaya ruwa zuwa sanyi ko ƙanƙara.

SO tsuntsu ne wanda yake kai kawo a tsakanin zukatan mutane mabambanta. So dausayin farin ciki ne mai haddasa ƙaruwar farin ciki mara misaltuwa ga masoya. SO ne fitillar da ke haskaka zuciyar wanda suka faɗa cikin kogin soyayya.

SO ne tekun da ke gudana a tsakanin zukata mabambanta. SO shi ne asalin jigon rayuwa, sannan kuma shi ne abin da ke sarrafa ragamar dokin rayuwa bisa hanya managarciya. SO wata bishiya ce wacce take tsirowa a cikin zukatan masoya.

SO shi ne sinadarin sadaukantakar zuciya wanda yake antaya zuciya zuwa cikin kogin madarar tantagaryar ƙauna. SO shi ne maganin da yake iya warkar da mutum daga cutar soyayya matuƙar an dace da abin da ake ƙauna. SO wata guguwa ce wacce take ɗaukan masoyi ko masoyiya zuwa tafkin annurin zinaren hadarin soyayya.

Idan guguwar SO ta ɗauki mutum sukan iya makancewa akan abin da suke SO, sannan kuma mutum ba zai iya samun nutsuwa ba har sai ya samu abin da yake so a cikin zuciyar sa ko kuma Allah (Subhanahu wata’ala) ya cire masa daga cikin zuciyar sa, haka kuma ba za mu iya cewa SO makaho ba ne kai tsaye, saboda akwai waɗansu alamomi guda goma wanda So yake bi ta cikinsu kafin mutum ya kamu da son wani abu.

Saboda haka waɗannan su ne matakai na farko, wanda SO yake iya kewayawa ta cikin su, kafin ya samu gurbi ko gwadaben zama a cikin zuciyar mutum. Bugu da ƙari kuma, soyayya ba ta tsufa, a kowa ne lokaci mutum yana jin zaƙin abin da yake so idan ya tuna da shi, amma kuma ƙauna ta fi so a cikin zukatan masoya, saboda ƙauna ba ta guduwa.

Haka kuma a soyayya ba a yaudara, ƙarya, ƙeta, mugunta, sa ido, hassada, jita-jita, ƙila wa ƙala, cin amana, mummunan zato, ha’inci, sannan kuma ta hanyar soyayya ce kaɗai ake iya samun farin ciki, nishaɗi, annushuwa, wasa da dariya, zolaya mai kyau, samun kulawa, lafiya, idan an dace da abin da ake SO da kuma jin daɗin rayuwa.

Kazalika kuma akwai waɗansu abubuwa waɗanda suke kawo dalilin soyayya, su ne kamar haka; Ilimi, basira, haƙuri, gaskiya, dukiya, kunya, hankali, nutsuwa, jarumta, yarinta, fara’a, murmushi, addini, dangantaka, amana da dai sauran su.

Domin karanta alamomin shigar so na ɗaya danna nan

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceAlamomin Shigar So 2
Labarin na GabaAbubuwan Da Ya Kamata A Lura Da Su Kafin A Ɗora Mace Akan Magungunan Tazarar Haihuwa