Yadda Ake Gyara soyayya

0
5527
Ana gyara soyayya ne ta fahimtar ma’anar so, zuciya ,Alamomin soyayya, rabe-raben soyayya da dai Sauransu . 
Da farko yadda ake gyara soyayya yana da mahimmanci akoye shi sannan mu fahimci So ko kauna shine yarda da amincewar zuciya game da wani mutum ko wani abu.
A gyaran soyayya sai mun fahimci matsayin zuciya. Zuciya itace inda so ko kauna ke zaune. Zuciya kuwa Babu wani daya ke da iko da ita Sai Allah (SWT) da ya halicceta. Allah Shi Ya ke Kimsa so acikin zukata. Awajen gyara soyayya sai mutum yai shirin  shiga kogin da ba’a fitowa. Soyayya wani kogine Wanda duk ya fada cikinsa, sai yai ninkaya ya kasa fita.
Son da zukata guda biyu kewa junansu shi ake Kira soyayya. Ta kan zama soyayya mai karfi ko mai rauni.
Mai son ya koyi yadda ake gyara soyayya sai ya Koyi Ingantacciyar soyayya. Saboda Ingantacciyar soyayya ko kauna ta na dawwama a zukata ne har abada.
Tabbas So ya farantawa mutane dayawa. Kuma So ya wahalar da mutane da yawa. Babu Wanda ya kubuta daga tasirinsa. Kun ga kenan tilas mu duba yadda za mu yi gyara a soyayya.
A Dan takaice kafin mu je hanyoyin da za’a gyara soyayya. Yakamata  mu yi nazari a abinda ke Kawo matsalolin da mu ke samu a Soyayya ko ince kauna.
Kauna ta gaskiya ba ta karewa, sai dai takan iya sanyi saboda nisa, rashin samun Kulawa, kiyayya daga daya bangaren ko rabuwa.
Inkuwa Ka ji ance maka ta kare to dama sha’awace. Ko kwadayin samun dukiya, mulki da dai Sauransu.
Shi So ya na da wahala Ka iya cire shi in har ya shige Ka. Masoya na hakika sun yi bayani su na iya hakura da abubuwa dayawa a rayuwa amma banda son Masoyansu.
yadda ake gyaran soyayya
HANYOYIN DA ZA’A GYARA SOYAYYA SU NE :
1-  Soyayya ta zama angina ta akan  gaskiya. Ka da a shigo da yaudara. Misali mace ta dinga Karin gashi, kirji, ko canja launin fatar jiki.  Namiji ma ya kiyaye aron Riga, mota, Ko kudi.
2- Soyayya ta zama mafi tsarki. Wadda Babu taba jikin juna, zantukan batsa, Balle sabon Allah.
3- Soyayya ta zama ana bayyana ta. Bayyanawa Masoyi/Masoyiya irin son da ake ji. Cikin kalmomin girmamawa da kauna.
4- Soyayya ta zama ana yawan tuntubar juna. Damuwa da halin wanda ake so ya ke ciki.
5-Soyayya ta zama ana amfani da hanyoyin zamani na waya da yanar gizo. Aikawa Masoyi/Masoyiya Sakonnin hotunan furanni, zuciya da kalmomin soyayya. Bidiyo wakokin soyayya don  gyara soyayya.
6- Soyayya ta zama ana karbar gyara. Kuma ana afuwa ga wanda ake so. Banda mita da riko.

7- Soyayya ta zama ana kokarin farantawa da kyautatawa. Tare da bada Kyauta . Kyautar katinan soyayya, turare, agogo, zobe, da dai Sauransu.

8- Soyayya ta  zama akwai kunya. Ita kunya ado ce a soyayya , alkhairi ce, ta na gyara soyayya.
9- Soyayya ta zama ana Koyi da Annabi (S.A.W) . Muna da kyawawan misalai dayawa daga gidan Annabi (SAW)  da iyalansa.
10- Soyayya ta zama ana neman iliminta ( karatu) . Tare da karance-karance labaran Masoya.

 

A takaice bibiyar  wadannan hanyoyin zai Kawo mana gyara acikin Soyayya. Duba da muhimmancin soyayya a cikin rayuwarmu.
 A soyayya ba talaka, ba shugaba, ba mai kudi. Za Ka samu mafi yawan hazukan mutane sun so wata Mace a rayuwarsu. Wasu Malamai, Shugabanni, Sarakuna da dai Sauransu. Saboda muhimmancinta ya zama tilas mu San hanyoyin yadda za mu Yi gyara a soyayya.
Domin masu aure kuma zasu iya dannan wannan koren rubutun nan domin karanta yadda ake tafiyar soyayya.

BAR AMSA

Please enter your comment!
Please enter your name here